page 9&10

125 11 0
                                    

•••••••••••••••••••••••••••
             💐💐
                🐚
        🐚🐚🐚🐚
  🐚🐚 ༼۝༽🐚🐚
    💐༼۝༽༼۝༽💐
   *YAN' SARAUTA*
       💐 *9&10*💐
   🐚🐚🐚🐚🐚🐚
          🐚🐚🐚
               🐚
             💐💐
      ••••••••••••••••••••
*_BROUGHT TO YOU BY DANCING FINGER TEAM TOGETHER WITH GO 4 THE BEST TEAMS✍️✍️_*

*CLEVERS WRITERS ASSOCIATION*

*🙋_NA HAJJARA MAMI NATTYGIRL_💃*

*Wattpad@ HAJARAMAMI20*


Kallanta jabir yayi ke sai kuma ya jijjaga Kai me ya kawo ku Nan sannan maye hadin ku da tsohunnan,.
   Kallan shi Tai ba mu San komai game dashi ba Kuma wucewa muka zo Yi,.
Wacece ke? Khalil dake gefe ya tambaya hafsa Ta bude Baki zarai magana ya ce ba dake nake ba da itta nake, murmushi Tai sunana kausar sannan nice shugabar wancan gun coffee and tea shop din, baice kala ba ya juyar da Kai kawai,.
  Wani Dan box a hannun jabir ya nuna wa kausar din kin San maye wannan? Kallan box din kausar din Tai sai kuma ta dauke Kai ni ban sanshi ba baku sanshi ba to a gun tsohun yake Kuma abune da ya shafi masarauta, tabe Baki tai batace komai ba.
   Khalil dake gefe ya kare Mata kallo ya kalli jabir zo mu tafi kawai ya fada tare da yin gaba shima ya bi bayan shi suka fice,.
  Da sauri safiyanu ya karaso ranki ya Dade Ina fatan ba wata matsala ba abun da ya same ki? Eh ba komai ta fada tana murmushi, ranki ya Dade kizo ki tafi akwai wata hanya boyayya kibi tanan ki wuce Saboda Kar ki hadu da su yarima Khalil a hanya, kallan hafsa din ta Yi ok na gode sosai sai na dawo haka tabi ta wannan hanyar itta da safiyanu suka wuce,.
   Suna fitowa jabir ya kalli khalil din Yaya Ina tunanin akwai abun da yasa aka kashe shi Kuma wannan box din a akanshi yai ta cewa kaje maybe anji labarin za ka je shi yasa aka zo a aka kashe shi, ajiyar zuciya ya sauke ba komai Allah yayi zai mutu kasa amai sutura sannan ka sa amun bincike akan wannan matar,.
Murmushi jabir yayi nifa tun a lokacin Naga ka kura Mata Ido ka kasa dauke kanka naga baka damu da Mata ba kodai na samu sister in law ne, ko kala baice Mai ba ya wuce ya rabu dashi hakan yasa shima yabi bayan shi sukai gaba,.
Madam ne da bayi biyo a bayan ta ta daga murna ranki ya Dade ki fito kowa Yana jiranki a dinning area Amma Baki fito ba, Jin shiru yasa zata shiga sajida ta tare hanya kallan ta Tai taiwa alaman bayin bayanta order suka rike sajida ta bude kofan sayyada ta tare kofan,.
  Kausar dake zaune Tai magana bana Jin Dadi saboda haka bazan samu zuwa ba zaku iya tafiya, shikenan ranki ya Dade ki huta lafiya ta fada tare da ficewa,.
Da sauri sajida ta karasa ranki ya Dade yaushe kika dawo Ina Nan dai bakin kofa Banga shigowan ki ba, eh ta baya na shigo Ina fatan ba wata matsala? Bbu ta fada tana murmushi,.
  Washe gari
Ta Gama shirya tasa komai, madam dake bakin kofa Tai gyaran murya,.
Ranki ya y dade akwai taro a Babban hall da kakar su ta hada shine aka ce har da ke ga sunayen wadanda zasu je in fatan Zaki gani shikenan Zan tafi ta fda tare da mikawa sajida list din ta fice,.
   Kallan list din kausar Tai har da yarima Khalil da Jabir Ibrahim ne ban gani ba hmmm Ina tunanin anyi hakan ne Dan a hada mu da shi shiyasa Amma in ba haka ba maye sai an gayyace ni, kallan safiyanu Tai kaga wannan list din wa dawa ka sani? Ya fada Mata Wanda ya sani.
Shikenan zamu iya tafiya ta fada Tare da yin gaba suka bi bayanta,.
   Tun shigan su hango ni da wata na tafiya Yana Mata magana.
  Waike adabiyyah maye haka Ina Miki magana kina ji Dan kin samu Ina Miki magana wannan ai rashin mutunci ne, kallan shi Tai toh nace bana sanka ana so Dole ne aa kaga Mubarak ka fita harka ta, riko hannun ta yayi da karfi bana San iskanci Mubarak eh kowama ya gani Amma Ni bazan kula ka ba ka barni ganin ya ki sakinta yasa ta Galla Mai cizo Tai gun su kausar da zuwan su kenan ta buya a bayanta,.
  Kallan shi kausar Tai bayin masarautar su sanar Mata Dan uwan yarima Ibrahim ne, kallan Mubarak Tai sarauniya kausar kenan waddda yarima Khalil zai aura,.
   Ban tambaye ki ba kallan kausar din yayi ai naji labarin ki kece wadda saboda mununki yarima Khalil yaki kula ki ko? Dama wa zai auri mummuna Ni ko Mata sun kare ai ba abun da Zan Yi da irin ki Kuma yanzu Zan nunawa kowa mununki, Yana kaiwa Nan ya Mika hannun akan zai cire mask din ta kauce kallan shi tai ai na dauka iya yarima Khalil ne yake da matsala Ashe akwai wanda ya fishi har ha zarce Dan Kai saidai a hada ka da kare sosai ranshi ha baci yayi kanta zai dauketa da Mari ta rike hannun taja hakan yasa ya fadi a kasa,.
   Dariya adabiyyah Tai hakan shi ya dace da Kai ai, yarima Khalil dake tsaye a baya ya Karaso dai dai lokacin kausar ta juya mask din ta kusa cirewa Tai saurin riketa sajida ta sake daure Mata ta baya, kallan ta yayi yaso mask din ta cire Amma Allah baiba,.
   Kallan Mubarak yayi me kace dazun kin kina ya fara bance komai ba, sosai Dan jabir ya baci ya dauke shi da Mari saboda Abun da yaiwa adabiyyah, kallan Khalil jabir yayi cewa nayi bazan taba Santa ba tunda kaima baka santa, matse Mai hannu jabir yayi hakan yasa ya Kara yin magana bazan sota ba Koda kaima ka sato, sake shi jabir yayi hakan yasa ya mike ya fice,.
  Kallan Khalil din kausar Tai shima ya dago suka hada Ido hakan yasa ya dauke nashi idon,.
   Kaima zaka je kenan nasan badan kowa zaka ba sai Danni ko har ka fara fadawa tarko, juyar da Kai yayi zaiyi magana kakar tasu ta karaso hakan yasa suka zube suna kwasar gaisuwa,.
   Ku mike ta fada da murmushi,kallan kausar Tai Ina ta ji labarin ki ana wai mummuna sai Ni kuma Naga Banga hakan ba ni banma taba ganin Mai kyau irin ki ba, dariya kausar Tai na gode yabawa ranki ya dade, murmushi ittama Tai to tunda kowa yazo kuzo sai mu karasa, Khalil ne ya karba ranki ya Dade bazan samu zuwa saboda akwai inda zani shi yasa, jijja Kai tayi ai shikenan tunda ba zaka samu zuwa ba ba sai jabir ya wakilce ka ba, kaiiii jabir ya fada Yana Dan hade Rai, godiya Khalil din yayi ya tafi yabar jabir din,.
   Babban gune an hada komai su lemo, su coffee su tea,.
   Kallan kausar kakar su tayi ya kike ji da zaman bangaren ki Ina fatan ba matsala? Murmushi Tai ba matsala komai ya tafiya dai dai saidai Kuma ..... Tun kafin ta karasa Grandma din tasu ta karba saidai me?
   Matsalan bayi ne indai suna Baki matsala matsala yanzu sai in canza Miki su, aa ba su bane kawai dai in Ina San fita nake samun matsala, akwai Wanda yake hanaki fita kenan? Aa ba wannann ba duk inda zani ne sai bayi suce sai sun bini, dariya Tai ai suna taare miki lafiyar kine shi yasa, murmushi Tai tunda zanzo ai yayana ya hado Ni da wani shi yasa sai baya Jin Dadi yake ganin kamar Bai iya ba shi yasa suke Mai haka shi yasa nace zanyi magana, eh gaskiya shikenan zanyi magana sai a barki kina futa da wancan din, nagode ta fada Tana murmushi.
  Kallan jabir grandma tayi Kai Jabir kawai kaci abincinka shikenan ko bama ka damu da itta kausar dinba, turo Baki yayi Kai grandma naga Ni ba Khalil bane?,

*Dedicated to you mariya abdulrazak together with Maryam dahiru*

By hajjara Mami Natty girl

YAN SARAUTAWhere stories live. Discover now