p 24&25

99 8 0
                                    

[8/31, 8:49 PM] Hajara Mami: •••••••••••••••••••••••••••
             💐💐
                🐚
        🐚🐚🐚🐚
  🐚🐚 ༼۝༽🐚🐚
    💐༼۝༽༼۝༽💐
   *YAN' SARAUTA*
         💐 *24*💐
   🐚🐚🐚🐚🐚🐚
          🐚🐚🐚
               🐚
             💐💐
      ••••••••••••••••••••
*_BROUGHT TO YOU BY DANCING FINGER TEAM TOGETHER WITH GO 4 THE BEST TEAMS✍️✍️_*

*CLEVERS WRITERS ASSOCIATION*

*🙋_NA HAJJARA MAMI NATTYGIRL_💃*

*Wattpad@ HAJARAMAMI20*



Tafiya suke jefi jefi suna Hira kamar Dama sun Saba sosai kasan na aika inda ka kaini Amma baka nan ko ba anan kake da Zama ba? Eh gaskiya ban fiya Zama a anan ba karki damu Ni da kaina zanzo inda kika din, shikenan ta fada gaurd nashi yace ranka ya Dade munzo, yauwa ya fada tare da bude kofan itta ta bude ta fice, hafsa dake waje Tai saurin karasawa yau sannunki da dawowa ta fada ta murmushi a face nata, kallan hafsa Tai sannan ta kalli usma wanna hafsa kenan tare Muke aiki da itta anan, sannu ya fada da murmushi yauwa sannu tunda kazo kazo ciki ko ruwa ne kasha, aa no no ba komai Ina sauri ai Zan dawo wataran yanzu akwai Abun da zanyi kallan kausar yayi to sai anjima yauwa San anjima nagode tana kallo ya tafi.
   Ina ta jiran dawowar ki muje ciki Tam ta fada suka shige ciki, da sauri safiyanu ya karasa gun KAUSAR sannu da dawowa tun dazun nake jiran zuwanki, Ina San in San plan din da kike shirya wa, murmushi tai kan shirya Mana mutane zamuje kawo village Dan nasan ba Wanda zai tsaya Bata lokaci yanzu Nima ba in shirya shikenan ya fada tare da ficewa,.

   **************
Dan jeji ne gun faskare matashin yake hankali kwanta tun daga nesa ya hango mtane da yawa fuska a rufe, su Mubarak ne Yar da gatarin yayi zai gudu suka zagayeshi, kallan shi Mubarak yayi me kake anan Kai kadai kana yaron wajiri daya mutu? Wai me kuke nema a guna nane kuke San takura mun? You don't worry ba Abun da Muke nema nasan tunda ka dawo Nan kana boye abune Amma karka damu ba sai kana da Rai zaka boye wani abun ba kallan gaurd ku kashe mun shi, ai kuwa sukai kanshi ya fara guduwa Dan kwatar kanshi, zuwan Khalil kenan Mubarak ya hango shi ai kowa yayi Kan matashin ba tsammani yaga Khalil a tsakiya tare da hankadashi gefe tuni fada ya kaure tsakanin su su suna San kashe matashin inda mutanen khalil kesan shi da Rai, ganin fada ya kaure yasa matashin Samu ya gudu ya fita daga gidan yayi dagin gun zuwan su kausar kenan Suma face nasu a rufe tana ganin ya fito ta bishi a baya da gudu, safiyanu shima yabi bayan ta, faduwar da matashin yayi yasa ta cin masa, a kanshi ta tsaya da wuka a hannun ta irin sword dinnan, Mikewa yayi Dan Allah Kar ka kasheni, shi ya dauka na mijine Dan shigar da tayi kenan, Nima ai basan kashe ka nake Yi ba kawai tambaya Zan maka da ka ban amsa shikenan,maye kake San sani? Zuwan Khalil kenan ya buya a bayan wani dutse Yana karawa kausar din kallo, voice din kamar yasan Mai shi.
   Tamabayar ka zanyi kaban amsah akan littafi masarautar Nan, Ni ban San komai a akai ba ya fda Yana kallan ta ok ai baka da amfani a guna kawai gara in kashe ka ta fda tare da yin gaba da wukar alaman caka Mai zatai, aa tsaya Zan fada,ok Ina ji, littafin Yana bangaren wajiri na duka Wanda da Nan ne ainihin fadar masarautar Amma daga baya aka canza koshi wajirin baisan da anan yake ba anan ta tunanin Yana secret part na masarautar Amma anan ainihi yake sannan Yana da code na Shiga gun, sai Kuma yayi shiru Ina ji code din *masarauta uku* shine code din Abun da na sani kenan, zatai magana taji an rike kafadar ta daga baya hakan yasa ta juya zata bar gun yasa Mata wukan shi dake hannun shi a wuya inda ya rike wannan matashin ba damar kwacewa, waye Kai khalil ya tambaya Yana kallan bayan kausar Wanda taki jiyowa, koma waye ya juyo ya fada Yana kallanta gabanshi na faduwa ba tsammani sai kawai harbi suka ji anayi irin na arrow dinnan Wanda har ya Sami matashin ya fadi agun mace, Kuma arrow wani ya Sami khalil a hannun, suna cikin haka mutanen kausar din Suka karaso hakan yasa wadancan guduwa, khalil da arrow ya samu ya fara ganin dishi dishi, Zama yayi a jikin dutse, hannun nashi kausar ta duba taga an same shi da arrow Kuma da gani Poison ne a jiki,lokacin ya riga ya fta hayyacinshi baya ganin ma waye da bakin ta tasa tana zuke poison din tana zubar wa har ta Gama, safiyanu ya karaso ya makata mu tafi,kallan Khalil Tai Wanda ya Suma ka taimaken sau daya Nima yau na taimake ka ,mikewa Tai suka tafi suna tafiya mutanen khalil na zuwa wannan kenan,.

YAN SARAUTAWhere stories live. Discover now