MAMAYA page 5

1.2K 70 1
                                    

*👺🤡MAMAYA👺🤡*

*NA*

*HAUWAU SALISU*

*MAGA_TAKARDAN KAINUWA CE ✍🏻*


*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

07081095452

My Gmail👉🏻
*Hauwausalisu407@gmail.com*

My Facebook 👉🏻
*Hauwa'u Salisu*

My Wattpad 👉🏻 *Hauwausalisu*
https://my.w.tt/P1yNEVRFl3


*Ina matukar godiya gareku masoyan Haupha 🥰🥰👉🏻❤*

*Shafi na Biyar*

Mal. Aminu ya kafe ta da idanuwan sa da ba alamar sauƙi cikinsu ko rangwame.

Addu'ar neman tsari kawai ta ke a zuciyarta.

Ya jima tsaye kafin ya shigo cikin ajin ,kai tsaye inda ta ke ya nufa numfashinta taji zai dauƙe dan haka ta zabura ta bangaje shi ta ruga da gudu tabar ajin .

Ga dai dariyar yanda ta bangaje shi ya faɗi ƙasa ƴan ajin nason yi amma gudun hukuncin mal Aminu ya hana kowa motsin kirki a gunda ya ke.

Gudu ta ke na gaske bata damu da yadda mutane keta bin ta da kallo ba har ta shigo layin su .

Ji tayi kawai taci karo da wani abu wanda yasa numfashin ta ɗaukewa.

Cike da tashin hankali Nasir ya sauko daga kan machine ɗinsa ya nufi inda Bilkisu ke kwance shame_shame ƙasa.
Mutane nan da nan suka kawo ɗauki dan wasu kan idanunsu lamarin ya faru.

Ba sosai taji rauni ba amma ta suma , abin da ya tada hankalin Nasir kenan duk ya ruɗe.

Mal. Ahmad da fitowarsa daga gida kenan zai koma kasuwa taci karo da   al'amarin .
Bakaramin tashin  hankali ya samu kanshi ba ciki , sai dai ya tabbatar ma da Nasir ɗin ya tabi ba komi Allah ya kiyaye gaba .

Shi kuma Nasir sai ya samu kanshi da kasa tafiya balle ya aminta da maganar mal. Ahmad ɗin duk da yanzu ya fahimci shine mahaifin yarinyar da tsautsai yasa ya banke .

Sai da mutane suka saka baki sannan mal. Ahmad ya amince suka dauki Bilkisu zuwa asibiti dan duba lafiyar ta sosai .

Inna tun da wancan lamari ya faru sai ya zama ta sake ɗauko wata sabuwar tsana da tsangwama ta ɗora akan Bilkisu ,kwata kwata bata barin ta ganta cikin natsuwa komi tayi sai ta gwasaleta ,hakan yasa Bilkisun a sabuwar damuwa ainun.

Ko ina an duba bata samu wani rauni ba wanda zai tada hankali illah kujewa da ta samu wasu wuraren ,hakan yasa aka bata magunguna kawai.

Tun da yake bai taɓa ganin yarinya natsatstsa kamar wannan ba , yana rayuwa cikin bariki amma bai taba ganin yarinyar da natsuwarta ta shahara ba kamar wannan yarinya da ya banke da machine ɗinsa .

Kallonta kawai yake yanda duk tabi ta birkice dan ganinsa tare dasu .

Gata ga alama jarumace dan ya ga ko gezau fuskarta batai ba da ana wanke ma ta raunuka da magani.

Sai Babanta daketa jera mata sannu wani kan wani , ita kam ba ta ko son ɗago fuskarta ma .

Bayan an gama komi ya sake biyo su dan ganin gidansu ,wanda ya karanci fuskar mutunniyar tasa sam bata so hakanba .

MAMAYAWhere stories live. Discover now