MAYAYA page 16

900 64 8
                                    

*👺🤡MAMAYA👺🤡*

*NA*

*HAUWAU SALISU*

*MAGA_TAKARDAN KAINUWA CE ✍🏻*


*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

07081095452

My Gmail👉🏻
*Hauwausalisu407@gmail.com*

My Facebook 👉🏻
*Hauwa'u Salisu*

My Wattpad 👉🏻 *Hauwausalisu*
https://my.w.tt/P1yNEVRFl3

*BARKA DA SALLAH MASOYAN HAUPHA* .🤝🏻🤝🏻🤝🏻

_Ina fatan fatan munyi sallah lafiya cike da farin ciki da walwala duk da cewar wannan shekarar munga rayuwa kala daban-daban to muna fatan Allah yasa ibadinmu sun karɓu, muna daga cikin waɗanda aka gafarta ma zunubbanmu baki ɗaya. Ameen_ 🤲🏻🤲🏻

Page 16

Bin bayanta yake cike da fargaba mai cunkushe da tsoro, ita kuma ko waigowa bayanta bata yi kawai tafiya ta ke cikin sassarfa ta ban mamaki wanda hakan yasa dole Malam Aminu fara haɗawa da sauri-sauri gudu-gudu dan ya cin mata amma ina sai ƙara sauri ta ke harta shiga cikin wani kwangon gida wanda ga alama an gamashi amma ba'a tare cikinsa ba tunda ko fenti ba'ai masa ba. Kai tsaye cikin gidan ta nufa shima ya mara mata baya cikin sauri, yana shiga yaga kofa ta samu da kanta ta rufe gidan kai tsaye nan ta ke wani uban duhu ya mamaye gidan baki ɗaya tamkar wata yayi nisa, hankalinsa yayi mugun tashi domin ko tafin hannunsa bai iya gani tsabar duhun cikin gidan. Yana nan tsaye inda yake ya ji wata uwar ƙara mai amsa kuwwa wadda ko shakka bai yi muryar Bilkisu ce sak, jiyayi ana juyashi da tsiya har aka waiga da shi hakan yasa ya hango Bilkisu tsaye ta sauya kaya zuwa wata zumbuleliyar riga ja da fari sai wani jan ƙyalle akanta da hannayenta, gashin kanta yayi cirko-cirko bisa shi akwai wata buta sai zubo da wani jini ta ke yana zuba cikin wata ƙaramar ƙwarya da ke hannun Bilkisun, ita kuma sai wasu surutai ta ke yi wanda ba wanda ya isa ya gane abin da ya ke ambata kai tsaye inba shima yana irin abin da ta ke aikatawa ba. Tamkar numfashinsa zai ɗauke haka ya dinga faman fizgoshi da tsiya amma ina numfashin ya ƙi fitowa dole ya sulale a gun yana dafe da zuciyarsa. Cikin wata baƙar fusata ta wullar da tukunyar jinin ya watse har kan fuskar Malam Aminu, cikin halin fusatar ta janyo wani abu da ke dunƙule cikin ƙyallen da ya gani gunta yana jini ta fito waje da shi, "Ya salam" ita ce kalmar da Malam Aminu kawai ya iya faɗa kenan ganin kan mutum a hannun Bilkisun tana kallon sa ta bushe da dariya mai ban tsoro matuƙa kafin ta sanya bakinta kai tsaye ta fara gwagwiyar kan tana fisgar naman tana ci kamar ta samu naman shanu soyayye, tana cikin ci ta fizgo idon ta wullo sai gashi bisa Malam Aminu, ai kuwa ya fasa uban ihu yana ba da haƙuri abin da yasa Bilkisu daina cin kan ta nufosa bakinta dagaje- dagaje da jini rigarta sharkab da jini ba kyan gani ko kaɗan " Dan ALLAH Bilkisu kiyi haƙuri wallahi ban san cewa ke matsafiya bace da ban biyo ki ba, na ɗauka ke din mayya ce kawai wadda karfinta bai kai haka ba. Wata mahaukaciyar dariya tayi data kashe masa dodon kunne na daƙiƙa guda, tasa hannu ta janyo shi yana ihu yana wulle-wulle amma ina sai da ta kaisa gab da bakinta san nan ta haɗe rai tamkar zata mutu tsabar baƙin rai har wani huci ke fitowa daga jikin kumatunta mai zafi idan ya ɗiga a jikinsa tamkar wuta yake jinsa, kallon sa tayi cike da mugunta tace "Na jima ina neman ran da zan kamaka amma sam kaƙi ban damar yau dai ga damar ta samu dan haka ba wanda zai hanani shanye jikinka na cinye namanka tas" Tsabar galabaitar da yayi ko ido ya kasa ɗagawa ya kalleta domin zuwa lokacin hucin duk ya gama ƙone masa jiki, can ƙasan zuciyarsa yaji ya fara karanto addu'ar neman tsari daga dukkan abin halitta, hakan yasa nan ta ke Bilkisu tayi wulli da shi gefe tana birgima ƙasa tamkar jikinta na ƙonewa, bai ankara ba ya gansa kwance kofar gidansu a mawuyacin hali.

*****

"Huraira yanzu dan Allah ke ba zaki girma ba? Kullum sai kinyi abin da zance Allah wa dai gareki dai ? Huraira da ke zaune cikin kayan Fulani ta caba fuska da kwalli sai wani hayaƙi ta ke tana surutai masu kama da fara koyon maganar yara ko kallon inda Malam Ahmad ɗin yake ba taiba, sai da ta kammala abinta san nan ta kalli Malam Ahmad ɗin fuska turɓune tace "Kasan Allah Malam na gama zama Aljanu na wasarere dani a gidan nan, tunda na kula kai ko a jikinka da ya ke ba kai suke wahal waba, ba kai suke mari ba, ba kai suke sakawa rawar indiyawa ba shine zaka ce kar na nemi maganin ƴan banza? To saurareni kaji da kyau wallahi dai-dai nake da kai kan lamarin nan. Abin ya ba shi tsoro ainun tabbas sai ya miƙe tsaye kan lamarin Huraira idan ba haka ba jahilcinta yawa zai ƙara har yasa shima ya samu zunubi mai girma.
Duk abin da ake Bilkisu na hange banda kuka babu abin da ta ke yi lamarin Inna ya ta'azzara shirka fa kenan ta fara aikatawa.

Tana gama hayaƙinta ta sunkuci kayan tsibbunta ta shige ɗakinta, tana masifar ba wanda ya isa ya ƙara hanata magani a gidan nan.

Taufa su Inna an sake kama wata hanyar kuma .
Taku ce dai Haupha mai matukar ƙaunarku ba tare da wani sanadi ba illa na nuna soyayyarku gareta kai tsaye.

Taku Haupha ✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻

MAMAYANơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ