MAMAYA page 24

383 48 0
                                    

*👺🤡MAMAYA👺🤡*

*NA*

*HAUWAU SALISU*

*MAGA_TAKARDAN KAINUWA CE ✍🏻*


*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

07081095452

My Gmail👉🏻
*Hauwausalisu407@gmail.com*

My Facebook 👉🏻
*Hauwa'u Salisu(Haupha)*

My Wattpad 👉🏻 *Hauwausalisu*
https://my.w.tt/P1yNEVRFl3

Page ___24

Dajin gaba ɗaya yayi duhu baka jin motsin komi sai kukan ƙananan dabbobi irin tsuntsaye.

Zaune yake ga alama cikin ɓacin rai yake yanda hayaƙi ke fitowa ta dukkan jikinsa, idanunsa sun juye zuwa jajir ba wani ɗigon fari ko kaɗan a cikinsa, kansa yayi girma na gaske hannunsa na ɗauke da wasu kafta-kaftan ƙumbuna masu tsawo da kaifi, zuwa yanzu hawayen jini ke zubowa daga idanunsa wanda daga gani tafasasshene ke zubowa, tsabar zafinsa shi kanshi idan ya ɗiga a jikinsa sai gun nashe ya kwashe tamkar garwashi ne ya zuba a gun. Ya taƙarƙare ya buga wani uban ihu wanda yasa gaba ɗaya dajin amsa amo mai ban tsoro da firgicin gaske take sai ga duwatsu na fashewa da kansu tsabar amon muryansa daya fita har wani walƙiya ta tashi a dajin gaba ɗaya, ya fasa uban ihu ya ƙara fasawa ya miƙe tsaye rai ɓace ya fara ɗaukar alwashi cikin matuƙar ɓacin rai da neman cikar buri "NA RANTSE DA WANDA KE BUSAMUN NUMFASHI SAI NA ƊAIƊAITA RAYUWARKI NA ƊAUKI MUGUWAR FANSA GAREKI NA MAMAYE KI MAMAYA MAFI MUNI DA BAN TAKAICI BILKISU, KO DA HAKAN ZAI SA NA IDA RASA SAURAN KIMATA DA KIKA ZUBAR MUN. Ya fashe da kuka mai tsuma zuciya yana birkiɗa zuwa duk halittar da yaga dama mafi munin halitta acikin masu ban tsoro, dai-dai nan Aljana Barriratul azam ta bayyana cikin matuƙar tsoro take kallon Yah Malam wanda ya dage ban da kuka babu abin da yake yi mai cin rai, sanin muguwar zuciyarsa yasa ta kasa masa magana kawai ta koma gefe itama ta kama kukan cikin yanayin tashin hankali da fargabar abin da zai mata idan ta gaya mashi bata samu damar canza Bilkisun ba, ba ƙaramin aikinsa bane ya huce takaicinsa akanta ba, shin waima miyasata zuwa a daidai wannan lokaci da yake cikin tsananin tashin hankali da baƙar zuciya ? Ganin bai san ta zo gunba yasa taba kanta shawarar ɓacewa agun kafin ya ankara da ita ya sauke komi kanta,cike da aminta da shawararta ta yunƙura da niyyar ɓacewa agun, sai dai ji tayi tamkar an ɗaure mata dukkan wata kafa mai motsi dake cikin jikinta akai, baki ɗaya wani matsiyacin zafi ne ke ziyartar dukkan sassan jikinta, tamkar ana kwarara mata zuwan dalma haka take ji a jikinta, baki ɗaya jikinta ya kwaye ya sulɓe tamkar an tsomata a cikin soyayyen mai. Ihu take da dukkan karfinta wanda ihun shine ya ƙara tunzura hawayen Yah Malam ɗin zubowa akai-akai akan jikin nata, cikin galabaita ta fara bashi haƙuri da magiya yayi haƙuri karya nakasata, amma ko sau ɗaya bai buɗe idanunsa ba, hawayen kawai ke zubowa cikin sauri da sauri, sai da ya tabbatar da ya ƙone mata kaf ilahirin jikinta sannan ya korata zuwa aikin da yasata cikin gargaɗin idan yau bata cika masa burinsa ba na kawo masa Bilkisu dajin nan ba tabbas zai mata hukunci mai girma da tsanani.

Cikin natsuwa ya koma gidansu dan dakatar da ƙannensa da sukace zasu je dubo Bilkisun, cikin falo ya iske su suna jiran akawo masu abincin da zasu tafi dashi, cikin basarwa yake sanar masu an sallame ta har sun tafi gida, Ummansu dake zaune tace "To ai ba komi sai ka kaisu gidansu su dubota ai duk ɗaya ne. Cikin rashin jin daɗin zancen Umman yace "Su bari sai wani time naje dasu yanzu a barta ta huta. Ya wuce sashensa, yana tunanin taya zai bari suje Inna Huraira tana tashen iskancin aljanun ƙarya ? Ai bazai taɓa barinsu gane gidanba balle suje wata rana ta sai da halin ta jamasa matsala ba.

Inna Huraira kam sai ji tayi an watsa mata wani abu amma bata ga komi ba bataga kowa ba, ta wuce ta shige itama tana yamutsa fuska, kai tsaye ɗakinta ta nufa da niyyar ida aikinta  na hayaƙi, cikin sauri ta saka kayan fulanin tai kwalliyar nan ta caccaɓa fuskarta tas, ta fito tsakar gida ba kowa ta kunna wuta ta fara hayaƙin, sai dai tana farawa taji gaba ɗaya jikinta ya ɗauki wani mugun ƙaiƙayi wanda nan take ta fice hayyacinta, ta fara zabure-zabure tana soshe-soshe tamkar  sabuwar kamun hauka, duk tabi ta birgice ga kwalliyar fuskarta zuwa yanzu hawayen da take ya ida watseta ta koma wata kalai ban tsoro musamman gashinta ya ƙara bada gudunmuwar da halittarta ta koma irinta aljanun nan, komi ta samu wawura take tana kartai jikinta, amma abin ba sauƙi dan haka ta fashe da kukan gaske kamar wata ƙaramar yarinya, tana birgima ƙasa tana ihu ta bani ta lalace yau zata mutu akawo mata ɗauki.

Malam yana tare da Bilkisun yana bata haƙuri kan tai haƙuri wata rana sai labari, ta tsaida kukanta da ƙyal tace "Baba ka yafemun ka gayamin wa ce ce mahaifiyata dan Allah? Jikinsa yayi sanyi dan tabbas yasan wannan ranar na zuwa da zatai wannan tambayar. Ajiyar zuciya yayi ya dafata yace "Bilkisu Huraira itace mahaifiyarki itace ta haifeki ki cigaba da mata addu'a kan ta gyara halinta kawai, amma ki cire duk wani tunanin ba ita ta haifeki ba kinji ? Kanta ta ɗaga tana jin natsuwa a ƙasan ranta..... daidai nan suka ji kukan Innar cikin yanayin tashin hankali, dan haka suka nufo tsakar gidan, dan ganin abin da ke faruwa take wannan kukan mutuwar.

Gaba ɗaya sun aminta bori ne ta fara ya bata ruwa dan haka da sauri Malam ya sakata ɗaki ya rufe ya fita neman masu maganin Aljanu , Bilkisu sai ta zauna ƙofar ɗakin taci gaba da kukanta, hakan yaba Aljana Barriratul azam damar shigewa ɗakin kai tsaye.

To ko miye zai faru ?

Taku ce Haupha✍🏻

MAMAYAWhere stories live. Discover now