MAMAYA page 13__14

995 51 4
                                    

[06/04, 9:35 PM] Haupha: *👺🤡MAMAYA👺🤡*

*NA*

*HAUWAU SALISU*

*MAGA_TAKARDAN KAINUWA CE ✍🏻*


*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

07081095452

My Gmail👉🏻
*Hauwausalisu407@gmail.com*

My Facebook 👉🏻
*Hauwa'u Salisu*

My Wattpad 👉🏻 *Hauwausalisu*
https://my.w.tt/P1yNEVRFl3


*Shafi na Goma sha ukku*

Major Nasir na zaune yana tunanin abin da yasa Bilkisu kwana biyu bata sakewa da shi a waya sam, ya samu saƙon gajeren hutu na karshen shekara da aka saba basu, ba ƙaramar murna da ɗoki yayi ba jin wannan labari, dan yana da tabbacin zai je ya gana da masoyiyarsa abun ƙaunarsa Bilkisu, yarinyar ta gama tafiya da zuciyarsa gareta, kwata-kwata baijin zai iya rayuwa babu ita halayenta sun masa ainun bata da kwarabniya gata da natsuwa.

Cikin mintuna ya kimtsa kayansa ya ɗau hanyar Funtua.

Cikin kwana uku da zuwan yah Malam makarantar sunyi shaƙuwar ban mamaki shi da Bilkisu, abin da yaba sauran ɗaliban ajin nasu mamaki matuƙa, domin duk shigowar da zai sunanta ne farkon ambata, komi kaji yace "Bilkisu ya akai ne ? Idan karatu yake maso kuma yace Bilkisu mike baki gane ba ?

Ita kuma sai ya kasance tana matuƙar jin daɗin yanda yake nuna mata kulawa ba kamar yadda Malam Muntasir ke hantara da zaluntar ta ba, sai take ganinsa tamkar wani yayanta na gidansu da suke matuƙar shiri.

Lokuta da dama tana tunanin masoyinta abin ƙaunarta Nasir wanda sai waya kawai da suke sha duk da cewar ita bata jure sakin baki ta furta masa kalamai kamar yanda yake zayyano mata su cikin shauƙi da jin daɗi.

Inna Huraira na zaune tsakar gida tana bakace shinkafa sai rera waƙa take hankalinta kwance.

Tana cikin waƙe-waƙen nata taji kukan kaza da ƴaƴanta tsakar gidan, cike da mamaki ta ɗago kai ta kalli kazar sai taganta ita ƴaƴanta sai nufa ta suke kai tsaye suna kuka su duka.

Cike da tsiwa tace "ji shegiyar kaza ko ta gidan uban waye ta shigo mun cikin gida da tarkacen ƴaƴanta, to wallahi yau zaku ci ubanku dan ko ƙwarar shinkafa guda baku ci daga cin shinkafar nan wallahi."

Ta ci gaba da aikinta bakinta bai lafa da zagin kazar da mai kazar ba.

Tana cikin bakacen kawai tiren ya suɓule ya faɗi ƙasa, shinkafar ta watse tas a ƙasa.

Aikuwa kamar daman jira suke kazar nan ta nufo shinkafar ita da ƴaƴanta suka fara caccaka suna ci.

Ai Inna Huraira sai ta miƙe tsaye ta ɗauko dogon karanta ta dage iyakar ƙarfinta ta sauke shi akan ɗan tsako guda, ya kuwa faɗi ƙasa yana mimmiƙewa alamar mutuwa zai yi .

Caraf ba zato ba tsammani Inna Huraira taji an shaƙe mata wuya ana cewa " wallahi yau sai kin biyani yarona akan mi zaki bugar min yaro ?

Idanuwa waje Inna ke kallon kazar da ke shaƙe da wuyan rigarta, faratan kazar sun nutse a wuyanta, ji take kamar wani ƙaton namiji ne ya fidda iyakar ƙarfinsa ya shaƙeta.

MAMAYAWhere stories live. Discover now