MAMAYA page 36---37

442 58 9
                                    

*👺🤡MAMAYA👺🤡*

*NA*

*HAUWAU SALISU*

*MAGA_TAKARDAN KAINUWA CE ✍🏻*


*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

07081095452

My Gmail👉🏻
*Hauwausalisu407@gmail.com*

My Facebook 👉🏻
*Hauwa'u Salisu(Haupha)*

My Wattpad 👉🏻 *Hauwausalisu*
https://my.w.tt/P1yNEVRFl3

My You tube channel 👉🏻https://youtu.be/h6gc8ahxrmM



Page 36----37

Cikin ƙwarin gwiwa Malam Aminu ya isa gidansu Shema'u jikinsa na bashi ita ce kawai wadda zata zame masa katanga mai tsanin da zai isa ga Bilkisu harya sameta matsayin mata abar alfahari garesa. Ba da jimawa ba sai ga ta fito fuska ɗauke da mamakin jin yaro yace ta zo inji malaminsu Aminu.
Bayan sun gaisa ya fara koro mata bayanin abin da ke tafe dashi gareta . Ba ƙaramin girgiza tayi ba jin cewa son Bilkisu yake , ai ba Bilkisu ba ko ita bata sonsa balle Bilkisu da ya maida jakkar gidansu dukan safe daban na rana daban,amma sai ta basar tace "Ba komi malam amma fa Bilkisu nada wanda take so wanda kaima ka san shi, ta kauda kai kada yaga dariyar dake neman kucce mata .

Ajiyar zuciya ya saki mai ƙarfi "Ba shakka na fahimci mugun sojan nan na sonta amma kuma hakan bai sa naji ɗar akan zuciyata ba, dan haka ki taimaka ki zame mun tsani na isar da soyayya ta gareta Shema'u dan Allah."  Ajiyar zuciya ta saki itama domin so yake ya tasa cikin tashin hankali ga alama, taya zai tunkareta da maganar ta shige masa gaba kan lamarin soyayyarsa bayan Nasir yace ita ce mai kula masa da duk motsin Bilkisun to me zai faru idan ya samu labarin ita ce ta haɗa Bilkisu da wani ? Kai ba zai yiyu ba gaskiya. Batasan a fili tayi furucinba sai da Malam Aminu yace "Na ɗauka tarenku ta gaskiya da gaskiya ce ai ke da Bilkisu, domin masoyin gaskiya bai barin masoyinsa ya kai kansa ga halaka, ina nufin bai kamata ki bar ƙawarki na makauniyar soyayya ba, ki yi duba ga yanda yayi mun shegen duka harna suma saboda na ɓata masa rai kawai to baki gudun itama wata rana ta ɓata masa rai ya kwatanta mata yanda yayi mun? Kin san fa soja dukan mace su ke."
Gaba ɗaya sai ya jefata a cikin tunani domin maganarsa gaskiya ce ance sojoji dukan matansu suke, to amma ai Nasir yayi fice ko a sojojin yanda yake son Bilkisu shaida ne akan bai iya takura mata balle ya duke ta amma dai zata taya ƙawarta addu'a Allah ya bata mafi alheri a tsakaninsu, haka sukai sallama batare da ya samu amsa ko alamar ya samu karɓuwa ga Shema'un ba, sai dai duk da hakan bai ji alamar karaya daga zuciyarsa ba kan lamarin soyayyarsa da Bilkisun ba.
Haka ya koma gida yana tunanin sabuwar mafitar da zai samu cikin sauƙi ya bita ya samu soyayyar Bilkisu.

Dajine wanda babu alamar akwai mutum a cikinsa, baki ɗaya wasu manyan bishiyoyi ne gajeru masu duhuwar gaske a cikinsa, ko tsuntsu guda baka ganin gilmawarsa balle kukansa, yawan bishiyoyin tare da girman ganyayensu yasa duhu samun matsugunni a cikin dajin, akwai wata gabjejiyar bishiya guda ɗaya wadda duk tafi girma da cunkushewa a cikin bishiyoyin dajin, jikinta akwai zanen ƙahunna da zanen tukunya anyi mata ado da wasu ƙyallaye koraye da jajaye, wata ƙaramar tukunya a je dai-dai bakin wawakeken kogon dake jikin bishiyar .

Dajin baki ɗaya tsit yake baka jin motsin komi baka ganin kowa tamkar tsohuwar sahara.

Wannan shine dajin Sarkin baƙaƙen Aljanu masu taƙama da karfin tsafi da sihiri,mahaifi ga Aljana Raƙiyyatul Zayyanul murrash bin zainul,wadda ke matuƙar ƙaunar Nasir. Cikin wani mawuyacin ta bayyana dajin daidai bakin bishiyar nan jikinta sai zubar jini  yake tana nishi sama-sama tamkar ruhinta zai bar gangar jikinsa. Wata uwar tsawa da walƙiya ta bayyana mai tartsatsin jar wuta, wasu guntayen tsoffi suka fito daga cikin kogon suka ɗauke ta suka koma inda suka fito.

Yana zaune gaban kayan surkullensa idanuwansa sunyi jajir fuskarsa babu alamar rangwame ko sassauci ya dage iya karfinsa ya fasa uban ihu wanda yasa baki ɗaya ɗakin ya fara girgiza abubuwa na tarwatsa ko ina yana amsa kuwwar ihunsa. Cike da alwashi ya fara magana "Na rantse da abin bauta sai na  ruguza Masarautar sakin fararen Aljanu sai na gwada masa karfi da irin karfin tasirin tsafina, ko shakka babu tunda ya taɓa gudan jinina sai na kassara rayuwarsa tare da sauran mabiya bayansa." Cikin fusata ya ɗora hannunsa akan Rakiyyatul zayyanul murrash bin zainul, nan take raunikan jikinta suka ɓace tayi zumbur ta miƙe tsaye ta juya baya ta fara magana cikin zallar ɓacin rai da fusata mai cike da niyyar ɗaukar fansa. "Ya kai Abbana ka sani daga yau na zubar da duk wani bore da nayi maka a baya na daina bijirewa dukkan umarninka amma fa bisa sharaɗin zaka ba Nasir kariya tare da ahalinsa kamar yadda na kasance ina basa, a cikin binciken da nayi na gano Sarkin fararen Aljanu Abduljalal bin Uwais (Yah Malam) na bibiyar rayuwar Nasir da wata yarinya da Nasir ke son aura,han haka inasan ka basu kariya ni kuma ka ƙara mun ƙarfi wanda zan tari Abduljalal bin Uwais da yaƙi wanda nice make son ya zama bawa gareni tamkar yanda nake baiwa ga Nasir."

Tana gama magana ya kwashe da dariya mai amo kafin ya turɓune fuska ya nuna ta da yatsa yace " Ya ke ɗiyata, ki sani kece tun farko kika yi kuskure na barin gadonki dan kawai kina son wani bil'adama wanda baima san da wanzuwarki a dogon duniyarba,na yarda da sharaɗin ki amma idan kema zaki yarda da nawa sharaɗin to haƙiƙa zan taimaka dan kare lafiyar Nasir shin zaki aminta da sharaɗin? "Ka faɗi sharaɗin ya kai Abbana ina jinka."

Cikin dakewa yace zaki fita daga addininsa kuma zaki auri Murazzam matsayin mijinki." Sai da ta zubar da hawaye sannan tace "Ya kai Abbana  ka sani tun ranar da Nasir ya kamu da soyayyar Bilkisu tun ranar nai bankwana da soyayyarsa ta aure daga zuciyata amma ko shakka babu zanci gaba da kare ahalinsa daga kowace barazana dan haka na aminta da auren Murazzam."  Tabi wani lungu ta shige wani ɗaki.

Tunda ya dawo daga aiki bai ga magen ba sai ya samu kansa da neman ta amma kamar wasa ya gaza ganinta dan haka ya fito waje yana dubata amma babu ita ba labarinta dan haka ya koma ya fara shirin tafiya gida domin yana don ganin Ibnarsa ne dan tsara hidimar saukarta jibin nan .
Ya fito bakin get kenan ya hango magen ta diro daga wata katanga samun kansa yayi da kashe motar ya fice kai tsaye ya kamota ya saka a motar ya ɗauki hanya .

"Baki ɗaya lamarinki Huraira ya kaini ƙarshe dan haka na samo maki islamiyar da zaki dinga zuwa ta safe da rana harma da date ko kin samu sauƙin lamarinki." (Cewar Malam Ahmad kenan) wannan karon Huraira bata musaba saima jinjina kanta da tayi kawai, to abin ya isheta itama da gaske take son Aljanu su daina bata wahalar banza .

Tunda yayi arba da ƴar Sarkin baƙaƙen Aljanu ya sake afkawa cikin wani yanayin na tashin hankali domin yafi kowa saninta ba ta da imani haka ubanta shaiɗani ne taƙadari ne da ƙyal Ashekarun baya aka samu nasara kansa yayi hijira zuwa dajin da babu wanda yasan inda yake tabbas bayyanarsa tashin hankaline ga fararen Aljanu.

Ya kama wajibi ya sace Bilkisu kawai ya kaita masarautarsa ya gana mata azaba ƙarshe yakasheta ya huta da takaici da ɓacin ran da ta sashi na tsawon lokaci.

To fa yaya kenan?

Mi zai faru a gaba ?
Ku bibiyi alƙalamin Haupha✍🏻

MAMAYAWhere stories live. Discover now