MAMAYA page 25

358 47 0
                                    

*👺🤡MAMAYA👺🤡*

*NA*

*HAUWAU SALISU*

*MAGA_TAKARDAN KAINUWA CE ✍🏻*


*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

07081095452

My Gmail👉🏻
*Hauwausalisu407@gmail.com*

My Facebook 👉🏻
*Hauwa'u Salisu(Haupha)*

My Wattpad 👉🏻 *Hauwausalisu*
https://my.w.tt/P1yNEVRFl3

Page ___25

Cikin tashin hankali Baba ya nufi wajen wani maƙwabcinsa, ya sanar dashi abin da ke faruwa gidansa ga matarsa Huraira, cikin jinjina lamarin Malam Umaru yace "Akwai wani Malamin da nasani ya ƙware kan wannan harkai, nasan dai aljanune suka rabeta to ko kaɗan kada ka damu indai yazo to komi zai zama tarihi , domin har yara garesa masu taimaka masa ko da ace aljanun mahaukata ne, to yaran zasu tayashi maidasu hankalinsu,sannan ya fitar dasu fit lokaci guda. Malam Ahmad yayi shiru yana jinjina maganar kamar dai akwai buƙatar nazari cikinta, shifa bai buƙatar harka da malaman nan na tsubbu fa, Malam Umaru ganin kamar Babansu Bilkisu nasan kaucema maganar sai ya fara gaya masa Malamin na kirki ne,aikinsa cikin ilimi yake yinsa dan haka ba wata matsala, muje da kanka a kira shi idonka ya gane maka. Sai kuma Babansu Bilkisun yaji ba daɗi mutum yayima abin kirki ka nemi turkesa, dan haka yace "Bawai haka nake nufi ba, Malam Umaru kaje daman ni yanzu zan wuce ne can gidansu ingayama ƴan'uwanta, nagode sosai da sosai. Ya wuce yana ƙara godema Malam Umaru da taimakon da zai masa.
Malam Umaru yayi murmushi domin ya tuno Malamin da zai kira shine wanda  yayi masa wani aiki kan yarinyarsa wanda yanzu haka tana gidan Malamin matsayin matarsa, kai tsaye bai koma cikin gidansa ba ya wuce gidan Malam Shehu mai Tawada, dan kiransa kan matsalar Huraira.

Malam Shehu mai Tawada, irin Malaman nan ne na zaure,ƴan tsubbu wanda basu iya komi ba sai kame-kame, wanda idan Allah ya bashi sa'a mace taje gunshi neman magani, sautari idan ya latsa yaji taushi to yana iya aikata alfasha da ita. To irin hakane shima Malam Umaru yarinyarsa ta kamu da shafar Aljanu sai matarsa ta kaita gunsa da sunan magani wanda shi bai san ankaita ba, sai da tafiya tayi tafiya komi ya kacame ciki ya bayyana jikin yarinya sannan labari ya iske shi wanda babu irin faɗan da baiba, ƙarshe dai cikin ya lalace, shi kuma yace Malam Shehun ya fito ya aureta tunda shine ya lalata ta. Tun daga lokacin yake neman hanyar da zai fanshe takaicin Malam Shehun amma bai samu ba, fatansa yanzu aljanun Hurairar su kasance masu karfi kuma masu mugunta yanda zasu rama masa abin da yayi masa na ɗirka ma ɗiyarsa ciki, ko daya aura masa ita ya bashi ne saboda ya riga ya zubar mata da mutunci duk wanda zai aure ta bazai taɓa ganinta da daraja ba balle mutunci, yana tafe yana addu'ar Allah yasa yau Malam Shehu ya gamu da gamonsa ya isa gidan, cikin sa'a ya iskeshi zaune zauren gidansa, kamar wani mutumin kirki yasha babbar riga ya kima hula sai zare idanu yake shi ala dole ga malam.

Cikin sakin fuska suka gaisa da juna daga nan Malam Umaru ya bayyana ma Malam Shehu mai Tawada abin da ya kawosa, ya ƙara dacewa "Ai abin da yasama nazo gareka dan nasan zaka iya dasu dan bata um bata um-um sai kallon mutane kawai ta sadda kai ƙasa, shine nace bari nazo na gayama kaje ka taimaka kamar yanda kasaba taimakawa ka rabata dasu. Sosai Malam Shehu yaji daɗin abin da surukinsa yayi masa tabbas yasan yanzu surukin nasa ya bar ganin laifinsa ko jin haushin abin da yayi ma ƴarsa, dan haka nan take ya shirya ya kira wasu yaransa uku suka nufi gidansu Huraira don cire mata aljanu.

Malam Ahmad kuwa yana zuwa gidansu Huraira ya iske yayanta ya gaya masa kasancewar iyayensu sun rasu, nan take yayan ya kama faɗa yace iskancin Huraira ya isheni Ahmadu kaje abunka ka rabu da ita kawai kana ƙoƙari da ƴar banza ai ni ban iyawa gaskiya naji da matsalai cikin gidana ma wallahi, haka kawai. Yayi ta faɗa kamar ya aro baki haka malam Ahmad ya fito yana jinjina faɗan yayan Huraira ya sake tabbatarwa da abun nasu a jini yake ashe.
Cikin sauri su Malam Shehu mai Tawada suka isu gidansu Bilkisu, banda addu'ar mugunta babu abin da malam Umaru keyi a ransa ta Allah yasa aljanun su nakasa malam Shehu, yayin da shi kuma Malam Shehu keta addu'ar Allah yasa mai ciwon irin wadda yake so ce ko mai komi ba yaɗan taba dai, ya dubi yaransa yaji kamar yace su koma karsu bashi matsala gun aiwatar da abin da yake hangen samuwarsa, amma daya tuna ance matar bata magana bata buge-buge sai yaji daɗi a ransa harda su murmushi ya shafa gemunsa. Sukai sallama cikin gidan Bilkisu dake ta uban kuka ta leƙo ta shaida masu Baban nasu bai nan, Malam Umaru ya dubeta da alamar tausayi yace "Bilkisu Malam Ahmad ne ya turomu ai, wannan shine malamin da zai duba ita Hurairar. (Ya nuna Malam Shehu mai Tawada dake ta ƙara gyarawa ) ta sadda kai ƙasa tace "Muje ciki to" suka mara mata baya zuwa cikin gidan.

Huraira tayi tumbur daga ita sai ɗan kamfai ta dage sai soshe-soshe take tana ihun Malam ya kawo mata ɗauki, tamkar ruwan sanyi haka taji an watsa mata wani abu, ɗub ƙaiƙayin ya ɗauke tamkar anyi ruwan sama an ɗauke, cikin sauri ta juyo dan ganin yima Malam tsogumin bai taimaka mata ba tun ɗazu sai yanzu data gama cin baƙar wuya mai azabar tsiya ? Bakinta ya datse idanunta suka fito waje, jikinta gaba ɗaya ya ɗauki karkarwa, ta kasa ko da numfashi mai ƙarfi, komi yayi tsaye cak, sai ido da take bin waje guda da kallo kawai.

To fa komi ya faru kuma ga Huraira?

Yaya zata kaya tsakanin malam Shehu da Huraira ?
Shin burin malam Umaru zai cika kuwa ?

Duk amsoshin naga Haupha kuci gaba da binta dan samun karshen balaƙalar nan.

*Nagode sosai taku ce Haupha* ✍🏻

MAMAYAWhere stories live. Discover now