MAMAYA page 20

570 55 3
                                    

*👺🤡MAMAYA👺🤡*

*NA*

*HAUWAU SALISU*

*MAGA_TAKARDAN KAINUWA CE ✍🏻*


*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

07081095452

My Gmail👉🏻
*Hauwausalisu407@gmail.com*

My Facebook 👉🏻
*Hauwa'u Salisu*

My Wattpad 👉🏻 *Hauwausalisu*
https://my.w.tt/P1yNEVRFl3

Page 20

Cike da tujara Huraira keta masifa gashi ta kama rigar ta riƙe gam, cewa take tana ƙarawa "Tsabar munafunci da kutungwila yasa ina zaman zamana kikasa matsiyacin yaron can mai kama da fuskar bajimin Sa, yaje ya tattaaroni ina kan gaɓar hayaƙin magani na, to daman nace jiki magayi ga duk uban da yai silar zuwana gun nan. Tayi-tayi taga ta janyo malamar asibitin nan amma ko motsi jikin malamar baiyi, maimakon ta shiga hankalinta sai tace "Baƙar munafukar Allah ta'ala, karfen gadon kika riƙe ko dan kar in ci uwaki da hujja ko ? Tana rufe bakinta taga hannun matar ya dawo bayanta kamar daman nan suke, "Ikon Allah kicema nakasassar banza ce mai sauƙin hukunci,kema da ganin sakakkun hannayen nan naki sauran likitanne ko ? Allah wadan naka ya lalace jakin dawa yaga na gida, to ni dai bari kiji in gaya maki wajen gaskiyar kinyi wauta  da kika sa aka ɗauko ni dan yau sai na huce haushina kanku har ƴar banzar can ta kwancen, mai ciwon ƙarya, dan ban ɗaukar asara ni aradun Allah.
Zuwa yanzu Aljanar ta gama fusata har wani hawayen baƙin jini ke zubawa daga idanunta ba ƙaƙƙautawa har ya gangaro ya ɓata farar rigar dake jikinta. Kamar wata zakanya haka ta juyo gaba ɗaya ta damƙi wuyan Inna Huraira ta ɗaga sama har bayan Hurairai na taɓo rufin ɗakin.
Dalalo idanuwa Inna Huraira tayi cike da razana ta kalli matar da tai mata wannan muguwar shaƙar da numfashinta ya kusa ficewa daga gangar jikinta, ai tana kallon fuskar matar sai taga yanda jini ke fitowa daga wasu manyan idanuwanta suna zuba har saman farar rigarta ba ƙaƙƙautawa sai ta dage ta kwartsa ihu iyakar karfinta tana cewa "Na bani na lalace kiyima uwayenki kiyi haƙuri aradun Allah ban san kece ba nasa likitace. Ita dai Aljanar batace ƙala ba ta dai ɗaga Huraira sama sai hawayen jini take tsabar takaicin abin da Huraira tayi mata yasa ta kasa daina zubda hawayen takaici, ba dan Yah Malam yace banda kisan kai ba da yau ba abin da zai hanata kashe wannan matsiyaciyar matar ba. Ita kam Huraira sai zunduma uban ihu take tana wutsil-wutsil da ƙafafuwa ta kasa motsin kirki, ta fashe da kuka tace "Ke yanzu dan masu garinku baki da tausayi ne ? Ki dage ki ɗaga tsohuwa kamata ki nunama sararin samaniya bako tausayi? To nidai nace maki kiyiwa uwarki da ubanki kiyi haƙuri ban san kece ba, haka kawai kin maƙale ni a saman rufin ɗaki..... Bata ida maganar ba aljanar ta sakota ƙasa, ta ko faɗo ƙasa timm.
Wata razananniyar ƙara tayi mai ƙarfin gaske numfashinta ya ɗauke alamar ta suma. Aljanar ta kwashe da dariya tace "Huraira kin tabka wauta domin nafiki turaja da masifa, tsabar turajata da masifata yasa ake kulleni duk bayan shekara saboda duk ƙarshen shekara nake sauke fushina kan ifiritai da bil'adama guda dubu goma wanda ciki nake nakasa wasu, ciki nake kashe wasu, ciki nake haukatar da wasu, amma yau kece kika sakani kuka bayan yau rabona da hawayen takaici shekaru dari bakwai da cas'in da tara da kwana tara, lallai yau hukuncinki na musamman ne gareni Huraira.

Tunda ya shiga office ɗin Dr.Isah yaji iska na kaɗawa mai sanyin daɗi ya iske Dr.Isah bai office ɗin sai ya kishingiɗa yana jin ciwon abin da akaima Bilkisunsa, ji yake tamkar yasa akai masa Malamin bariki ya sake labadtar dashi yanda yakamata amma sai Baba yayi masa karan tsaye ya hana, to waima ita yarinyar da tazo faɗin maganar miya hanata kiransa shi kaɗai ta gaya masa abin da ke faruwa batare da Baban yaji ba balle ya sani? Tabbas zai sa ai mata kashedin karta sake hakan duk wanda ya taɓa mai farin cikinsa kai tsaye zai gaya mata wanda zata faɗi mawa ai maganinsa, koda bai garin dole ne yaci uban duk mai takurama masoyiyarsa, yazama dole Bilkisu taji daɗi awaje tunda bata da huruminsa a cikin gidansu, itama Innar tasu Huraira ba idanuwa zai kawo ya saka mata ba tsira zaluntar masa mata ba, shifa ba dan kada ace suruki ya bugi surukarsa ba da ya jima da koya mata hankali tas zai sauke mata banzar turaja da faɗan iskancin nan nata, ta wani ɓangaren kuma nauyin Baba yake ji dan haka yake ɗauke kai ga musgunawar da take ma Bilkisun, amma fa yana jin ciwo a ransa iyakar ciwo, sai dai ana barin halas dan kunya. Haka yayi ta tunanin halin da Bilkisu ke shiga da nema mata mafita har ya ɗauki tsawon lokaci bai saniba, gaba ɗaya hankalinsa tunaninsa ya tafi inda zai samoma masoyiyarsa sauƙin rayuwa, sau tari yasha rayawa a ransa yayi ma Baba magana abashi damar fitowa ya auri Bilkisun ta huta ya huta, yayi nesa da ita zuwa inda zatayi rayuwar farin ciki, sai dai kuma tana yawan gaya mashi burinta tayi saukar Alqur'ani mai girma ta haddace sa sannan tayi aure, to yanzu dai saura kwana kaɗan tayi saukar saura haddar yake jira tayi sai ya fito suyi aurensu ya nesantata da garin yaga uwar da Huraira zata cuta. Wasa-wasa ya ɗauki tsawon lokaci yana saƙawa da kwancewa bai farga da yawan lokacin daya ɗauka gunba.

Dr.Isah na zaune yana rubuta magungunan da yakamata Bilkisu tayi amfani dasu yaji alamar tafiya kai tsaye an doso inda yake, abin da ya bashi mamaki sam bai ji alamar buɗe kofarba to tayaya aka shigo ciki? Yana wannan tunanin ya ɗago kai ya kalli inda yake tsammanin an shigo ɗin, ilai kuwa yaga wata mace jage-jage da jini sai zuba yake bai san daga inda jinin ke fitowaba daga cikin jikinta ba, gata wata ramammiya duk ta ƙyamushe jikinta babu alamar akwai tsoka ka kaɗan, baiga wata tsokar dazatasa  samuwar wadatar jini ta samu gareta har hakaba, amma ji yanda take zubda uban jini mai kyau, cike da alamar tausayi ya isa gareta kasancewar ta yanke jiki ta faɗi ƙasa "Sannu meke damunki haka? Kina zubda jini sosai kin samu haɗari ne baiwar Allah? Ita dai tana kwance ƙasa kanta kife bai ganin fuskarta sai jinin dake ta gudu kamar an ƙara tunkuɗosa, cike da tausai ya miƙe da nufin ɗebo kayan aiki sai yaji an riƙe masa ƙafa, ya waigo ya kalleta dan ganin fuskarta da yanayinta. "La'ila me zan gani haka? Baiwar Allah ke mutum ce kuwa ?
Ya sake kallonta yaga yanda hancinta ke wani zungurere bakinta wargajeje idanunta ƙananan gaske kuma cikinsu babu ɗigon fari ko kaɗan duk baƙi ne, sai wani uban kai kamar an haɗe kanunan mutane biyar masu girman kai, kunnuwanta kuwa buɗe suke yana iya hango yanda dodon kunnenta ke motsawa kamar wani ƙwaro. Hakan yasa bai san lokacin da yayi mata wannan tambayoyinba, cikin wani murya marar daɗin saurare tace "Nice Sambullazul Ayman nazo ka dubani ne saboda nasamu rauni kimanin shekaru takwas da suka wuce yau nasamu labarinka dan haka nazo kai mun magani. Kusan numfashinsa ɗaukewa yayi jin abin da tace, ya dubeta a firgice yaga fatace kawai a jikin bai ga alamar tsokaba to kenan jinyarce tasa tsokar barin jikinta baki ɗaya ko ko ? Ta ina zai fara ? Wa zai iya mata allura mema za'aima allura jikinta? Tabbas yau yayi mugun gamo.
Kamar tasan me yake nufi sai yaga tayi hamma tana rufe bakin ta zama wata dumemiya mai katon ciki amma kan ya koma mitsitsin gaske, ta dubesa da ƙyal tace "Kai sauri ka dubani likita ina jin ciwo ainun. Gaba ɗaya jikinsa rawar ƴan bori yake sai gashi zaune yana neman kamuwar da cutar sarkewar numfashi ta zamanin nan wato Corona (Covid 19) wata mahaukaciyar dariya ta kwashe da ita ta cacumeshi ta watsa cikin ɗakin hutunsa dake cikin office ɗin wani farin hayaƙi ya fito daga idanunta ya shiga jikinsa nan take barci mai nauyi ya ɗauke sa, tayi girgiza ta ɓace ita da jinin dake malale gun. Shine fa dalilin zuwan Major Nasir ya iske bai nan ya zauna shima ake ruɗarsa da iska mai kashe jiki har ya zauna yana tunane-tunanen yanda zai warware matsalar Bilkisu.

To me zai faru idan Bilkisu ta farka ?

Yaya Dr.Isah zai farka shima kota kasheshi?

Inna Huraira ya zata kaya da aljanar nan ?

Ko kufa dan Allah , yanzu da kuke ruwan comments ai Ni da ku duk muna darawa ko ?

*Taku ce dai Haupha* ✍🏻

MAMAYAWhere stories live. Discover now