MAMAYA page 38--40

472 59 4
                                    

*👺🤡MAMAYA👺🤡*

*NA*

*HAUWAU SALISU*

*MAGATAKARDAN KAINUWA CE ✍🏻*


*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

My Gmail👉🏻
*Hauwausalisu407@gmail.com*

My Facebook 👉🏻
*Hauwa'u Salisu(Haupha)*

My Wattpad 👉🏻 *Hauwausalisu*
https://my.w.tt/P1yNEVRFl3

My You tube channel 👉🏻https://youtu.be/h6gc8ahxrmM

Page 38-------40

Kai tsaye islamiyar ya wuce gun malam Surajo, bayan sun gaisa ya tambayi abin da ake buƙatar kowane ɗalibi ya kawo mai sauka. Nan take ya bada duk abin da aka buƙata ya bar makarantar, kai tsaye ƙaninsa ya ɗauka suka wuce kasuwa, babban rago ya siya tare da kaji masu yawa yaba ƙaninsa yace ya kai gidansu Bilkisun.

Gun kayan cefane dasu lambu ya koma yayi siyayya mai yawan gaske, ya nufi shagon Babansu Bilkisu ya bashi tare da kuɗi ya nufi inda ya ba da kayan Bilkisu ɗinki ya amsa ya wuce gida.

Kasancewar Inna Huraira bata lafiya kwance take sosai yasa Babansu Bilkisu kiran ƴan'uwansa da nata yace suyi aikin da ake yi tunda Huraira na kwance.

Gida ya kacame da iyaye da abokan arziki anata gyaran kayan miya da sauransu sai ga rago da kayan lambu,aka ce daga saurayin Bilkisu, sai iyaye suka saka guɗa, suna ta godiya da sa albarka.

Bilkisu na zaune ana kwance mata akai ana zana mata ƙunshi Nasir ya shiga da sallamarsa, ya gaisa matan gidan ya shige ɗakinsu Bilkisun dan bai iya shiga ɗakin Babansu.

Gaba ɗaya kunya ta kamata ta rasa yanda zatai sai sunne kai take tana murmushi.

Yana shiga ɗakin ya saki murmushi yanda yaga gimbiyar tasa sai yaji cewar yafi kowa dacen mata kaf zamanin nan .

Daman kayanta  ya kawo mata sai yace ta shirya zai turo ƙanwarsa ta rakata ai mata kitso da ƙunshi, dan haka ya fiddo kuɗin kunshi da kitson ya aje saman kayan yayi mata ƴar wasika ya fice yana murmushi mai ƙayatarwa.

Tana ta tunanin yanda zatai sai gashi ya fito ya aje mata takardar ya fice yana tunanin yau ina Innarsu take ? Ya ga anata abu cikin tsari da lumana ba tare da ta watsa gayyar ba, inko hakane to bari yau yayi amfani da damar ya tura ƙannensa gunta, shikenan ya wuce da gun.

Malam Aminu (Ɗan-bahago) ma ba a barshi a baya ba,ya siyo kaji masu yawa ya kai gidansu yasa a soya masa,domin kaima Bilkisu gobe idan Allah ya kaimu zai bata agun saukarsu.


Gaba ɗaya sun natsu suna jiran abin da zai ce masu,  ya dubi Badi'atul azam yace, "Ina san gobe duk yanda zaki yi ki yi, ki tabbatar da kin shiga jikin Bilkisu,ki tabbatar da kin aikata abin da zai sa a tsaneta a aibata ta cikin taron nan,ni kuma zan shiga jikin mahaifinta nasa shi ya wulaƙanta ta a wajen. Ya nuna wani baƙin Aljani yace, "Saduƙu kai kuma ka shiga jikin malamin nasu ka tabbatar da nemo laifi mai girma ka ɗora mata wanda mutane za su ƙara tur da ita.  Ya dubi su Shamwiylu yace, "Ku ne za ku shiga cikin jikin yaran gun Idan Badi'atul azam ta shiga jikinta ku nuna cewar ita ɗin mayya ce. Cikin murmushin mugunta ya nuna Rayhanatu yace, "Ke ce zaki siffar Innarta Huraira kije gun ki bayyana yanda take wahal da ke duk daren duniya.

MAMAYAOnde histórias criam vida. Descubra agora