MAMAYA PAGE 42--43

436 60 3
                                    

*👺🤡MAMAYA👺🤡*

*NA*

*HAUWAU SALISU*

*MAGA_TAKARDAN KAINUWA CE ✍🏻*


*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

07081095452

My Gmail👉🏻
*Hauwausalisu407@gmail.com*

My Facebook 👉🏻
*Hauwa'u Salisu(Haupha)*

My Wattpad 👉🏻 *Hauwausalisu*
https://my.w.tt/P1yNEVRFl3

My You tube channel 👉🏻https://youtu.be/h6gc8ahxrmM


Page 42------43

Baki ɗaya sai Bilkisu ta rasa yanda za tayi, da gaske ba fuskar Inna take gani a jikin madubin ba idan ta kalla, to mi hakan ke nufi kenan ?

Bai kamata ta sake tada ma Babansu hankali ba, domin ko yanzu bai zaune bai tsaye kan lamarin maganin Innar tasu, gashi Ibnah fushi yake da ita bai ko kiranta, balle ta nemi shawara garesa, amma fa duk rintsi duk wuya ba zata lamunci kalan wannan azabar ga Innar tasu ba, duk faɗan Inna duk mitarta yanzu babu, rabon da Innar ko ruwa tasha cikin daɗin rai har sun manta, dan haka zata samu mafita gaskiyar kan lamarin Innar tasu, domin ta jima tana zargin Innar tasu na ɗauke da muggan baƙaƙen Aljanu, kawai furta wa ne batai ba, amma yanzu anzo gun da zata ɗauki mataki da kanta.

Tayi shiru tana tsara dukkan matakan da zata ɗauka kenan taji an dafa kafaɗarta, cike da mamaki ta ɗago sai kuwa su kai ido huɗu da ƙawarta Shema'u Yahaiya ce ashe.

Bayan sun gaisa ne Shema'u ta dubi inda Inna take kwance ta yamutsa fuska tace ma Bilkisun, "Tun yaushe Inna ke kwance ne ba lafiya ? Bilkisu ta dubeta da fuskar mamaki,  "Amma dai yau baki jin dai-dai ko Shema'u ? Sau nawa kina zuwa kina duba jikin nata amma ace ke ce ke wannan tambayar ?

Kanta ta dafe Shema'un alamar mantuwa tace,  "Ke ni fa yau ki mun uzuri ji nake kamar ba ni bace yau, amma kuwa kun jaraba yi mata maganin Aljanu Bilkisu ? 
Girgiza kai Bilkisun tayi, "Ban da na asibiti babu abin da ake mata, dan Baba bai yarda da maganin ƴan tsubbu ba Shema'u, kwanakin baya da aka kira wani munga bala'i sosai a gidan nan ai.

Murmushi Shema'un tayi tace to zan amso maki wani magani gun Kakana, indai Aljanu ne ana kawo maganin zasu fara neman hanyar guduwa da kansu, amma fa ki sani idan sune ranar da na kawo maki maganin ba za ki yi barci ba, domin za su yi ta razanaki suna baki tsoro dan su ƙwace maganin daga gunki, sai dai kina tsorata to ki sani ba zata taɓa warkewa ba, kuma ke da ita har abada."
Tana gama maganar ta miƙe tsaye, "Na tafi Bilkisu sai na kawo maki, ki kula domin naga idanun ɗiyar Azam a gidan nan." (Tayi gaba ba ko waiwaye)

Duk sai Bilkisu ta sake shiga wani tunanin domin yau zuwan Shema'u yazo mata a wani kala, gashi sai sakin maganganu take waɗanda ta rasa gane kansu ita kwata-kwata ma.

Shema'u na zuwa zaure ta zama hayaƙi ta ɓace, tana gaggaɓa dariya mai ban tsoro, tana cewa, "Huraira zan taimakeki ne kawai dan Nasir na san yarinyarki, ba yan haka da na bari Rayhanatu azam ta cigaba da zama matsayin ke, ke kuma kina dajin mibrazul ladak, kina bautuwa.

Kamar yadda ta yi niyya a ranta, ƙarfe ɗaya na dare ta farka domin zuwa ta ga halin da Innar tasu take ciki, dan haka ta lallaɓa ta fice daga cikin ɗakinsu ta nufi ɗakin Innar tasu jikinta ko ina rawa yake kasancewarta mai shegen tsoro ga uban duhu daya mamaye gidan baki ɗaya.

MAMAYAWhere stories live. Discover now