Bissmillah Arahman Arraheem.Hasbinallah qarfe uku saura,barin tashi inyi Shirin makaranta kar inyi latti,keh Ruqayya kutashi kushirya mutafi makaranta kinsan malan Mahadi yanzu sai ya zane mu ba ruwanshi.Nikamma nashirya yawwa Fatima nima barin shirya mutafi.Karkumanta da safa dan wlh yau zanyi dukan safa da baje.
Khadija kenan da yaran dan uwanta Ruqayya da Fatima wanda tare suke zuwa makarantar islamiya, wanda dan uwannata ayanzu yake matsayin mahaifi a wajenta.Khadija diya ce ga Alhj Ibrahim Malunfashi Wanda akafi sani da Malam Ibrahim Mati.Malam ibrahim haifafen garin katsinane mazaunin qauyen Dankama,matanshi biyu Hajiya Abu da Hajiya Aisha,yaranshi goma sha biyu,Khadija itace autarsu diyace ga Hajiya Aisha amaryar Malam mati.Tun tana qarama Yan uwanta ke rububin daukarta wasu tsakanida Allah wasu Kuma saboda sonda mahaifinsu ke nuna mata,duk ciki dai babu Wanda Allah yabama ikon daukarda sai wanta dake zaune agari kaduna Mai suna Abdallah,alokacin bata shige shekara ukuba.Abdallah malamine a jamiyar garin kaduna wato Kaduna State University wanda akafi sanida KASU,Matarshi daya yaranshi mata hudu Ruqayya Fatima Amina da Aisha.Mahaifiyar khadija bataso hakanba hakama mahaifinta saidai bayanda suka iyada hukuncin ubangiji,Shike yin komai yadda yaso.Ta qaitaccen labarin Khadija kenan.
Kungama Shirin Khadija tace.Eh mungama anty,toh muje.Ina bude kofa sai naga mutum yana qoqarin shigowa kafin in dago kai sai Fatima tace uncle Hakeem,Fatiti ya kike ,lafiya lau.Nagaishe shi saina fice nabarsu da su Ruqayya suna gaisawa.Har nadau hanya sainaga basu fito ba naqwala masu Kira sai gasunan,naga alamun yau kunaso muyi lattine sainaga Hakeem ya biyo bayansu,muje in ajiyeku in dawo tunda ba nisa,dazance yabarshi sai nace toh har zan shiga baya sai yacemun shiga gaba ,ban musaba nashiga suma suka shiga yafara ajiyesu tukunna ya kaini.Makarantan dayake sashi biyu takedashi dana yara aji daya zuwa uku sai na manya hudu zuwa shida.Har zan fita sai ya riqe hanuna.Nur, nace naam,wai laifin me na mikine kike shareni,sai nace mishi,yanzudai kaga a qofar makarantanmu muke Kuma zanyi latti sai anjima nafisge hanuna na fice.Bayan na fita yakai minti biyar kafin ya tada motarshi yayi gaba.
Ina shiga naci karo da Malan Mahadi,Khadija nace naam malan zo ki karba baje na sabbin dalibai nasan nawajenki ya qare Kuma yau kuzo idan an idarda sallah keda sauran prefect din makaranta munada meeting daku,toh Malam.Hakeem qanine ga abokin yayana wanda duk mun zama daya dasu,mun daukeshi tamkar dan uwa ya nuna yana Sona nayarda dashi sosai.Tun ina qarama shi kadai nikema magana har yaga dariyata kasancewar banida magana sosai Kuma na tsani na miji yamun magana,amma shi mukan jima muna wasada dariya.Tun awannan lakacin yakan cemun amaryata inyi dariya kawai in kyaleshi.Bayan na Fara mallakar hankaleen kaina sai ya bayyana nufinshi nason aurena alokacin bai tunkareniba sai yasamu dan uwan shi sukai magana shikuma yasamu yayana sukai magana.An tsaida shawara akan zan aureshi amma sai nagama secondary School Kuma har sai na amince saboda yayana bazai tabamun auren doleba.Muna tareda Hakeem tun kafin yasamu aikinyi, bayan yasamu aiki a Abuja a qar qashin NNPC ,nanda nan arziqi yazo mishi abuna farko daya tsoratani da alamarinshi kenan duk da cewa Allah keyin yadda yaso amma Hakeem akwaishi da shige ma Manyan mutane.Yasha ya gwada bani kyautar kudi inqi karba,abun na bashi mamaki sosai duba ga irin zamanin da muke ciki Wanda samari ke iya shawo kan Yan mata da kudi har su cinma burinsu wa iyazu billah.Hakeem matashine farin bafulatani kyakkyawa Wanda kyanshi na daya daga cikin abunda ke qara sa shi jinkanshi da taqama tayadda Yan mata ke bibiyarsa,hakan yasa nakanji bazan iya auren Shiba.
Mun idar da sallahn Laasar munshiga meeting da malamai sakamakon ina daya daga cinkin dalibai masu kulada harkokin makaranta,bayan angama muka shiga ajujuwa muka sanardasu sabbin dokokin da aka kafa domin cigabar makaranta da gargadi akan duk wanda ya karya dokar makaranta zaa hukun tashi.Bayan munshiga aji munyi karatu zuwa qarfe shida na yamma aka tashemu.Nadau jakata na fito sai naji an dafani ta baya najuya sai naga qawata mubeenah.Tace haba Anisaty yau kwata kwata bangane miki ba tunda kika shigo aji hankalinki na wani waje,yau ko darasin da kikafiso baki maida hankalee akaiba na lura akwai damuwa atattaredake.Hmmm wlh mubeenah damuwace tamun yawa amma kinga yanzu mangariba zaiyi idan muka tsaya tadi akan hanya Kuma kinsan ba kyau idan Allah ya kaimu gobe a school zan fada miki abunda ke faruwa yanzu muyi sauri kafin yarannan su tafi gida su kadai ace na tsaya wani abune.Toh Allah ya kaimu goben ammadai ki rage damuwa da yawa.Toh qawata nagode.
YOU ARE READING
NURUL JANNAH
General FictionKirkirarren labarine akan wata yarinya mai suna Khadija wacce ake Kira da Nur.Irin rayuwar da ta tsinci kanta dakuma jinya datasha.Ku biyomu domin jin Ya labarin zai kasance.