Su Momy sun isa kasar Egypt misali 12na dare inda suka sauqa a babban birnin cairo.kai tsaye Asibiti aka wuce dasu,ankai momy dakinta ita kadai inda Kai tsaye likitoci suka hau dubata, Aisha itama an kaita dakin yara da farko ta fara kuka sai su baba suka shigo dakin,bayan taci abinci tayi bacci sai aka kaisu wani ban gare a cikin asibitin.Gidane aka yishi domin masu jinyar mara lafiya kasancewar majiin yaci kadai ake bari acikin asibiti.Ginine Mai kamada hotel da akayishi,kowani daki da lambarshi.Ciki babban falo ne da kitchen sai dakuna biyu,daya na yarane gado biyu ne manya aciki tsakaninsu wardrobe ne babba,sai master bedroom guda daya Mai dauke da qanqararren gado da Wardrobe aciki.Kowani daki da bayan gidan shi a ciki.Ba abunda babu a gida,kama daga kayan kitchen,kujeru, TV da sauransu.Wajen gidan akwai wajen wasan yara dauke da kayan wasa iri daban daban.
Sunyi wanka,aka kawo musu abinci daga hallal restaurant kusa da asibitin,naman kazane da gasasshen kifi,sai kayan fruits iri daban daban,kamar su inabi, apple, pear da sauran su,sai fresh madaran shanu da aka kawo musu.Sunci sunqo shi,sai sukayi sallolin da ake binsu,sai suka kwanta domin su huta.Can wajen momy ma hakane sun bata abinci taci sai suka mata waka dayake masu kulada ita matane kuma musulmai sun mata alwala dukda sunsan ba iya sallar zatayiba saboda bata gane komai.Haka wajen Aisha ma ya kasance sai dai ita goge mata jikin akayi saboda baaso a kunce daurin da aka mata.
Bayan da suka tashi sukayi sallar asuba basu farkaba sai misali qarfe goma na safe.wanka sukayi sukashirya suna fitowa suka samu an shiya musu abun karyawa, chips da soyayyen kwai sai madara mai dumi.Bayan sun karya suka fito domin komawa cikin asibitin.Har yanzu Baba da sanda yake anfani amma duk da haka zasu duba mishi qafar don su tabbata ba wata matsala da zata dame shi nan gaba.
Sun fara shiga wajen Aisha suka samu an kunce daurin da aka mata an sake wani.Sun dubata Daganan likita yashigo ya tanbayi baba ya suka kwana ya kuma qafannashi,duk da turanci suke maganar.Bayan sun gama gai sawan doctor ya buqaci ganin baba a office dinshi,ya mishi bayani akan momy sannan yaba shi wata takarda yayi signing domin asamu ayi mata aikin tun kafi abun yayi yawa.Yayi signing din shima sai akawa wuce dashi dakin duba qashi suka dubashi.Ba'a samu wata matsala gameda qashin shiba,kuma cikin kwana biyar zai fara taka qafarshi inshallah.Aisha ma anyi nasara qashinta ya hade dayake yarin yace har ta fara iya daga annun amma dai basu kunce daurin baki dayaba,sunce sai ya qara qarfi.
Anyi ma sau ran yaran general checking bawanda aka sameshi da wata matsala.Misalin qarfe daya na rana aka shigada momy dakin tiyata.Baba ya Kira qasa Nigeria ya sanar dasu sun isa lfy kuma an shiga da ita aikin.Sun mata addua sosai.Shima ba abunda yakeyi sai addua,haka yaranma ya sasu suyi ta mata addua.Anyi sallan azahar hakan yasa suka tashi sukayi sallah sannan suka cigaba da zaman jira.
Kusan awa uku ana abudaya.Misalin qarfe ukuda rabi likitocin suka fara fitowa daga dakin tiyatar kowanne dauke da murmushi a fuskarshi.Amma basu ce mishi komaiba.yana tsaye aka fito da ita aka kaita wani dakin daban aka sa mata ruwa,duk Yana biye dasu.Bayan sun gama komaine suka sanar dashi anyi aiki kuma anyi nasara.Inshaallah zata samu sauqi nan bada dadewaba.
Wasawasa yau kwanan su uku,suna samun kulawa sosai don har momy ta far fado amma Bata fara yin maganaba.Baba yafara taka qafarsa,Aisha ko tana iya tashi ta zauna da kanta kuma tana iya dafa hanunta don kafadar ta warke sai sauran abunda bazaa rasaba.
Cikin wata daya komai nasu ya dawo Normal.Baba na tafiyarshi cikin qoshin lfy,momy ma tana iya komai saida ciwo da kanta ke danyi lokaci zuwa lokaci amma likitoci sunce zai daina.
Keep voting⭐
The show is yet to begin.
Next page zamuji shin Khadija ta mutune Koh tana raye.kudannan star a qarshen kowani pagi don Allah. your vote mean a lot to me, comments are permitted.

YOU ARE READING
NURUL JANNAH
Художественная прозаKirkirarren labarine akan wata yarinya mai suna Khadija wacce ake Kira da Nur.Irin rayuwar da ta tsinci kanta dakuma jinya datasha.Ku biyomu domin jin Ya labarin zai kasance.