Mun koma gida daga gidansu Mubeenah kafin magriba saboda banason kaiwa magriba a waje,kuma Abbanmu zai mun fada.
Kwana uku da zuwa gidansu Mubeenah sai gata a gidanmu,taje suka gaisa da mama tasamu abba na gida shima suka gaisa.Tazo ta sameni a daki ina aikin da na saba(reading novels (one of Zainab Alqali's)).
Kina nan dai kina aikin naki koh?
Toh mekike so inyi,na dago kai ina kallonta,tayi murmushi kawai,
Yawwa ya batun tafiyanku yana nan kuwa
Hmm yana nan gobe inshallah,ga jakata chan har na hada Kaya
Kinsan meye habibty?
Sai kin fada🙄
Wlh banason tafiyarnan kawai dai banaso ki damu sosaine.
Ke dai bari,wlh jinake kaman nima bazan dawoba,kawai ki tayani da addua kuma inaso kisa a ranki duk inda nake bazan manta da keba,kuma ki yawaita mun addua.
Inshallah habibty,zan miki addua koda yaushe,kema kinyawaita yi.
Muka gama yima juna ban kwana tatafi gida.Natashi na cigaba da gyara sauran kayan da na fitar.
Yau ranar Alhamis,misalin qarfe shida na safe kowa nata safa da marwa acikin gida kasan cewar yauce ranar tafiyanmu.Tunda natashi banajin qarfi a jikina,ga yawan faduwan gaba.Na yawaita yin adduoi.
Misalin qarfe takwas kowa ya gama shiri ansaka kaya a booth din mota.Muka shiga mota ,muka dau hanya.
Mun tsaya a wani super market na cikin daya daga cikin gidajen mai na AYM Shafa,mun sayi drinks da snacks,muka qara mai sai muka cigaba da tafiya.
Munyi tafiyan awa biyar kafin muka isa garin bauchi kasan cewar hanyar ba kyau.Mun tsaya awani masallaci na matafiya mukayi sallan azahar muka cigaba da tafiya.Misalin qarfe biyu muka isa gombe mun dau hanyar Adamawa muna wani qauye mai suna Demsa,Bamu ankaraba muka ga wani abu ya yo kanmu da mugun gudu,sai salati kawai muke,kafin na ankara duhu ya mamaye ko ina.
Salam my voters and follower,ina matuqar farin ciki da irin son da kuke nuna ma wanna littafi nawa,sai mu saurari next page.Karku manta yanzu labarin ya fara akwai sauran runa a kaba.keep voting 😇
![](https://img.wattpad.com/cover/221799096-288-k601890.jpg)
YOU ARE READING
NURUL JANNAH
General FictionKirkirarren labarine akan wata yarinya mai suna Khadija wacce ake Kira da Nur.Irin rayuwar da ta tsinci kanta dakuma jinya datasha.Ku biyomu domin jin Ya labarin zai kasance.