Assalamualaikum warahmatulla wabarakatuhu.Jamaa kuna lahiya,Ina fatan komai lahilau,zamu cigaba.(not edited).
Continuation.......
Bayan sun idarda sallarne Khadija ta jawo abinci don yunwa takeji sosai.Bude kular tayi nurse din na kallonta,shinkaface da miya taji ganye ga kuma Kwan zabi guda shida a cikin wani leda.Juyawa tayi takalli nurse din tace ta sauqo suci abincin don dama chokali biyune aciki.Ai kuwa ta fada a daidai don itama yunwar takeji sauqowa tayi don bazata cutar da kantaba kuma taga abincin zai ishesu.Bayan sun gama cin abincinne nurse taimata godiya ta qara da cewa"wlh naji dadin a bincinnan rabo na da abinci tun qarfe goma na safe,na gode sosai".Khadija tace "ayya ba komai wlh nima naji dadi da kikaci don daman ban saba cin abinci ni kadaiba da bakiciba nasan qarshe in barshi ya lala ce.Amma nurse Dan Allah meye sunanki". Ta bata amsada "sunanan Halima,ke kumafa".Sunana khadija.
A haka dai suka cigabada tadi har Khadija tafara jin bacci.Nurse Halima tace taje ta kwanta ta dauko mata pillow a wardrobe din dakin.Khadijan malam ta shimfida tabarma ta kwanta ,sai ta rufe ido sai ta tuna da abunda ya faru dazu sai ta kasa bacci.Nurse Halima ta lura da hakan sai tace mata;"ki karanta uizuka bi kalimatullahi taamah minsharri ma kalaqa sau uku sannan ki karanta ayatul kursiyu ki hada da falaqi da nasi ki hada da qulhuwa ki tofa ki kwanta a hanun damarki ba abunda zai sameki Inshaallah".Ta amsa da toh sannan tayi adduar,cikin ikon Allah tayi baccinta lafiyayye.Nurse Halima kuma tana zaune tana kallon marallafiyar har likita ya shigo ya dubata sannan ya tambayi Halima ko da wani abu ta ce mishi babu juyawa yayi ya kalli Khadija yanda take baccinta cikin kwanciyar hankai ne ya burgeshi,sai ya kauda kanshi yace saida safe Halima ta amsa sannan yafice.A haka har bacci ya dauketa tana zaune.A gida kuwa bayan Malam Umar ya sanarda matarshi abunda ya faru a asibiti tayi ta jinjinawa tana tunanin diyarta,koh ya take koh ta iya bacci oho.Malam Umar ya Kira number likita yaji ya jikin yarinyar,nan ne yake bashi labarin tsoratar da diyarshi tayi.Bayan sun gama waya da likitanne ya ci abinci tareda matarshi suka Dan taba hira sannan suka kwanta.Bayan Aliyu ya dawo daga makarantar dare dayake zuwa koyama yara karatu,sai ya rufe musu qofa shima ya shiga ya kwanta.
Qarfe hudu da rabi Nurse Halima ta farka,ta tashi Khadija don lokacin sallar asuba ya kusa.Misalin qarfe takwas na safe Marallafiyar ta farka. Nurse ta taimaka mata tayi wanka da ruwa Mai zafi sannan Khadija ta ciro kayan da ta taho dasu a jaka aka samata,suka hada mata shayi Mai kauri suka bata, sunci saa ta sha sosai.Bayan ta gama Shane ta jinginu da gadon kanta na sama kamar me tunani daidai lokacin Malam Umar da matarshi suka shigo asibitin.Khadijace ta gaidasu sannan ta amso kular dake hanun mamanta ta ajiye.Nurse Halima ta dauko musu kujeru suka zauna.Tun shigowarsu Baiwar Allahnnan take binsu da kallo.
Suka gaisa da nurse,Malam yace,yajikinta nurse ta amsa da sauqi sosai don har mun mata wanka ta kuma sha shayi Amma har yanzu bata ce komaiba.Malam yace" inshallah zata samu sauqi yanzu ku karya kafin me gari ya iso sai muji yanda zaayi".Fita yayi ya basu waje nurse halima ta tashi zata fita matar malam tace ta zauna suci abinci,sai tace suyi haquri tanaso taje gida ta dawone don yanzu ba duty dinta bane Amma idan tayi wanka kafin su tafi zatadawo.Haka dai suka rabuda ita ta Khadija ta diba nata abincin,matar malam da diba ta ba marallafiyar.Taci sosai har ta fara bacci.Mai garine ya iso suka Dan tattauna da likita da Malam Umar,likita ya tabbatar musu da babu wani matsala sosai kawai addua zasu dage da magungunan garga jiya Amma kafin a fara mata magani ga wasu magun gunan saboda ciwon kai da zata riqayi Dana jiki su fara bata Tasha na sati buyu.A haka dai suka taho da ita gida har lokacin bata ce komaiba.Sun isa gida,dakin khadija suka kaita, aka bata magani sannan takwanta ta Dan samu bacci.
Vote vote and vote..... just keep voting.
Next page on the way.
![](https://img.wattpad.com/cover/221799096-288-k601890.jpg)
YOU ARE READING
NURUL JANNAH
General FictionKirkirarren labarine akan wata yarinya mai suna Khadija wacce ake Kira da Nur.Irin rayuwar da ta tsinci kanta dakuma jinya datasha.Ku biyomu domin jin Ya labarin zai kasance.