Bismillahirahmanirrahim
Continuation...........
Sun gama cin abinci an tattara wajen,Malam ya dauko litattafanshi Yana dubawa sai suka jiyo anata dariya daga cikin daki,abun ya basu tsoro.Malam Umar ne ya miqe inna na biye dashi suka shiga dakin khadija.Marallafiyarce tsaye a tsakiyar gadon sai dariya take gashi kanda duk sun miqe.Malam ne ya daka mata tsawa;
"ke zauna".
Ko kallon inda yake batayiba Ci gaba tayi da dariyarta.Karatun Qur'ani ya fara a lokacinne ta juyo ta kalleshi cikin murya me kamada ta maza yaji ance;
"Kai ummaru,ka rufa mana baki a wajennan ko kuma kaji jiki".
Beko kulataba ya cigaba da abunda ya keyi.Juyowa yayi ya kalli Inna yace a kawo mishi ruwa a kofi.Bayan ta miqo mishi ruwanne ya karba yayi addua ya tofa a ciki sannan ya watsa mata,ko gizau bataiba.Fita yayi da sauri ya dauko ruwan khal-Tuffah(Maulkhal, da turanci ana kiranshi vinegar)dama yariga ya yi adduoi a ciki, Yana zuwa ya zuba a hannunshi ya watsamata a fuska.Zama tayi tana wani iri qara babu dadinji.Idonta sukayi jajazur suka kafe kamar bana mutumba.Qafafunta ne suka juye kamar babu qashi a jikinta sai ihu take tana gurnani kamar wani zaki.
Malam umarne yace;"kar kusake ku karya mata qafa,idan Baku bar jikin yarinyar nanba saina illataku da ayar Allah.Tukunnama me ta muku,kuma su waye ku"?
Dif kakeji kamar nefa sun dauke wuta,Shiru akayi ko kukan da take ta daina saidai idonta sunanan a kafe qafartama bata dawo dai dai ba.can sai ta kwanta tayi wani irin miqa da attishawa.Basu sakejin motsiba.
Malam ummar ya matsa kusada ita ya dubata yaga idonta na bude amma kamar me tunani,sai hawaye da yake gangarowa daga idanunta.Yace mata;"sannu baiwar Allah". Ta daga kanta alamun tanajinshi."zaki iya tashi"?sai ta girgiza kai alamun bazata iyaba.Juyawa yayi ya duba inda Inna maryamu take yace;" Kira Khadija ku taimaka mata ta tashi ta zauna".Shigowa tayi suka kamata suka zaunar.Innace tafita ta debo abinci da ruwa ta dawo.Ta qara gyara mata kwanciyarta sannan ta fara bata abincin, ci take kamar ta shekara bata ciba.Saida tacinye aka qaro mata,taci sosai sannan aka bata ruwa tasha.
Malam ummar fitayayi ya koma dakinsa ya fara tunanin magungunar da zai hada mata.Bayan ya gama tunaninne ya Kira Aliyu;
"Naam baffa,gani".
"Anjima zamuje gona idan rana tayi sanyi, naga jiya kamar magaryar nan tayi ganye sosai,zamu debo inaso inyi aiki dashi".
Ya amsa da;"toh Allah ya kaimu".
"Ameen,Don lamarin nata sai a hankali.Naga alama idan bamu tare abun da wuriba zasu illatar da ita ne kawai".
"Baffa ina tausayawa iyayen yarinyar nan ko wani hali suke ciki oho".
"Allah shine masani.mudai fatan mu Allah ya bata lfy,tananne zamusan LABARINTA".
"Allah ya bata lfy".
"Ameen ya Hayyu ya qayyumu".Anyi sallar Laasar,waje yayi sanyi sosai,Aliyune da baffa suna tafiya suna Dan tadinsu na uba da da,har suka isa gonarsu dake bakin kogi.Gefe can wata bishiyar magaryace,baffa ne ya qarasa wajen yayi sallama sannan yayi bismillah ya fara ciran ganyen Yana miqama Aliyu Yana zubasu cikin wata yar leda.Bayan sun gamane suka Dan zazzagaya cikin gonar sannan suka koma gida.
Next page on the way.....
Thanks for voting
YOU ARE READING
NURUL JANNAH
General FictionKirkirarren labarine akan wata yarinya mai suna Khadija wacce ake Kira da Nur.Irin rayuwar da ta tsinci kanta dakuma jinya datasha.Ku biyomu domin jin Ya labarin zai kasance.