Nayi sallama aka ammsa na qarasa ciki nanemi waje a qasa nazauna na gaidasu gaba daya suka amsa.Wajen yayi shiru Kamar ba mutane can sai babana ya dago ya kalleni,Khadijatu, na amsa da naam.Sai ya gyara zamanshi yafara bayani Kamar haka,
Daman na kirakine akan maganar abunda ke tsakanin ki da hakeem,abaya munyi kuskure da muka yanke hukunci batareda sanar dakeba duk da hakan ba dolebane amma ni bazan so in tilastaki akan abun da bakyasoba,Don haka yanzu munaso muji daga bakinki kinason aurennan koh ba kyaso?.Nayi shiru kafin nadago kai nakali Hakeem idonshi yayi ja ko sodaya banajin tausayin shi.Na sunkuyarda kai na ce baba nasan bazaka taba cutar daniba nasan kafini sanin abu Mai kyau da Wanda bashida kyau don hakani zabinka shine nawa.Yakalleni yace hakane amma yanzu nabaki zabine Kuma banason dogon bayani don haka kinason shi ko bakyaso.Nasakeyin shiru kafin nace baba gaskiya banason shi. To Alhamdulillah kinga da yanzu kinsa na aikata abunda bashiba,tashi kije, Allah yamiki Albarka.Na amsa da amin natashi na fice.Naje nasamu momy a daki tana kishin gide akan gadonta nazauna a gefen gadon,tace ya akayi,na gayamata yanda akayi daga farko har qarshe.Tace toh yanzu kokefa da duk kinbi kin sa damuwa a ranki kina neman ki cutar da kanki abanza da wofi,kizo ki aureshi ya wulaqantaki ya fifita yar uwarshi akanki,ba gara ki nutsu ki qarasa karatunkiba kisamu ki tafi jamia koda aji biyu in kinkai kafinnan Allah yakawo miki mijina gari ki aura.Nace hakane .Yanzu duka duka shekara daya ya rage Miki kigama secondary School ki nutsu kiyi karatunki aure lokacine komai sai Allah yayi.
Nasihar da tamun ya shigeni sosai Kuma ta qaramun qarfin gwiwa.Nanda nan naji kamar an sauqe mun nauyi.washe gari da mukaje makaranta na sanar da aminiyata abun da ya faru,ta tayani murna sosai,tace toh yanzu kin rabu da chewing gum din da bazaki anfana dashiba.Qawata Allah ya zaba mana mazaje na gari ba zabin kanmuba,ta amsada Amin.Tun daga wannan rana Hakeem bai qara tako inda nakeba kwata kwata yarage zuwa Kaduna yazabi zama a Abuja.
Akwana Atashi babu wuya,har munfara registration din waec harna biya nawa kudin jarabawar.Muna zaune pc dinmu tazo taraba mana receipt dinmu muda muka biya.Da nakoma gida nakai wa babana ya karba ya ajiye yace Allah yasa ayi asaa.Islamiyama haka awannan shekarar zamu yi sauqa muta shirye shirye,kullum sai munyi rehearsals,sai yazamana bakoda yaushe muke zama a ajiba saboda yawancin littattafan mu mun gamashu.Hakanne yasa ba kulum muke zuwaba.Assalamualaikum fans haryanzu da qofa bude take😁😎 idan akwai maimun gyara kokuma bada shawara😇 kunsan dai nidin 9 nake bancika 10 ba🤓.Nagode🙏.Bazan barcewa aimun voting ba harsai naga voters suna qaruwa, keep voting.

YOU ARE READING
NURUL JANNAH
General FictionKirkirarren labarine akan wata yarinya mai suna Khadija wacce ake Kira da Nur.Irin rayuwar da ta tsinci kanta dakuma jinya datasha.Ku biyomu domin jin Ya labarin zai kasance.