Hakeem mutumne mai tsassauran raayi, yana yawan neman mata,kodan kyau da Allah yamishine oho,nan kinsha ganin don ko ke saida kika yaba kyan shi.Baban shi ya umur ceshi da ya auri cousin sistern shi wato Amnah,wannan maganar sai kwanannan nakejinta abakin yar sistern shi dayake muna good time da ita.Nur ashe dalilin dayasa amna ta tsaneki kenan?Wlh kuwa hakanne habeebty,akwai randa Amnah tazo har gida tasameni tamun Jan kunne akan Hakeem alokacin bansan meye a tsakanun suba,karki manta akwai ranarda Amnah tasa driver dinsu yakusa bigeni nafito zanje aika,irin wa innan abubuwan su sukasa nakaraya akan batun aurena da Hakeem don acewarsu ko ya aureni daga baya sai ya auri Amnah.Wannan maganar ko Momy Maryam bata saniba don nasan bazata taba yarda amun hakaba,Toh amma babanki yasani kuwa?bana tunanin yasani gaskiya.Hmmmmmmmm,Mubeenah tayi dogon ajiyar zuciya kafin ta dago ta kalleni,Aneesaty gaskiya akwai matsala a cikin wannan alamarin amma kicigaba da roqon Allah ya zaba miki abunda yafi Alheri.Nagode qawata Allah ya qara mana tausayi da soyayyar juna kema ina buqatar adduarki plc.Bakomai insha Allah zan tayaki.
Lokacin break ya qare muka koma class,qarfe biyu muka fito yin sallar Azahar,bayan mun idar muka koma domin yin extra lesson na minti talatin.Misalin qarfe uku dai dai muka tashi.Munfito nida Mubeenah bamuga motar malam mamman ba(Mai daukomu a makaranta) sai muka nemi waje Mai inuwa mukazauna jiranshi.Chan sai muka hangoshi yaqaraso ya dauke mu.yafara ajiye Mubeenah kafin ya ajiye ni.Na shiga ciki na cire uniform dina nayi alwala nai sallar laasar,sai nafito na shiga kitchen domin dibar abinci ganin abunda aka dafa sai daji duk gajiyar ta washe saboda naga abunda nafiso Kuma nasan momy ce tadafa da kanta.Farar shinkaface da ferfesun kayan ciki sai lettuce da tomatoes da aka yanka gefe Kuma alpple just ne.Na zauna a kitchen din saboda anan dinning table dinmu yake,naci Kamar bagobe.Ina cikin cin abin cinne saiga momy tashigo takalleni tayi murmushi.Eh dayake favorite dinkine ai babu mecemiki kici ko karkici,yanzu da wani abunne andunga biki kicikenan,toh idan kingama kizo main pallor ana jiranki.
Nan danan naji gabana ya fadi abincinma ya isheni,momy ta gane haka sai naji tace keh Khadija ki nutsu kici abincinki sannan Kuma ki kwantarda hankalinki ba abunda zai faru sai Allah yaso.Sai ta juya tayafi tabarni.nacigaba da cin abincin amma hankalina baa nutseba.Ina gamawa na sha ruwa na koma dakinmu nadauki hijjab dina na saka na nufi Fallon Baba.Anan natarar da Hakeem,Baba,da Baban ummi (brother din Hakeem).Fans kuyi haquri da late update,kasan cewar watan ramadana ya kama shiyasa najinkirta da rubutu,saboda watace Mai Alfarma Mai zuwa lokaci daya duk shekara,lokacine daya kamata mu koma ga uban gijin mu,mu gyara ayyukanmu mukuma yi istigfari, Allah yasadamu da Alkhairan da ke cikin wannan wata Mai Alfarma, Allah Kuma yayi mana maganin wannan cuta da ke damun mutane watoh corona virus (covid 19).vote vote vote and vote don't stop voting plc
![](https://img.wattpad.com/cover/221799096-288-k601890.jpg)
YOU ARE READING
NURUL JANNAH
General FictionKirkirarren labarine akan wata yarinya mai suna Khadija wacce ake Kira da Nur.Irin rayuwar da ta tsinci kanta dakuma jinya datasha.Ku biyomu domin jin Ya labarin zai kasance.