Page 7

160 18 0
                                    

Ji nayi an jefani gefe,sai karar fadawan abu cikin ruwa kawai kakeji.Daganan ban sake tuna wani abuba.

Wata babbar motace ta bugi motar su khadija, motarsu ta bugu da wata bishiya gefen bishiyar wata qaramar kogine ruwa na gudu sosai ,inda qofa daya yafita tagefenda Khadija take zaune hakanne yasa taji anyi jifa da ita cikin ruwa.sauran yaran kuma(ruqayya,Fatima,da Amina) sungangara gefen kogin basu Kai ga fadawaba.Aisha yar autansu na tareda mamanta.

Mutanen qauyen sunyi gaggawar isowa wajen da abun yafaru,anyi saa anfidda sauran mutanen cikin motar,an kauda yaran daga bakin kogin.Dukkan su basa cikin hayyacinsu.Baba ya samu karaya a qafa,momy ta bugu a kanta sosai,Aisha ta samu karaya a kafadarta,Amina da ruqayya basuji ciwo sosaiba sai suma da sukayi,Fatima bata bugu sosaiba sai kuka da takeyi.

Anyi saurin Kiran motar asibiti ta kwashesu.Bayan tsawon kwana biyu baba ya fara far kawa.yayi yunqurin ya tashi sai yaji zafi a qafarshi sai ya lura da daurin da aka mishi,dai dai lokacin likita ya shigo.

"Kayi a hankali kar ka motsa qafar"

Likita Dan Allah ina sauran iya laina?

"Ka kwantarda hankalinka suna qar qashin kula warmu".

Ko zan iya ganinsu?

"Eh ba damuwa".

Momy dakinta daban,an saka mata wasu naurori a jiki.Ta samu tabuwar kwakwalwa sanadiyyar buguwar da tayi,jini ya daskaremata a cikin kwakwal warta.Sauran yaran suna daki daya.Anyi ma Aisha dauri a kafadarta,sauran an goge musu raunukan da sukaji an basuba magunguna.

A wheelchair aka daurashi.An fara kaishi wajen momy yaganta hankalinshi ya tashi sosai,batama San inda takeba bata gane kowa,bata magana.Ya jima riqeda hanunta yana kuka yana mata addua kafin aka kaishi dakin yaran.Suna ganinshi sukasa kuka,yaje ya rungumesu su ukun dayake basu jikkata sosaiba sai ya shafa kan Aisha yace;

"Mamana ya jikin?"

Ta saka kuka,ya rarrasheta bacci ya dauketa.

Ruqayya tace;baba ina momy?

Momyn ku tana can wani daki daban anjima zamuje ku ganta.

Fatima tace;Adda Nur fa?

A nanne tunaninshi ya dawo ya gane cewa Khadija bata dakin da farko yayi tunanin tana wani dakinne itama sai ya ce musu tana wani daki yanzu zanje in dubata.Duk yawon da sukeyi tareda likitanne.

Ku jirani barin dubota indawo.Anne likita ya yi maga na

"Wacece kuma zaa dubo?"

Likita ai akwai sauran mutum daya,mu bakwai ne a motan akwai babban yata daya mai shekaru sha bakwai.

"Ku shida aka kawo asibitinnan".

Baba mamaki da tsoro ya cikashi.shin ina yar qanwarshi tashiga,karfa ace ta rasu.😥










Toh masu karatu ku dai cigaba da haquri da late update,am a business woman,ina famada customers shiyasa bana samun time inyi rubutu.A gaskiya banajin dadin reactions dinku yakamata ku riqa comments sannan idan akwai gyara ayimun.Nagode lots of love from Your unknown writer😁.

NURUL JANNAHWhere stories live. Discover now