Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin halittu,Mai kowa mai komai.
Ina mai baku haquri sakamakon jina da kukaji shiru,wani Dan matsala aka samu Amma biiznillahi ansamu mafita,kuyi haquri da jinkirin da nayi wajen typing.InshaAllah zamu cigaba daga inda muka tsaya.
I
Ina me qara miqa godiyata ga makaranta wannan littafi da kuma masu kada mun quria,na gode sosai Allah ya kara Mana fahimta.Continuation.......page 11
Hadarine yake qoqarin haduwa,ga wani iska me dadi da yake kadawa,tsuntsaye nata rera sauti.Wani Dan matashine keta safa da marwa a tsakanin wata gonar shinkafa,Yana qoqarin cire ciyawar da ke fitowa a tsakanin shukar.Gefe guda kuma wani dattijo ne da a qalla yayi shekara 65,Yana gan garawa wajen wani Dan qaramin rafi da ruwanshi ke tafiya a hankali.Qrasawar shi keda wuya ya hango wata halitta a saman ruwa.sai ya qarasa ya shiga cikin ruwan dayake bashida zurfi,ya miqa hanunshi ya jawo qellen da ke yawo a saman ruwan,sai yaga alamun fuskar mace yar matashiya wacce bazata wuce saar yar Shiba.Ya fito da ita daga cikin ruwan sai ya Kira wannan Dan matashin.Ya qaraso gurin dattijo yace gani baff........Ganin wannan baiwar Allahn sai yakasa qarasa maganar dake bakinshi.Kaje ka sanar da Mai gari a tahoda hukuma.
Hanzari yake tareda sassarfa,ya qarasa fadar Mai gari,ya kwashi gaisuwa sannan ya isarda saqo.A take Mai gari ya aika aka nema hukuma da kuma likita.Suka rankayo gabaki dayansu zuwa bakin rafin,nan suka tadda wannan dattijon zaune gefe Yana qarema yarin yar kallo.Da iso warsu suka tambayeshi yanda ya sameta,ya zayyana musu komai sannan ya koma gefe ya basu waje.
Wani Dan sanda ne ya sanya hand gloves ya dubata ko zaaga wani rauni a jikinta,alamar buguwa kawai ya gani a kanta bayannan babu wani rauni,sannan yaba likita damar dubata.Likitan ya fiddo kayan aikinsa ya fara mata wasu Yan gwaje gwaje,abun mamaki Yana duba bugun zuciyarta sai yaga alamun Yana tafiya daidai ,shaidar tana raye.Juyawa yayi ya kalli Mai gari yace mishi "yallabai,na dubata nima Banga wusu munanan raunukaba,abun mamakin shine tana raye domin zuciyarta na bugawa daidai".Mutanen wajen sukai hamdala tareda jimamin abun.Likita yajuwa zuwaga abokiyar aikinshi yamata izini da tazo ta matsa cikinta ko zaa samu ruwan da tasha ya fito.Matsowa tayi ta tsuguna tana danna cikin ta atake ruwa ya fara fitowa daga bakinta.Tasha ruwa kam ba laifi.
Bayan wasu mintoci saiga isowar motar asibita aka dauketa zuwa asibitin dake qauyen domun bata kulawar da ta dace don har lokacin bata farkaba.Asibitine babba kamar baa qauyeba,ko Mai tsaf tsaf,ga maikata ta ko ina.Ankaita emergency room domun abata taimakon gaggawa,likitoci ukune akanta Amma har lokacin baace ga abunda ya sametaba.
Gefe guda wani babban falone inda Mai gari da muqarrabanshi ke zaune sai Wannan datijo daya tsamota a ruwa mai suna Malan Umar tareda danshi mai suna Aliyu.Malam Umar babban malamine a qauyen,Yana bada taimako sosai musanman idan abu ya hadu da shafar aljanu.Yana bada magani irin na gargajiya,ya yi suna baa qauyen kadaiba harda qauyukan dake kusadasu.Malam Umar nada yara Su shida ya aurar da guda uku dukkansu mata sai qaramarsu da ke gida wacce bata shige shekara shashida zuwa sha bakwai ba,Sai maza su biyu da Aliyu sai Dan uwanshi Ahmad Wanda shine babba acikin yaran.
Alhamdulillah,
Page 12 loading....... keep voting.
![](https://img.wattpad.com/cover/221799096-288-k601890.jpg)
YOU ARE READING
NURUL JANNAH
قصص عامةKirkirarren labarine akan wata yarinya mai suna Khadija wacce ake Kira da Nur.Irin rayuwar da ta tsinci kanta dakuma jinya datasha.Ku biyomu domin jin Ya labarin zai kasance.