Alhamdulillah,yanzu babu batun aurena da Hakeem,zan cigabada rayuwata cikin kwan ciyar hankali.
Misalin qarfe biyar na yamma muna dawowa daga islamiya kasancewar jarabawar qarshe mukeyi baa karatu sosai a wannan lokacin kuma mungama jarabawar yau da wuri dake yayi sauqi sosai.A hanya nakeba Mubeenah labarin abunda ke faruwa,ta tayani murna sosai,tamun fatan zabi nagari.
A kwana a tashi ba wuya mun zana waec da jamb,hakanan munyi sauqan alqurani tartilan a makaranta,munyi walimarmu inda aka bani kyautar zuwa nabiyu danayi,gidama sun hadamun walima sosai anci ansha anmun fatan Alheri.Nasamu kyau tuktuka sosai Alhamdulillah.
Tundaga lokacin da aka yake alaqarmu da Hakeem ban qara ganin Shiba,yayi auren shi ya tare a Abuja.Tun bayan nan mutane daban daban suke tururuwar nemana amma ban basu damaba,atuna Nina inada sauran lokaci saboda yanzune nake chika shekara goma sha shida,nutsuwata da hankalina shikesa ana mun kallon babba.Mutane dayawa basa yarda da shekaruna sukance zurfin tunanina yafi na shekarun.
A yanzu banida burin da yawuce in samu admission a jamiar Ahmadu Bello University Zaria Dan in karanci fannin Islamic law(wato sharia law),Inadai ta kan addua.Yanzu hutun harya fara isana,gashi yau jummaa.Da yamma lokacin rana tayi sanyi na nemi izzinin zuwa gidansu Mubeenah,na dauki Fatima mukatafi dayake bamuda nisa sosai.Mun isa nasamu tana zaune a bakin gate ta ciki.
sannu mai gadi, kekuma yau ji kikai ki zauna a bakin qofa.
wlh kawai naji cikin ba dadine sai na Dan fito shan iska,ammadai batan hanya kikayi?.
wlh ba koh daya dama inada niyyar zuwa kawai dai fitan kemun wuya.Toh ya kk ya gida,barin shiga in gaida mama sai inzo naji nandin yafi iska.
Wlh mama ta fita,taje duba mara lafiya.
Waye ba lafiya?
Hajjiya ce.
Toh Allah ya bata lfy.
Muna cikin tadi sai na jiyo hayaniya awaje,na tambayeta lfy kuwa,tace,"wlh wai wani tsoho aka kama yayi raping yar shekara bakwai".Allah ya sawwaqe,tace amin.
Yawwa yar uwa jiya naji Abbanmu yana cewa zamuje yola akwai wani bincike da zai yi a qauyen manbila,yace zamuje muga qauyen idan ya gama da wuri mu dawo tare in bai gamaba kuma sai mu dawo mu barshi.Toh kice zaki je yawon bude ido.Hmm kedai bari yar uwa wlh banason tafiyar nan hankalina bai kwantaba.kedai kiyi addua kawai Allah ya kaiku lafiya.Toh amin.Insha Allah kafin ku tafi zanzo.Tohm bari mu koma kar magriba tayi,idan mama ta dawo ki gaidata.zataji inshallah barin rakaki.Ina godiya ga masu karanta NURUL JANNAH.vote vote vote plc.

YOU ARE READING
NURUL JANNAH
Ficción GeneralKirkirarren labarine akan wata yarinya mai suna Khadija wacce ake Kira da Nur.Irin rayuwar da ta tsinci kanta dakuma jinya datasha.Ku biyomu domin jin Ya labarin zai kasance.