Page 13

96 12 0
                                    

Assalamualaikum warahmatulla Fatan kuna lfy,zamu cigaba daga inda muka tsaya.

Continuation........

Bayan Khadija tayi sallarta ta idar tanacikin azkar dinta sai taga alamun marallafiyar na motsi kamar magana takeyi.Tashi tayi ta matsa kusa da ita ta kai hanu zata tabata kenan sai taji tasa wani irin qara Mai razanarwa,da sauri cikin tsoro ta janye a jikinta ta fita da gudu sai taci karo da wata nurse nan tace mata Dan Allah ta zo ta duba ta.
Cikin sauri nurse din ta shiga dakin tanashiga ta ga yarinyar azaune a kan gadon ta hada kaida gwiwa,sai ta matsa kusa da ita tasa hanu ta dago fuskarta sai taga idanun yarinyar sunyi ja fuskarta kuma ya canza kamar ba itaba,da sauri nurse din ta janye sai sukaji ta saki wani irin dariya mai qarfi dagaji ba muryan bil Adam bace,can kuma suka jiyo wata muryar daban tana cewa wlh sai mun dauketa sai mun kasheta.Khadijan malam ba abunda take sai kuka, nurse dince ta umurceta da taje ta Kira likita.
Da hanzari ya shigo kasan cewar shima ya nada ilimin addini sosai ,sai ya qarasa kusada ita ya dafe kanta Yana mata adduoi cikin saa surutan da takeyi ta daina,ya dauko alurar bacci yamata tun tana binsu da kallo har bacci ya dauketa a zaune.Kafin ya fita yace ma nurse din ta cigaba da kulada ita kuma kar tabar dakin saida kwakkwarar dalili,ta amsa da toh ya juya wajen khadijan malam yaga har yanzu kuka takeyi saboda ta tsorat sosai kasan cewarta me qaramin shekaru,rarrashinta yayi sannan yafita ya basu waje.
Yana fita nurse din taje ta gyra mata kwanciya sannan ta cema Khadija taje tayi alwala tayi sallar ishai don an Kira.Har lokacin da tsoro a tattare da ita.Toilet din dakin tashiga tareda yin addua tayi alwala ta fito, tafara sallah sai nurse dinma ta dauro nata alwalar ta jira ta idar sannan itama tayi sallar.

Likita na fita ya Kira Mai gari ya sanar dashi halin da ake ciki,dama suna tareda malam Umar don tun da akayi sallar magriba suke tare suna tattaunawa.

Bayan sallar ishaine suka cigaba da magana akan yadda zaa shawo kan wannan matsalar.Maigari ya fara da cewa:

"Da farkodai ina miqa godiyata ga Allah da ya raya wannan yarinya sannan kai ma Ina gode maka da kayi qoqari wagen ceto ran wannan baiwar Allahn.Abunda yasa na kirawoka kuwa shine,kasan cewar likita yace sai an hada da magani namu na musulunci yasa naga ya dace kafin ta farka musan shawarar da muka yanke wajen cigaba da kulada ita basai ta farka afara tunaniba.A matsayin na masanin magungunan gargajiya Dana musulunci Mai kake ganin ya dace ayi mata."Maigari ya maida kallonshi ga malam Umar.

Malam Umar yace;"Toh Alhamdulillah ga wannan jarabawa da ta zomana daga ubangiji,nidai a nawa tunanin afara mata maganin islamic idan ta farka tunda likita yace gobe zaa sallameta don zaman asibitin bashi da anfani.

Mai gari yace;"toh yanzu idan ansallameta gobe zata cigaba da zama a gidanka domun ta samu kulawa sosai don kasan yanda matana suke ba hankali kedasuba basu kulada kansu bama balle bare".

Malam Umar ya gamsu da abunda Mai gari yafada don haka ya amince da zaman marallafiyar a gidanshi don shima zaifi samu nutsuwar kulada ita.

Inaqara godiya karyadda na saba ga masoyana. Ida akwai gyara don Allah ku sanarda ni,i will appreciate that.

Page 14 loading........

NURUL JANNAHWhere stories live. Discover now