Page 12

134 16 0
                                    

Bayan awa biyu sai likitan da suka kawota taredashi ya fitoh ya samesu.A lokacin da ya fito sauran Mutanen sun watse daga mai gari sai Yan rakiyanshi su biyu sai Malam Umar da danshi.Likita ya fara kwararo bayanai kamar haka.

"A gaskiya yarin yar nan ta taki babbar saa da ta kasance a raye,koda yake dama dan adam sai lokacinsa yayi yake mutuwa.A Gaskiya ta dade a cikin ruwa don ba a wannan rafin ta fada ba ruwa ne ya gangaro da ita zuwa nan,da kuma yake Allah yasa tanada sauran rayuwa a duniya.Sai dai ba lallai a sameta cikin hayyacinta ba dole zata samu tabin hankali Amma idan ta samu kyakkyawar kulawa zata iya dawowa cikin hankalinta.Yanzu zamu bata nan zuwa gobe idan ta farfado sai muga yanayinta inhar baa samu wata matsalaba zaa mai data gida acigaba da bata kulawa da kuma adduoi don neman samun sauqi."

Maigari yace:

"Toh Alhamdulillah tunda dai tana raye ,yanzu ku ba wata kulawar da zaku bata anan kenan?"

"Ah ah,zamu daurata akan magunguna.sai ta farka zamu ga abunda ya dace a mata."

"Toh bari mu jira zuwa goben".

Malam Umar ya amsa da cewa:

"Shin ko anada buqatar me kulada ita zuwa goben?"

"Eh da so samune akwai yar uwarta mace kusa da ita don zata iya farkawa cikin dare".(Inji likita).

"Toh babu damuwa barin koma gida inyiwa me dakina bayani sai a turo Khadija ta zauna daita".(Khadija sunan diyar malam Umar kenan )

"Toh babu damuwa".

Bayan sun gama tattaunawane suka fito dukkansu tareda likitan suna cigaba da jimamin abunda ke faruwa.Likita ya barsu ya koma cikin asibitin.Malam Umar sukayi sallama da maigari ananne Mai gari yace Yana son ganinshi bayan anyi sallan magriba,kuma karya manta da turo diyarshi wajen marallafiyan,ya amsa da inshallah.

sunbar asibitin misalin qarfe biyar na yamma,da isarsa gida ya zayyanawa matarshi abunda ke faruwa,ta jimanta abun sosai nan take tausayin yarinyar ya kamata.Bayan sun gama magana da Malam dinne ta samu diyarta a daki ta sanar da ita abunda ake ciki itama taji tausayinta sosai,ta kuma amince da zuwa asibitin.

Hajiya inna wato Maryam matar malam Umar macece mai tsananin tausayi ga kula,bata cika fushiba tanada haquri sosai hakanne yasa malam bai da raayin Tara mata a gidanshi,shakaru bakwai da suka wuce ya auro wata mata Mai suna saratu,batada mutunci ko kadan ga masifa da balai ko shekara basuyiba ya sallameta Allah yaso babu haihuwa a tsakaninsu.Hakanne yasa yaji ya haqura da qara aure ya cigaba da lallabawa da matarshi tunda bata taba bata mishi raiba.

Kafin a Kira sallar magriba Baffa yace Aliyu ya raka Khadija asibiti wajen marallafiyar.Ta dauki abunda zata buqata kamar Sallaya,flask na ruwan zafi da kuma na abinci,sai kaya kala daya da hujabi da ta dauka ma marallafiyan.

Aliyu ya kaita har dakin sannan ya juya ya fice saboda an kusa shiga sallar magriba.Khadija na shiga dakin ta qarema ma yar budurwar kallo wacce ke daukeda drip a hanunta.A ranta take yaba irin kyau da baywa na ubangiji wajen halittar wannan baiwar Allah.Gata itama da kyakkyawar ce Amma da taga baiwar Allahnnan sai ta ganta mummuna a wajenta.

Ta ajiye kayan da ta shigo da shi ta shiga toilet din dake dakin ta dauro alwala ta shin fida Sallaya ta fara sallah.Bayan ta idar ta nemi tsari daga sharrin mutane da aljanu sannan tai wa marallafiyar adduan samun sauqi.Tana zaune taji sallamar likita,yace daman yazo ya duba ne ko akwai wani abu tace mishi babu sannan ya juya ya tafi.

Masha Allah,la quwwata illa billah.

Page 13 pending........ keep voting.

NURUL JANNAHWhere stories live. Discover now