Bismillahirahmanirrahim.
Bayan sundawo gida Malam yashiga Dakinshi ya fito da wani bokitin roba Dan madaidaici,Ya Kira khadija ta debo mishi ruwa a ciki.Bayan ta kawo mishine,ya dauraye gayaen magarya guda bakwai ya saka cikin ruwan sannan ya karanta Fatiha qafa bakwai sanan ya karanto qulhuwa da falaqi da nasi,sannan ya karanto ayatussihir a ciki sannan ya tofa acikin ruwan.Ya dauko wata qaramar jarka ya juye a ciki sannan ya miqa ma Inna yace wannan ruwan ariqaba marallafiyar har ya qare muga sakamako.Ta amsa sannan ta ajiye a dakinta don kartakai dakin Khadija wani abu ya sameshi.Zuwa tayi ta samo kofi me tsafta ta siyayi ruwan sannan taje ta bata da farko taqi bude bakinta, amma da Inna tai mata tsawa sai ta bude.Tai mata bismillah sannan ta bata ta shanye tas.
Khadijan ce a dakinta tana tattara takardunta domun ranar Monday zasu koma makarantar boko sannan ranar asabar su koma ta islamiya.Aliyu na waje Tareda wani Aminin shi Mahmood (Mahmood Ba a qauyen yakeba a cikin garin Adamawa yake amma saboda amintarsu da Aliyu yasa idan suna hutu yakan zo wajen kakanshi a kwauyen yayi kwana biyu). Malam ne ya fitoh ya samesu a bakin qofar, Mahmood ya durqusa har qasa ya gaisheshi da yaren fulatanci Ya amsa sanna Yace musu bari yaje fadar mai gari,ya wuce ya barsu.
A Fadar maigari,Bayan sun gaisa Mai gari ya tambayi "ya Mai jiki" ya amsa "da sauqi amma na musulunci",sannan ya bashi lbrn abunda ke faruwa a halin yanzu da kuma matakin da ya dauka na farko na bata ruwan addua.Mai gari yaji dadi sosai kuma ya jinjina wa Malam Umar,don ba kowa bane zai yarda ya zauna da yarinyar da baisan daga ina takeba kuma har ya bata kulawa.Malam Umar ya qara da cewa "ai da na kowa ne kuma wannan taimako da mukayi bamusan tarin alherin dake cikiba".Mai gari ya amsa da "hakane Allah dai ya tayaka riqo ita kuma ya bata lfy".Ya Amsa da "Ameen".
Anan sukayi sallar magriba da ishai sannan Malam ya dawo gida.Bayan ya dawone yake tambayar "ya Mai jikin babu dai abunda ya faru bayan tafiyata" suka amsada "eh bakomai,Tasha ruwan tana baccima"."Ince dai Baku barta tayi bacci da magriba ba Koh"?"Eh saida akayi sallah sannan tayi bacci bayan taci abinci".
Ya buqaci ruwan wanka yayi wanka sannan ya saka jallabiyarshi yaci abincin shi shi kadai saboda yau be dawo da wuriba.kasan cewar akwai wutar nefa sai ya kunna fanka ya dauko Al-Qurani ya zauna ya fara karatu,Tun daga baqara saida yakai Anam sannan ya yi adduoin shi ya tashi ya ajiye Qur'ani.Sannan ya dawo kujerar da Matarshi take zaune wacce tun be dade da fara karatu ba tashigo.Shafar fuskarta yayi sannan yace "ya akayi Matata".Ido ta kafeshi da kallo sannan tace "Ba komai
mijina,Kawai yau naga ka jima a wajene kuma baka sababa". Murmushi yayi sannan yace"Mai garine ya tsareni da tadi bayan mun gama kuma sai na je hira wajen yar bazawarar Dana samo".Kunnenshi taja sannan tace"Ka kyauta ai,shine baka daukeni naje rakiyaba".A hakadai suka cigaba da raha da hiraraki irin na matada miji,har bacci ya daukesu.
A Dakin kadija kuma,tana zaune ta kasa bacci tanata saqe saqe.Sai ta tuna da waazin da malaminsu ya musu kan cewa idan kana tsaron abu Yana bibiyarka kuma idan baka addua Allah bazai tai makekaba,sannan yawan kwana da alwala Yana kareka daga duk wani sharrin dare.Tashi tayi da sauri ta dauro alwala tayi nafila sannan tayi adduoi ta kwanta.Nandanan bacci ya dauketa.
.................. Next page.................
YOU ARE READING
NURUL JANNAH
General FictionKirkirarren labarine akan wata yarinya mai suna Khadija wacce ake Kira da Nur.Irin rayuwar da ta tsinci kanta dakuma jinya datasha.Ku biyomu domin jin Ya labarin zai kasance.