page 8

166 17 1
                                    

                         Continuation............

Hankalin Baba yayi matuqar tashi,ya shiga tunani irida kala akan batan Khadija.Shin wani hali take ciki,tana raye ko ta mutu.Yana cikin tunanin ne ya tunada wayarshi.Ya kalli likita ya;

"Doctor ko zaa iya bani wayata idan tana tareda ku?"

"Eh barin koma office sai insa a kawo maka."

"Toh nagode."

Bayan likita ya koma office dinshi,ya daga waya ya kira daya daga cikin ma ai katansu.Cikin minti biyu wata yar budurwa ta shigo,ya bata umurnin zuwa ta qarbo wayar ta kaima baba.Bayan ta Kai mishine ya kunna yasamu da charji,sai ya kira number oganshi da farko,yana kira aka dauka.kasan cewar an sanar dashi abunda yafaru kuma yayi ta Kiran wayar bai samuba.

"Assalamu alaikum,malan Abdullah kana lfy ya jikin ya iyalanka?"

"Alhamdulillah sir."

"Masha Allah ya qarfin jikin kuma kuna wani gari ne."

"Alhamdulillah dai zamuce,ni na samu karaya a qafata, little daughter na kuma a kafadarta,sauran yaran basuji ciwo sosaiba,mata kuma abun ba dadi."

"Yi mun bayani meya sameta."

"Ta samu matsala a kwa kwalwarta jini ya taba sakamakon buguwar da tayi."

"Ya Allah."

Yayi shiru na tsawon wasu mintuna kafin yace;

"Zan yi magana da doctor Bashir na general hospital gombe state, kamar yafi kusada qauyen da kuke sai a maidoku cikin gari daga nan kuma sai insan yanda zaayi afita daku domin duba lafiyar ku musanman matarka, don a canne zaa bata kulawa yanda ya dace kuma gara atari abun da wuri tun kafin yafi qarfinmu."

"Nagode sosai sir"

"Ka Kira gida kuwa?"

"Yanzu nake so in kirasu."

"Toh ya kamata.Ya mamana (Khadija)ita ma ba abunda ya sameta koh."

Ananne baba yaji kamar yasa mishi kuka,kasan cewarshi namiji mai tawakkali da juriya sai ya danne.

"Sir Khadija bamu gantaba kuma bamusan inda tayiba,mu shida aka kawomu asibitin."
Yana qarasa maganar ya sa kuka baisan ma kukan ta fito ba.

"Inallillahi wa inailaihi rajiun."

Abunda ya iya fitowa daga bakin Baba Hashim (boss din baba)kenan.

"Abunda nakeso da Kai idan ka Kira gida karka sanar dasu batun batan mamana har sai nasa anyi bincike idan baa sametaba sai mu sanar dasu,muna fatan a ganta."

"Nagode sosai kuma zanyi yanda kace."

"Shikenan Allah yaqara muku lfy inshallah gobe da safe zaazo a daukeku,mun riga mun gama magana da likitan ku na nan qani doctor Bashir dinne ma satin shi biyu a nan."

"Toh shikenan mungode sosai."

"Godiyar ta isa haka Kai kaman Da ne a wajena.sai na kiraka."

"Toh sai anjima."

Ya katse wayar.bayan sun gama wane ya kira Alhaji Ibrahim (Baban su).Ya mishi bayanin abunda ke faruwa amma bai sanar dashi batan Khadija ba.Ya musu adduan samun sauqi da kuma miqa godiyar shi ga Baba Hashim,sai cewa da yayi idan an dawo dasu gombe za suzo su dubasu.A cikin ran Baba Addua yake Allah yasa aga khadija kafin lokacin da za suzo duba su.

Washegari misalin qarfe sha daya na safe motar asibiti guda biyu  da extra mota daya suqa iso qaramar asibitin dake qauyen Demsa.Ansa mama a mota daya Aisha da Baba a dayar motar asibitin.sau ran yaran kuma acikin motar doctor Bashir.Qarfe biyu da rabi suka isa gombe state general hospital.Momy na qarqashin kulawar likitoci kafin su tafi Egypt domin ganin likita.
Har kusan kwana hudu ana bincike akan neman khadija.Dan kwalinta kadai aka gani a cikin ruwa,hakanne yasa aka nemo masu shiga ruwa don neman gawarta amma baa
sametaba.Baba ya daure ya sanar da mutanen katsina halin da ake ciki.Sunyi jima min abun sosai sukasa a ransu Khadija ta rasu amma baa sanar da sauran jamaba,an dai sanar dasu ta bata.

Kwana bakwai  da zuwansu gombe su Alhaji ibrahim suka zo daga katsina domin duba lfyar su,kuma washe garin ranar ne su baba zasu tafi Egypt tare da iyalansa gaba daya.Yana samun sauqin qa far shi sosai don har ya fara gwada takawa, Aisha ma tana samun sauqin  karayarta sosai.

Page 9 loading😍🤩

NURUL JANNAHWhere stories live. Discover now