peg 8

292 20 1
                                    

💓💓 *((INDO AISHA))* 💓💓
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________________*
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻

  _A• W• A•_

_{{Al'umma writers_
_Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane   gsky al'umma sai dan Al'umma  Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}}_
https://www.facebook.com/Alumma-Writers-Association-101394218126525/?referrer=whatsapp
*_________________________________________*

              *LITTAFIN*
NAFISAT ALIYU FUNTUA
     ((Ummu fadimah))

_Nagode da addu'o'inku ga kakata nagode ina yinku over💋_

Peg 8

   *WACECE INDO AISHA*

Asalin su malam tijjani shine mahaifin Malam Umar yanada Mata daya wadda suke kiranta da yakumbo Sunanta Aisha yakumbo a'i macece me hakuri da son jama'a haka shima Malam tijjani yake suna zaune a kauyen gwaram ta jengeben jahar zamfara

   Kauyen gwaram manomane amma sumfi shahara a noman shinkafa da ridi
      Shima Malam tijjani yanadaya daga cikin wa inda suka shahara da noman shinkafa manomine sosai yanada yara biyu Garba da Umar
     Garba da Umar sunsamu tarbiyya me kyau daga iyayen su yakumbo a'i da Malam kamar yadda suke kiran iyayen nasu suntaso cikin kulawa da soyayyar junansu

    Abu daya ne ya banbantasu bayan girman shi garba mutum ne me son kasuwanci abinna na matukar burge shi ganin hakan yasa Malam mahaifin su ya hadashi da wani mutum acikin garin Gusau yana nuna mashi harkar kasuwanci cikin ikon Allah da yardar sa abu yayitayin albarka Alh Hamisu shine uban gidan garba yanayi mishi tsaron shagon shi da yake cikin kasuwar dake sabon gari gusau

     Sana'ar Alh Hamisu shine suna saida turamen atamfofi da shaddoji kowanne iri kake so abinyana burge Alh Hamisu yadda yaga garba yana kula mishi da dukiya sosai gashi shago Nata habbaka

    Saboda farin cikin hakanne yakira garba yake tambayar sa yanada budurwa yace mishi a'a yace umban takura makaba kaje gurin kanwar ka Hauwa'u Ku daidaita kanku
     Garba yayi kasa da kanshi yace to Alh. Nagode kuma insha Allahu zanje yace bakomi ainike da godiya

   Cikin ikon Allah saigashi cikin lokaci kankani sun daidaita Kansu kasance war garba kyakkyawane ajin farko gashi shima da 'yar wayewar shi daidai gwargwado
     Garba yashirya yaje kauyen su ya fadawa mahaifan shi sunji dadi sosai suka saka ma abin albarka

   Su Malam suka shirya sukaje cikin Gusau aka tsaida maganar auren su wata biyu cikin ikon Allah har lokacin yayi aka sha biki amarya hauwa'u tatare a gidanta dake kofar Mani Gusau Wanda mahaifinta ne ya mallakawa garba shi

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Shiko Umar yagaji mahaifin shine a noma shima yana yin nomanshi sosai
    Bayan auren yayanshi da shekara bakwai shima wani abokin mahaifin shi ya bashi Mata wato asabe Allah yasani baya son auren amma bazai Iya jayayya da mahaifan shi ba anan cikin gidan su ya Gina daki da Dan bayinshi sai ya zagaye da katanga

    Bayan auren shi da asabe asabe masifaffiyar macece kwata kwata bata ganin girman Umar kokadan rashin mutun cin yau da ban na gobema daban indade Allah ya ta kaita abun Malam Umar mutum ne me matukar hakuri da juriya

   Gakuma nasihar mahaifanshi a kullum yaje gaida su saboda suma sunsan halin da yake ciki

   Bayan wasu shekaru Allah yayiwa Malam tijjani rasuwa bayan 'yar gajeruwar jinya da yayi
   Garba yazo dashi da iyalin shi gurin gaisuwa don a lokacin yanada yara ukku babban shine Aliyu suna kiran shida haidar sai na biyu tijjani Mai sunan mahaifin su suna kiranshi affan sai Wadda take goyo mace Hafsat

Bayan shekara Tara da auren Malam Umar da asabe kuma har lokacin Allah bebasu haihuwa ba

  Ranar wata laraba da yake ranar kasuwar gwaram takeci Malam Umar yaje kasuwa ya hadu da wasu 'yammata su biyu kyawawa daga ganinsu kasan ba 'yan garin bane bakine

Ata kaice dai anan Allah ya hada Malam Umar da Usaina su biyune hasana da usaina biki sukazo Jangebe shine suka biyo masu zuwa cin kasuwa don suga gari su 'yan shinkafi ne

Bayan sunkoma Gida Malam yaje yasanarwa mahaifiyar shi tayi murna sosai tasa ma abin albarka ata kaice iyayen Malam sunje gidan iyayen usaina aka bashi ita saboda itama mahaifinta mutum ne kamili duk da yaso ya hadasu da 'yar uwarta amma Allah be nufa ba haka akasha biki amarya tatare a gwaram

    Sirikarta na maturkar sonta itama tana girmama ta asabe kuwa tana musguna Mata sosai itako hasana tana biye da ita sauda kafa

   Bayan watanni da auren su saiga ciki aiko ina wuta asabe ta saka hasana shiko Malam da yakumbo sunata tattalin ta
    aifa nan hankalin asabe yakara tashi tayi gidan aminiyarta tace Kawata ki taimake ni yalwa tace me yafaru tace shegiyar ciki gareta
   Cime ciki aiba muga tazama ba kinji tashi zakiyi muje wurin da za ashare mana kukammu wurin wani Dan tsubbu sukaje suka fada mishi komi yadauki wani magani yabasu yace kusa Mata a abinci

      Aiko hakace ta faru saida asabe ta zubarma hasana ciki hudu hankalinta timbe Kai kanta ba harta gane saboda duk Randa ta bata abu taci to ranar cikin bazai kwana ajikinta ba amma saboda kauda Kai irinnata bata taba fadawa kowa ba

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Bayan shekara uku abubuwa da yawa sumfaru ciki hadda rashin yakumbo dasukayi hasana tayi kuka sosai na rashinta

    Bayan rasuwar yakumbo komi ya kuma chakude Mata a lokacin ne kuma Allah yaba Gwagwgo asabe ciki ai murna kamar tayi me haka taci gaba da renon cikinta
    Aikin komi Nata yadawo kan hasana ahaka har lokacin haihuwa yayi ta haifi 'yarta mace me kamada ita sak

   Wani ikon Allah Ashe itama hasana tana dauke da Nata cikin bawanda ya farga saida yayi girma sosai asabe tayi yadda duk zatayi ta zubar da shi Allah bebata dama ba

Bayan wata tara itama ta haifi 'yarta mace murnan wurin malan kamar yayi me ga yarinyar kyakykyawa sonkowa kin Wanda yarasa ranar suna yarinya taci sunan kakarta wato *INDO AISHA* Sunakiranta da indo inda mahaifinta kekiranta da uwata wannan abu yanayiwa asabe ciwo tarasa yadda zatayi

      Takoma gurin malaminta tayi mishi bayani yace yanzu mekikeso ayi musu tace inda hali kawai akashe su  wash Allah wallahi nagaji typing wuya.....................✍🏻

*yaude gashinan nakara muku korafi yakare🤥*

Yawan comments
Yawan typing

Read & share pls👏
.

💓💓 *((Ummu fadima ce))* 💓💓

INDO AISHA Where stories live. Discover now