💓💓 *((INDO AISHA))* 💓💓
*LITTAFIN*
NAFISAT ALIYU FUNTUA
((Ummu fadimah))*_Wannan shafin me tsada ne saboda haka na mallaka miki shi 'kawa 'yar'uwa Aminiya ta Wato Karimatu Abdulhamid (Mommyn Meenal) marubuciyar AUREN LAGOS DA GIMBIYA NA'IM DA WANI JINKIRI
Allah yak'ara fasaha yaraya mana zuri'a ya albarkacesu Allah yabar k'auna ameeeen_*Pege 47–48
Mutuwar tsaye kawai yayi yakasa koda k'wak'k'waran motsine, kawaide yabita da kallo har tashige d'akinta ta rifo k'ofa to meye hakan kayi? Zuciyarshi ke tambayarshi shire bashi da amsar bayarwa amma nide ban saniba ko fans kunada amsar da zaku bawa Haidar? Nide banida ita.
Yadad'e atsaye acikin falon sannan yaja k'afafun shi da kyar yanufi d'akinshi, mutsssssss wani mema yasani damuwa da rashin dawowarta gidane dawwuri, gashinan abanza najama kaina raini agurin wachchan jaririyar yarinyar.
Maganarta ta k'arshe kawai me amsa kuwwa acikin kunnanshi, "_masoyinane mek'aunata dukkuww da kasan cewata 'yar k'auye sabo ba second ba_" besan sanda ya kaiwa gadon shi wani irin bugu duk ya watsar da fulaluwan kan gadon ak'asa, toni inama ruwanane? Inkinga dama ma kikoma gidan shi dazama, abinda yasani damuwa dama saboda Daddy ne amma ba ruwana da hidimarki, "Tofa fans kuzo kutayani gani Karna gani nikad'ai anya Haidar kaima baka afkaba to gamu ganide".
Ina shiga d'akina da sauri nasaka key ak'ofar duk da haka gani nake kamar zaizo ya bud'e k'ofar ya dakeni nakasa barin jikin k'ofar ina tambayar kaina Anya Indo baki zak'e dayawa ba, tab ni wallahi bamma san nafad'i wasu maganganun ba sai yanzu da nake tuno abunda ya faru.
Nada d'e ajikin k'ofar har saida naji na fara gyan-gyad'i sannan naja ledar kayana da na watsar ak'ofar d'akin, cikin wadrop d'ita na saka ledar sannan na shiga na watso ruwa ajikina nasaka rigar baccina kawai nayi addu'o'ina na kwanta.
Washe gari da safe wajen bakwai saura naji k'arar wayata wadda hagga Allah ni mantawa ma nakeyi da inada ita saboda ba damuna tayi ba, tsaki naja, saboda banyi niyar tashi dawwuri ba saboda ina fashin sallah, ko tsayawa duba mekiran banyi ba saboda nasande d'ayan biyu kode Zahra ko Anty Billy Helloh Sister wato kinsamu yaya shine kimmanta Dani ko?
Aiban san sadda nakai zaune ba saboda jin muryar da bantab'a tsammaninta ba, hello ko bakijinane? Inajikin sis wallahi tsabar murnace tasa nakasa cewa komi wallahi nayi kewarki sis irin sosai d'innanfa, "bawani kedai kawai kice kinsamu soja ahannunki kina juya shi son ranki shiyasa kika manta dani a'a wallahi sis kinsan da inada number inki da dole inkiraki ko? Aiko yaya kikace yabaki number na zaibaki wanne yayan tab.
Bangane tab ba? Kede kawai kice bakison kifad'a min sirrinne bayan naji komi ai ingaya miki jiya wallahi har tsallen dad'i nadingayi, duk ba wannan bade yanzu yaya jikinnaki da kuma babymmu? Babynku na ina? Ko Anty Billy ta haihune "dayake tsohon cikine da ita" ke dallah karki maidani yarinya barganin kina auren babban yaya kinsande na girmeki ko?.
Eh nasani amma bangane mekike fad'aba ni lafiyata lau fa, amma yaya yace wai bakida lafiya idanuwa nazaro tare da dafe k'irji kamar tana kallona, yaushe yace muku banida lafiya wallahi lafiyata qlau ni "jiyane Daddy yakirashi yace yabaki yatayaki murnar gama junior wec d'inki shine yace da kyar ma kika iya gama peeper d'in daga school d'imma Asibiti ya wuce dake akayi miki allura wai kina bacci.
Bansan sadda na fashe da dariya ba nace tab ammade gayennan ya iya tsari al Qur'an wallahi ni qlau nake, "to amma me hakan kenufi huumh sister kenan zamfad'a miki komi amma saikinyi min alk'awarin bazaki fad'awa Daddy ba, "nayi miki alk'awari sis wallahi bazan fad'a ma kowa ba".
Nan nashiga bata labarin komi tundaga ranar dana baro gidansu har zuwa yau bam b'oye mata komi ba saboda ta wuce haka agurina, shiru tayi batace komi ba hello bakijinane? "Huuhm inajinki abunne yagama d'aure min kai amma kinsan me kiyi k'ok'arin bin shawarasu zahra da Anty billy idan ma kina buk'atar k'ari zank'ara miki, meyasa baki bud'e whatsapp ba? hakanan wallahi ni wayar ma har mantawa nakeyi da ita tunda ya Bash yabani ita lokacin muna gab da fara exam shiyasa kawai na ajiyeta ok yanzu ki bud'e zansaki group-groups sosai wa'inda zaki k'aru ok zambud'e zuwa anjima insha Allahu "ok sun dad'e suna fira sannan sukayi sallama.
Mik'ewa nayi na gyara d'akina tsab sannan nashiga toilet na d'an watsa ruwa sannan nafito cikin kayan da muka siyo jiya ne na d'akko wata hap gown wadda da kad'an ta wuce gwiwata nasa shima saboda nasan bakowa agidan kuma duk cikin kayan ita kad'aice me d'an dama-dama gabam mirror natsaya fouder kawai nashafa sai ribon Dana d'aure kaina da shi fita domin gyaran gidan.
Da babban falon nafara sannan kitchen daga nan nashiga part d'in oga sai azzahar sannan nagama komi kitchen na wuce na d'ora girki inayi ina bin wak'ar da nayi connect da wayana da mp.
Sai wajen la'asar nagama najera komi akan dining nagyara kitchen d'in wanka nakuma yowa wando nasa wanda bekai gwiwa ba da t sheet marar hannu yanzuma kama kaina nayi da ribbon me kalar rigar jikina pink color, kawai saina fito falon gidan na kwanta kan doguwar kujera,.
Wayata na d'akko nabud'e WhatsApp aiko nayi sa'a Sister tana online aiko nan take tafara yin add d'ina a group group Dana gyaran jiki dana make-up dana girke-girke gakuma na matan aure kai groups masu yawa tasani har saida nace tabarsu haka.
Slm sisters ga bak'uwanan 'yar uwatace kuma Amarya gashi tanada kishiya pls kutaimaka kubata shawarar yanda zata kwaci angon nata, aiko nan kowa tashiga bani shawarwari iri-iri nayanda zan samu soyayyar angonnawa, hankalina ya tafi kamfirar da akeyi da irin shawar-warin da aketa bani wani abun ma insuka fad'a har kunya suke bani.
Kwata-kwata banji shigowar shi gidam ba nide hankalina yatafi kan chat sai de inajin kamar na takura juyowa nayi da niyar na gyara kwanciyata kawai naga mutum tsaye akaina yana k'are min kallo, ni shafma na manta da kayan dake jikina mik'ewa nayi Nima tsayen nace sannu da zuwa yaya nafad'a cikin wata irin murya wadda ni kaina bansan inada itaba.
Juyawa nayi na nufi d'akina danaga be amsani ba nayi tsammanin yau 'yan mulkinne akanshi juyawa nayi ina tafiya kuma ina Danna waya, idan kaga yadda hip's d'ina ke juyawa kai kace da gan-gan nake kad'asu, nikuma hagga Allah bammasan sunayi ba.
Aliyu Haidar kam mutuwar tsaye yayi yakasa komi har tashige cikin d'akinta, kanshi ya dafe yana kiran sunan Allah afili yafurzo wata irin zazzafar iska daga bakin shi, kujerar data tashi nan yakoma ya zauna yana me fatan Allah yasa tak'ara fitowa domin ji yakeyi kamar yabita zuwa d'akinnata. "Niko nace yau jaririya ta ya mutsa babba hahahahahahahaaaaa!.
Oho niko bammasan yanayi ba kan gadona na fad'a daret na cigaba da chat d'ina nacigabaa dayi har ina jin haushin me yasa tunda bam Fara chat ba da tuni anwuce gurin, saida naga yamma tayi sosai sannan nayi musu sallama na sauka nashiga toilet nashiga saida nakalli kaina ajikin mirror dake toilet d'in, nashiga uku na bade haka yaya yaganni ba tab.
Shiko Haidar baibar falon ba saida yaga lokacin salla yayi sannan yaje yayo alwalla yatafi masallaci, Allah-Allah yakeyi ayi isha'i yadawo gida, ko zai k'ara ganinta itako kunya ta hanata fitowa.
Haka de yagaji da zaman falon yaci abincishi sama-sama domin hankalinshi na kanta amma ko mekama da ita begani har wuce sha d'aya da rabi na dare sannan dole mik'e yayi d'akin shi, ranar de baccin shi ragaggene haka yayi tafaman juyi agado sai Chan dare sannan yasamu baccin ya d'auke shi, shima cike da mafarkinta.......................
*Wash wlh nagaji kuyi hak'uri da wannan ngd karku manta yawan comments d'inku shi zaibani k'warin gwuwar yimuku typing ngd*Don't forget
comments#
Vote#
Share#*Ummuhfadima@gmail.com*
YOU ARE READING
INDO AISHA
RandomLabarin wata yarinya da ta taso cikin wahala da azabtar wa akwai abin tausayi sosai da soyya me ratsa zuciya%