💓💓 *((INDO AISHA))* 💓💓
*LITTAFIN*
NAFISAT ALIYU FUNTUA
((Ummu fadimah))*_Inakuke masoyana shinko kunsan Nasake zuwa muku da wani k'awataccen littafi me cike da chakwakiya, huhmmh ai idan anasalla ba'a magana sister's nasan duk wanda ya mallaki littafinnan bazaiyi dana saniba kuma dole kayi nishad'i acikinsa kardenacikaku GIRMA YA FA'DI tofa shin girman wa yafad'i kamar yadda nace kuzaku bawa kanku amsa , kad'an daga chakwakiyar dake ciki d'ane yaga yarinya yanaso sund'auki dogon lokaci suna soyya, kwatsam sai akace yafito domin aurensu, shinefa yatura mahaifinshi domin ya nemo mishi aurenta, uban naganin yarinyar yaji aduniya ba yarinyar da yakeso sai ita k'arshede uban yazagaye ya aureta yabar danshi bud'e da baki tashin hankali ykk ganin abun zaikaya domin jin maza ki nemi UMMUHFADIMA ta wannan Number 09033587886 akan farashi me sauk'i mazaki mallaki naki domin kuwa tuni amfara biya._*
Pege 53–54
*K'AUYEN GWARAM*
Mashin d'in da yad'akko Gwagwgo yana fakawa ak'ofar gida, tayi tayi takasa sakkowa saboda kunsan k'afarta ta kumbure ga azabar ciwo tanayi mata, shiko me mashin yanata faman masifa akan ta sauka ko kuma ya jehota shi baruwanshi, haba d'annan kayi hak'uri mana bakaga yadda naketa faman k'ok'ariba Gwagwgo tafad'a kamar zatayi kuka toni ina ruwana haka kawai kimcikani da wari chan kinje yawon baranki ainide tsautsayi yasani d'akkoki wallahi, dayaga de tak'i sauka gashi safiyace ba yawan mutane sosai shikuma koda kud'i bazai iya tab'ata ba, jujjuyawa yayi yag ba mutane kawai yakarkato da mashin d'in ako ji kuke tim kamar anjefar da buhun masara, shiko beyi wata-wataba yaja mashin d'in shi yayi gaba abinshi.Wani irin k'arar azaba Gwagwgo tafasa saboda azabar da taji cikin k'ugunta gashi tafad'a akan k'afarta me ciwo har saida tayi k'ara 'karas, ihunta shiya fargar da mutane masu shirin zuwa kasuwa aiko nan take kafin kace kwabo gurin yafara cika da mutane, itako Gwagwgo sai ihutake saboda kwata-kwata bata cikin hayyacinta ita kad'ai tasan azabar da takeji a'kafarta da k'ugunta, wannan hayaniyar ita tafito da malam Sada da Malan Tsalha lokaci guda, ganin Gwagwgo dasukayi yasa malam Sada komawa cikin gida yayi kiran med'akinshi, tafito suka kama ta suka shigar da ita cikin gida kowa bakinshi cikin da tarin tambayoyi?
Matan da suka kama Gwagwgo zuwa cikin gida susuka taimaka mata inna Hassatu matar malam sada takawo mata tabar aka kwantar da ita, Baffa dake barci alaokacin saboda har lokacin jikin begama yimishi dad'i ba, cikin barci yaji anata haniya kamarma acikin gidanshine yasashi mik'ewa yafito domin ganin abinda ke faruwa, yana fitowa tsakar gidan yaga mata tsaye cirko-cirko ga Gwagwgo kwance agefe cikin wani hali saifaman ihu takeyi, da sauri yak'arasa yana subu'hannallahi Lafiya meke faruwa ne? Saboda shima Baffa Allah yayi shi mutum ne me bala'in sanyi da tausayi.
Jin maganar Baffa da Gwagwgo tayine yasa take yawwa malam zoka taimakeni k'afa zata cire wayyo Allah na Malam zan mutu kataimakeni karna mutu, kanta yak'arasa ganin halinda take cikine yakuma tada hankalinshi, Inna Hassatu tace malam bari inje inkawo ruwa ad'aureye mata jiki sai akira malam Buba ya duba mata k'afar k'ila had'ari suka samu, cikin alamun fita hayyaci Gwagwgo ke cewa shegiya tsinanniya tasanadinki na had'u da wannan masifa insha Allahu bazaki tab'a gamawa da duniya lafiya ba gantalalliya kawai yadda kikasa akamin haka amatsayina na uwarki insha Allahu kema ammiki mafiyinshi! Wayyo! Allah kutaimakamin wayyo zammutu, tofa mutane saifaman kalon kallo akeyi sabida kiwade yasan Gwagwgo gurin abuwa taje, to me tasa akayi mata haka wasukuma suna ganin kawai zafin ciwone da gigita suke damun Gwagwgo.
K'ananun magan-ganun dake tashi agurinne yasa Inna Hassatu cewa matan dake gurin yawwa mungode da taimakon ku Allah yasaka kuyi hak'uri duk kuna iya tafiya, shide Baffa yana duk'e agefe yana tofa mata addu'o'i, da d'ad'd'aya matannan suka fara ficewa duk dade ba haka suka soba sunso suji k'wam,
Kafin wani loakaci maganar halinda Gwagwgo tadawo aciki tuni ya bad'e k'auyen bare abuga k'aramin gari.
YOU ARE READING
INDO AISHA
RandomLabarin wata yarinya da ta taso cikin wahala da azabtar wa akwai abin tausayi sosai da soyya me ratsa zuciya%