💓💓 *((INDO AISHA))* 💓💓
*LITTAFIN*
NAFISAT ALIYU FUNTUA
((Ummu fadimah))Peg 39-40
*K'auyen Gwaram*
Rayuwa tatafi dad'i da akasin shi, Baffah yazama abin tausayi acikin k'auyen saboda kowa yasan halin da yake acikin gidansa, saboda kunsan yau da gobe ta wuce wasa.Wani dattijo nagani zaune yayi tagumi wanda gani d'aya zakayi mishi kasan wahalar rayuwace tasa sa wannan ya mutsewar, Malam sada ne yake ta sallama amma sam Baffah da yalula dogon tunani beji shiba saida Malam sada yatab'ashi sannan ya dawo daga dogon tunanin daya Lula.
Haba malam Umar wannan wanne irin tunanine haka nadad'e akanka Ina magana amma bakama San inayi ba, meye matsalar? Shiru Baffah yayi saichan yaja wata doguwar ajiyar zuciya bakomi malam sada muna lafiya ya iyali? Duk lafya yanaka iyalin?
Suma suna lafiya qalau kasha unguwa tafiya ba sallama saida nazo nemanka kamal yaronka kecemin aikayi tafiya, wallahi kam tafiyarce kwatsam tasameni amma don Allah kayi hak'uri, a'a aibakomi ya wajen mejikin aijikikam yayi kyau sosai don harma ankwance karayar, dayake yaje jinyar d'an'uwanshine da yayi had'arin mota ya karye a a.b.u Zaria.
Niko Malam ya wajensu Alh. Garba da 'yar Baffah Indo nasande ina Chan kaje ko? Wani irin mummunan fad'uwar gabane yariski Baffah, lokaci d'aya duk yafurgice kanshi yana wani irin juya mishi mak'oshin shi yabushe, k'wak'walwarshi naso ta tuna mutanen da malam sada ya ambata amma kuma wani abu yazo yatokare mushi duk wata hanyar tunanin shi, kafin kace me saiga Baffah yayanki jiki yafad'i idanuwanshi akakkafe.
Subuhanallahi Inalillahi wa'ina'ilaihir'raji'un Malan Umar, Malam sada yafad'a agigice, yana k'ok'arin d'agoshi amma yagaza saboda gaba d'aya jikin shi saki kamar gawa.
*Katsina ddukko d'akin Kara kunye garemu ba muda tsoro*
Abuwa anzama 'yan gida itama tafare bata da abokai sai su suby sune yaran me abincin gidan yanda suke shiga ta rashin mutunci gashi tanaganin yadda suke kashe kud'i kamar basu, san zafinsu ba ci banza ci wofi haka itama zasu siya Mata abu donsuyiwa mutum kyautar fivek tenk bawani abu bane.
Sannu sannu sai abun yafara shiga kanta dukkuwa dacewa mijinta be rageta da komiba saboda duk abunda yasamo akanta yake k'arewa amma ganin yadda su suby ke kashe dubbunnai saita ke rainawa Haruna komi yayi araine kuma ba gode bare nagode.
Wataranar labara suna zaune a tsakar gida ita da maman Amira mak'ofciyarta suna fira Maman Amira take cewa niko amarya umbadamuwa inason nayi miki magana, lah bakomi inajinki, "dama akan yaddanaga kina son k'ulla alak'a dasu suby ne sainike ganin kamar bekamata ba amatsayinki na matar aure kinganninan tun ina Amarya nima nan aka kawo har na haihu kinga baruwana dasu iyakar mu gaisuwa tunda nagane ba mutanan kirki bane su".
Bangane ba mutanan kirki bane kawai don dekinga sumfi sona akanki shi kikeyiwa bak'inciki da hassada to wallahi saide bak'in ciki yakashe mutum ba, tayi tsaki ta tashi ta shige d'akinta, da ido kawai Maman Amira tabita tace Allah de ya kyauta mana shiyasa yanzu fad'ar gaskiya yake da wuya.
"Bayan sundawo daga yawon karuwancinsu suka bud'e tsarabarsu gasassun kajine sai jus-jus kala-kala masu sanyi, d'akin Abuwar akayi tsinke acan aka baje, akaci dad'i su kad'amma sukaci akabarwa Abuwa kura sauran,.
Anan take fad'a musu abinda Maman Amira tace aiko nan suka yita yiwa Maman Amira tsiya itade bata tanka musu ba, jin haushin tak'i tanka musunne sukaje suka fad'awa uwar d'akinnasu, k'arya da gaskiya suka fad'a mata, to dama ya lafiyar kura bare tayi hauka.
YOU ARE READING
INDO AISHA
RandomLabarin wata yarinya da ta taso cikin wahala da azabtar wa akwai abin tausayi sosai da soyya me ratsa zuciya%