💓💓 *((INDO AISHA))* 💓💓
*LITTAFIN*
NAFISAT ALIYU FUNTUA
((Ummu fadimah))*بسم الله الرحمن الرحيم*
Peg 1⃣9⃣➖2⃣0⃣
*Wannan Shafin nakune masoyan Indo Aisha wallahi ina matuƙar ƙaunarku Comments ɗinku yana ƙayatar Dani yanabani ƙarfin guywa ngd love you all💋💋💋💋💋💋💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻*
An d'aura auren *Haruna* Da amaryarsa *Zainabu* Allah yabada zaman lafiya, Kai wai bangane ba Dan Allah kutayani ji kode daga kunnenane kamar *Abuwa* Naji ance ba *Indo* ba kode nine banji da kyau ba, *Ilane* abokin *Haruna* ke wannan maganar, Wanda yake tambayar yace nima tambayar da zanyi maka kenan,
Tab akwai chakwakiya, bakad'an ba muk'arasa gurin *Angon* muga wanne hali yake ciki, Ga mamakin su sai suka iske haruna bakin shi harkunne yanata gaisawa da mutane, kallon-kalloh aka farayi tsakanin su, *Ila* yajashi gefe yace zomuje inason inyi magana da Kai,
Janshi yayi sukayi gefe yace kako San abinda ke faruwa? Kamarya? Wani Abu yafaru ne? Eh kakoji da wadda aka d'aura aurennan? Eh" nasani da *Zainabu* kokuma nacema *Abuwa* wato tauraruwar zuciyata wani shok" ne yad'ibi su ila salisu wani acikin abokannasu ya girgiza shi yace *Haruna* kadawo cikin hayyacinka bafa da *Indo* aka d'aura maka aure ba"
Ban son rashin mutunci wacece kuma me wannan sunan? Inde kuna so mushirya to kudena yimin maganar wannan, Dabbar! Dabba *Indon*? Mtsssssssss! Wani dogon tsaki yaja ya juya yayi tafiyar, shi yaci gaba da gaisawa da mutane cikin farinciki"
Tofa wai meke faruwa ne? Toni yaza'ayi nasani tunda tare muke da kai" kumafa hakane aide nanne gidan ɗan uwannaka Ko? Eh tabbas Allah de yasa ba wani abubane yafaru da shiba! To ameen"Aibazama zamuyi ba muje mugani ko, Atare suka fito daga motar *Daddyne* dashi da *Abba* cikin mutane suka kutsa sunzo gittawa ta wurin wasu sukaji sunacewa Allah sarki wallahi da ace inada kuɗi da saina auri yarinyar nan, aikaide kawai kabari ai Matar nan tacika mayaudariya, kuma maciya amana bayan azabtarwar da takeyiwa yiwa yariyar nan amma duk hakan be ishetaba harsaita hanata aure kuma wai umbanda abin kunya sai Yaya ta aure mane min ƙanwa"
Amma fashima *Harunan* da laifin shi, kai wallahi kudena ganin laifin shi ba'ahayyacin shi yake ba, to Allah ya kyauta.. *Daddy* kanshi ya ɗaure bakaɗan ba to waimeke faruwane?
Kunsan ƙauye abun magana bashi da wuya, duk inda su *Daddy* suka nufa saikaga Ana basu wurida haka harsuka isa cikin indasu *Malam Umar* suke zaune me unguwane kecewa kayi haƙuri Malam *Umar* wallahi bansan abinda ya haukan yaronnan ba jiya dayakoma Gida yake cemin wai shi baya son *Indo* kuma bazai aureta ba wai *Abuwa* yakeso Dana hanashi nace gabar wannan maganar ma ba me yiwuwa bace"
yanke jiki yayi ya faɗi, daya farfa ɗo zaice *Abuwa* in akace *Indo* saiya ƙara komawa wlh ahaka inaga ya suma yakai sau goma!..To kaji dalilin da yasa muka roƙi da aɗaura da *Abuwar* Malam Liman yace don Allah agafarce Mu itakuma *Indo* Allah yabata miji nagari Wanda yafi *Harunan* bakomi karku damu aiduk ɗaya suke da *Abuwar da Indon* amma Tunanina ayanzu yadda zanje na faɗa Mata bada ita aka ɗaura ba da ƴar uwarta aka yi Allah sarki mamana Ina tausayin rayuwar ki Allah gaggauta fito miki da miji, mafi Alkairi"
Karka damu ɗan Uwana Allah yabata miji kuma insha Allahu ina kyautata zaton yazamto Mata Alkairi"
Da sauri duk suka juya suka kalli me maganar da hanzari Malam *Umar* ya miƙe, Yaya Kaine kuwa Dan Allah karkuce min mafarki nake kutabbatar min da cewa Ɗan uwanane yazo gareni!..
Da sauri *Daddy* yayi wurinshi yace nine *Umar* nine ɗan Uwanka *Garba* suka rungume junansu suna masu fitar da hawaye saida suka karyawa kowa dake wurin zuciya! *harni saida na tayasu hawayen*
Me gari ne yayi gyaran murya sannan suka cika junansu amma sun kasa yinnesa da juna gani suke kamar za'aƙara rabasu,
Ikon Allah yanzu Kai *Garba* Ashe kana Raye amma ka kasa waiwayar Gida ko? Ayi haƙuri me gari wallahi inason zuwa abubuwane sukayi yawa amma insha Allahu hakan bazai sake faruwa ba to Masha Allah" ya iyalin komide Lafiya KO?
Alhmdulillhi" madallah Allah ya albarkaci zuri'a da nema duk suka amsa da ameeen, sannan duk suka gaggaisa da kowa, anan ya gabatar musu da *Abba* amatsayi aminin shi"
Malam Liman yace munji kace yarinya tasamu miji waye shi yace babban ɗanane *Aliyu* amma abu yayi kyau to shi yanzu yaron yana inane eh yanzude ya lagos domin sojane achan yake aikin shi to Alhamdulillah" amma aishiyaron baisani ba ko yace kawai a ɗaura ba wata matsala"
To Malam Liman bissimillah anan take aka tsaida mutane akace za'aƙara wani ɗaurin auren yanzu wa'inda basu tafi ba suka tsaya ganin ƙwam!..
Anan take aka ɗaura Auren *Aishatu Umar gwaram Indo* tare da Angonta *Aliyu Abubakar gwaram Haidar* sai muce Allah yasawa wannan aure albarka ameeen...............✍🏻
*please kuyi haƙuri da wannan damma karkujini shirune yasa nayi muku ngd*
Read & Share pls👏
Yawan Comments
Yawan Typing09033587886
YOU ARE READING
INDO AISHA
RandomLabarin wata yarinya da ta taso cikin wahala da azabtar wa akwai abin tausayi sosai da soyya me ratsa zuciya%