💓💓 *((INDO AISHA))* 💓💓
*LITTAFIN*
NAFISAT ALIYU FUNTUA
((Ummu fadimah))*_Assalamu alaikum 'yan'uwana masoyana masoyan book d'ina Ina yiwa kowa da kowa barka da salla Allah ya mai-maita mana yakaimu ta bad'in bad'ad'a da rai da lafiyar mu da wa'inda suka kirani da wa'inda sukayi min tex kaidama wa'inda basu kira ba duk Ina gdy Allah yabar zumunci, ngd sosai UMMUHFADIMA tanayiwa kowa fatan alkhairi_*
Pege 45-46
*K'AUYEN GWARAM*
Tun daga ranar malam sada yadage ya hana idonshi barci, yanata k'ok'ari akan Baffah saboda abun na matuk'ar damunshi.Baffah ma tunda yafarko daga suman da yayi tundaga nan bekoma dai-dai ba yawan shurunshi sai yak'aru fiye da da, yanzu saide kaganshi ya zauna yayi tagumi,
Yau dayake juma'ace bayan sundawo daga masallaci, Malam sada yashiga gidanshi, yace ina zuwa malam Ummaru, "to yace yasamu guri ya zauna kan dakalin dake k'ofar gidan, be dad'eba saigashi ya fito rik'e da rubutu acikin k'warya ya mik'awa Baffah amsa yayi yana jiran yaji k'arin bayani.
Kasha mana maganin meye? Had'a fuska yayi yace kana tunanin zan cutar da kaine? Umbazaka sha ba bani kayana, ya ida maganar yana kai hannu zai karb'a, a'a yi hak'uri abun bekai chamba Baffah ya fad'a yana kai maganin abakin shi, saida yasha sosai sannan ya cire daga bakin shi yana mik'awa malam Sada k'waryar, kauda kai yayi yace aiduka zaka shanye shi, bece komi ba ya kuma kaiwa bakinshi saida ya shanye shi tas sannan ya mik'a mishi k'waryar.
Amsa kawai yayi yajuya zai shige gidanshi saurin rik'oshi Baffah yayi yace haba Malam Sada fushin kuma na meye? Inde maganinne aide nasha ko.
Eh kasha ainaji kana yimin wasu tambayoyi ne kasande bazan iya cutar da kai ba ko? Eh nasani kayi hak'uri bari inje insamu in d'an kwanta saboda inajin kaina kamar yana d'an juya min. To jeka Allah yasawwak'e da ameen ya amsa sannan yamik'e yanufi cikin soron gidanshi yana had'a hanya, da kallo Malam Sada yabi shi yana me matuk'ar tausaya mishi mutum har mutum amma gaba d'aya yazama wani iri saboda illar sihiri, girgiza kanshi yayi yana menemawa d'an uwannashi amininshi kuma mak'ofcinshi lafiya.
*KATSINAN DUKKO*
Wata arniyar motace naga tayi parking ak'ofar shagon tabawa me abinci, wata farar macce ce tabud'o k'ofar motar ta fito tana wani yayya mutsa fuska, oooooooh hajiya Zeee kina wuta fa wannan arniyarfa wani kallon nafik'arfinku naga tana bin 'yammatan da suke Mata kirarin naga tabisu da shi, Niko nace tofa ikon Allah kuko daga ganin hajiya guda ta tsaya amotar ta sai kufara yimata irin wanna banbad'anc....... Ban kai k'arshen maganar da nakeyi ba naji wani saurayi yana tambayar su Suby wai wannan ba wannan 'yar k'auyen bace? Huuhm kaide bari kawai Ziko wallahi ita ai ingaya maka yanzu Abuwa tashigo gari sosai saboda tashigo bariki da k'afar dama.Bansan sanda na aza hannu akaba nace tab bade abuwar Gwagwgo me k'irar maza ba ta gwaram?, suka amsa min da cewa itafa, aida sauri nayi cikin shagon domin na k'ara k'are mata kallo, aikode ita ce amma saide wannan Fara ce tas domin har wani kashe ido takeyi, sannan ga 'ya'yan banki atare da ita duniya sabuwa.
Magana suke da hajiyar k'asa k'asa sannan naga ta d'ebo d'auri-d'aurin 'yandubu dubu ta mik'awa tabawa tace gashinan duk, yanda kukayi ki kira saboda ni daganan ma Abuja zamu wuce tare da Hajiyata domin tanaso waita nunani agurin k'awayenta.To shikenan Allah ya kiyaye hanya Hajiya Zainab, amma zaki biya ta gida ko domin kindad'e baki jekika ga Haruna ba domin ko d'azu kafin nafito saida yake tambayana wai yaushe zaki dawo, mitssss toke mekikace mishi? Yoni mezance mishi kuwa, zageshi nayi tas saikace yabani ajiyarki.
Mitsss kimmun dai-dai bar sakaran niyanzu banida lokacin shi ke bama shiba ni duk wani namiji yanzu baya gabana, maza mezasubaka umbanda wahala sai su d'irka maka ciki, amma hajiyoyi fa ga dad'i ga nera kibari kawai, dariya sukayi harda tafawa, _wa'iyazu billah Allahumma ajirnifiii masibati wakkalif'ni khairaan minhaa ya Allah katsare mana imanin mu damu da 'ya'yanyemmu da dukkan zuri'ar musulmi, wannan wacce irin musibace dake faruwa, me 'yar'uwarki mace zata iya yimiki mezaki samu agareta ummbanda tarin zunnubai Allah shirya duk masuyi yasa subari kafin lokaci ya k'ure musu ameeeeen_
*GWAGWGO*
Adai-dai lokacin da Abuwa tasamu duniya take bachaka da ita itakuma Gwagwgo tanachan durk'ushe gaban bokanta tana begin d'in bokanta akan ya binciko mata halin da 'yarta take, madubin tsafinshi ya d'auka yayi surkullenshi, saiga Abuwar acikin wani ma haukacin falo zaune tsakiyar manyan hajiyoyi sunsata atsaka, itako saifaman dad'i takeji.
Ai Gwagwgo bata san sanda ta fashe da kuka ba tana rok'on boka akan ya taimaketa ya binciko Mata inda 'yarta take saboda wallahi ninasan farrak'u akayimin da 'yata saboda umba haka bayadda za'ayi Abuwa ta manta dani, 'yarki tana garin Katsina a wata unguwa mesuna tudun 'yallihidda, wajen masallacin idi, daganan duk Wanda kika tambaya gidan tabawa me abinci yasani, ammafa duk abunda kika taras baruwana karkiyi kuka dani kiyi kuka da kanki, babu ma abinda zantaras sai alkhairi "shikenan kitafi rauhanai sukareki" duk'awa tayi har k'asa tace godiya nake me taimakona akan komi dabaka daban San yadda zanyi da rayuwata ba.
Hahahahahahahaha wata mahaukaciyar dariya yarink'ayi kamar zaifasa kogon dutsen, tashi kitafi kina cikin kariyar mu harki dawo ga wannan kiyi amfani dashi dai-dai sanda zakigana da 'yar taki, "godiyanake" wa'iyazu billah.
*LAGOS*
Kaina tsaye nashige cikin falon saboda kwata-kwata bantsammani ganin wani acikin mutanan gidamba, turus naja na tsaya saboda ganin megidan danayi saifaman kai-kawo da yakeyi acikin falon, k'arar bud'e k'ofar danayi ce ta ankarar dashi da sauri ya juyo yana, kallona.Ko k'ala bance mishi ba na cigaba da tafiya abina, keeeeeeeeeeeeh wata irin tsawar datasa saida nafurgita yadaka min daga gidan ubanwa kike? Kuma wane tsinanne ne yasauke ki amota? Duk da cewa na tsorata da yanayinshi kuma na firgita matuk'a amma duk da haka sai kawai nadake kwata-kwata ko afuskata ban nuna mishi cewa natsorata ba,.
Juyowa nayi fuskata dauke da wani murmushi wanda yafi kama da kai asuwa, wai badake nake magana ba saina tattakaki agurinnan, ok Ashe dani kake nayi tsammanin dakanka kake magana saboda banji kakira sunanaba; eh dakaina nake magana kinsan aini ma haukacine.
Sorry nibance ba amma koma daga Ina nake ai inaga bakada matsala da hakan ko saboda ba ajiyeni kayi bako sannan kuma bakowa bane ya saukeni ba sai masoyi abin k'aunata yaro sabon jini fil aleda wanda nizan b'are abuna, ba second hand ba, mesona tsakani da Allah duk dakasancewa ta 'yar k'auye, ta idasa maganar tana cigaba da tafiyarta zuwa d'akinta ko waigowa batayi ba saboda wani mugun tsoro ganitake kamar zai ma k'areta. Tab yanzufa za'afara wasan kude kubiyini karku Bari abaku lbr..................
*pls kuci gaba da hak'uri Dani de komi yakusa zama normal ngd gashide na dawo da k'arfina insha Allahu ammafa yawan comments d'inku shine zai bani k'arfin gwiwar yimuku typing kullum yawan comments yawan typing ahaaaaaaa*
Vote.
Vote.
Vote.*Ummuhfadima@gmail.com*
YOU ARE READING
INDO AISHA
RandomLabarin wata yarinya da ta taso cikin wahala da azabtar wa akwai abin tausayi sosai da soyya me ratsa zuciya%