💓💓 *((INDO AISHA))* 💓💓
*LITTAFIN*
NAFISAT ALIYU FUNTUA
((Ummu fadimah))Peg 27
Ranar Monday tunda nayi sallar asuba ban zaunaba nayi duk, Abinda nasan zanyi k'arfe 07:00am nagama komi, wanka nayi nasaka uniform d'in da yayi masifar, amsata azuciyata kuwa, bazan iya musalta muku farin cikin danake ciki ba saboda, "karatu" shine burina tun ina k'auye bare da na shigo, gari naga yadda mutane ke "rayuwarsu na k'ara tabbatarwa kaina tabbas ummutum", Bashi da ilimi beda wani amfani.
A tsaitsaya nasha ruwan tea kawai saboda d'aukin da nakeyi. Falo na fito rik'e da kofin dana gama shan tea da shi, dai-dai lokacin da megidan, shima ya fito wani irin fad'uwa naji gabana yayi, yabada rassss!.
Dandanan naji na daburce saboda bam manta irin tsawar, dayayi min shekaran jiyaba. K'asa nayi da kaina na wuce zuwa kitchen. Keeeeeeeeeee!
Da sauri naja natsaya jikina yana shaking d'in tsoro. Ke wacce irin dabbace? Umbanda jakanci da gidadanci irin na ba k'auyen mutum wanda yasaba rayuwa cikin dabbobi, kina ganin mutane bazaki iya gaishesu ba koda ba laifinki bane abunda aka saba da shine.Wani hawaye ne naji yana gangaromin akuncina me tsananin zafi, Maganganun shi sun bala'in k'ona min rai amma duk da haka banga laifin shiba kwata-kwata, tafiyata naci gaba dayi ko waigowa banyi ba har nashige cikin kitchen d'in, inajin dogon tsakin da yaja.
Shima Haidar kujerar dining d'in yaja ya zauna, cof yaja yazuba, tea d'in da yasha kayan k'amshi yaja kular da soyayyan arish potato da kwai, cikin kad'an yazuba aplat d'in yasoma kurb'ar tea d'in shi hankalin shi, akwance yana yi yana kallon k'ofar kitchen d'in, ko uban meta tsayayi acikin kitchen d'in? Ya tambayi kanshi, ohommata ma yoni meye ma nawa aciki tama tabbata a kitchen d'in damuwar tace.
Nide ina chan cikin kitchen d'in ina jiran yagama ya fita sannan nima na fito saboda arayuwata natsani disgi, shikuma wannan mutumin na lura Yana son yaga ya disga mutum.
Yagama breakfast d'in amma saboda neman fitina yak'i tashi ya fita ko meyake jira ohommishi, nock d'in k'ofar da akayi ne yasa shi mik'ewa, briefcase d'inshi ya d'auka, sannan ya nufi k'ofar falon.
Bud'ewa yayi Bashir ne atsaye shima cikin shirin shi nazuwa office, musabaha sukayi, Ashe kaima baka wuce ba eh wallahi yanzu nake shirin wucewa ya yaran da madam? Suna lafiya god muje ko? Ina office mana a'a niyanzu ba channayi ba saina fara ajiye Aisha a school tukun, ko k'ala bece mishi ba rab'ashi kawai yayi ya wuce,
Murmushi kawai Bash yayi sannan yanufi cikin, falon" dai-dai lokacin da nima na fito daga cikin kitchen d'in,.
Yaya sannu da zuwa yawwa k'anwata kintashi lafiya ko? Lafiya qlau yasu Anty tana gaisheki "ina amsawa" kingama shiryawa ko? Eh hijab d'ina kawai zan d'akko ok yimaza to mu wuce, da sauri ta shige ciki, school bag dinta ta daukko sai guntun hijab d'in ta wanda iyakar shi aka fad'arta sannan tasa whit sos and black shoes d'inta sannan ta fito.
A waje tasame shi tsaye gaban motar Haidar wanda yakasa tafiya ya tsaya shine bayan Bash yafito yaganshi betafi ba shine yaje yana tambayarsa ko meya hanashi tafiyar.
Shimade beda amsar tambayar sai de k'arya yayi mishi da akwai abinda yake jira, akawo mishi. Shikanshi besan abinda ya hanashi tafiyar ba, Niko nace kode indo ka tsaya gani🙊
Mota tashiga suka nufi makarantar. Ko inda yake bata kalla ba duk da zuciyarta taso ta cilastata kallon nashi amma, haka ta daurewa kanta.
YOU ARE READING
INDO AISHA
RandomLabarin wata yarinya da ta taso cikin wahala da azabtar wa akwai abin tausayi sosai da soyya me ratsa zuciya%