💓💓 *((INDO AISHA))* 💓💓
*LITTAFIN*
NAFISAT ALIYU FUNTUA
((Ummu fadimah))* kuyi hak'uri da kura-kuran dake ciki yau bansamu yin editing ba ngd😪
*Pege 41–42
Da sauri take bin bayanshi tana cewa dear ka tsaya ka sallami wacchan shegiyar agidannan don wallahi nagaji da zama da ita wallahi haushinta, nakeji don haka kazo ka medata inda ka d'akkota.
Shide ko k'ala bece mataba haka kuma betsaya daga tafiyar da yakeyi ba, amma azuciyarshi ji yakeyi kamar ya mammaketa, ita wai wannan wacce irin macece? Takama hanya tabar gida kusan two weeks, bata damu da yadda yake rayuwaba yaci ko beci yayayi da matsalarshi it's badamuwarta bace amma duk da haka be ishetaba, shine daga dawowarta, zata tada mishi da fitina agida.
“Ranta yayi mummunan b'aci na kyaletan da yayi, da sauri tabishi har cikin d'akinnashi, lokacin yagama cire kayanshi yanad'aure da towel, magana nakeyi maka fa ka kyaleni! To mekikeson nace miki? Aubakamasan abinda zakace munba kenan? Shide kallonta kawai yakeyi yana shafa sajen fuskarshi, dagaji da jinnacin datakeyimishi bata ankaraba kawai saijitayi yajanyo jikinshi sumfad'a tsakiyar bed d'inshi. Ta bud'e baki da niyyar tayi magana ya had'e bakinsu guri d'aya yacigaba da yamutsata, tana ta mutsu-mutsun kwace kanta amma ya gwada mata shi cikakken naamijine kuma soja.
"Be bartaba saida yasamu natsuwa da ita, sannan ya mik'e yashige toilet domin ya tsarkake jikinshi tanan a inda yabarta kwance sai kuka takeyi tana faman shashshekar kuka, harya fito daga toilet tanan kwance yadda yabarta haka yadawo yasameta abun ya k'ona mishi rai saikace wadda yayiwa fyde, jallabiyarshi kawai yasa ya wuce zuwa masallaci sallar magriba.
“Indo tanashugowa bayan wucewar Zahra kitchen ta wuce ta d'ora abinci, tuwon semo tayi da miyar d'anyar kub'ewa wadda tasha bushashshen kifi da naman rago, sannan tayi ginger juice, tasa afrige, sannan takwashe abincin tajera akan dining, ta gyara kitchen d'in tawanke duk abinda ta b'ata, kamar ba'agurin tayi aikinba komi yayi tsab.
'Dakinta ta wuce wanka tayi sannan ta d'auro alwallah, gaban mironta ta tsaya tana kallon kanta taga yadda yatsu suka kwanta akan farar fatarta, wasu hawaye masu zafi suka zubo mata akan kuncinta, tace insha Allahu saikinyi nadamar marina dakikayi shima med'aure miki gindi saiyayi danasanin duk abinda yayi min lokaci yayi da zankwatarwa kaina 'yanci amatsayina na 'yar adam, lokaci yayi da zan fara fratical d'in abinda Anty Billy kekoya min tabbas nayarda da maganarki Anty Billy dakikecewa idan harbanyi k'ok'arin kwatar 'yancina ba to zancigaba da fuskantar k'alubale iri-iri gashi kuwa inagani amma komi yazo k'arshe insha Allahu takai k'arshen maganar tana murmushi.
*Kauyen Gwaram*
Akid'ime malam Sada yaci gaba da girgiza Baffah yana kiran sunanshi amma ko motsi beyi ba, yarasa yadda zaiyi dashi kamar daga sama saiga malam tsalha Allah yakawo shi dawowarshi kenan daga daji yagansu cikin wannan halin da sauri ya ajiye kayan hannushi yanufosi yana tambayar lafiya,.
"Yanzude duk ba wannan ba taimaka min mushigar dashi cikin gida mayi maganar daga baya, tallatalla sukayi suka shigar da Baffa. Cikin d'akinshi dake a soron gidan ruwa malam Tsalha ya d'akko yashiga yayyafa mishi suna tofa mishi addu'o'i cikin ikon Allah saigashi ya farfad'o yana jan ajiyar zuciya me k'arfi.
Sai kalle-kalle yakeyi gadikkan alamude ba'acikin hayyacinshi yake ba addu'o'inde sukaci gaba da tofa mishi har barci me nauyi ya d'aukeshi, sannan suka mik'e suka fita k'ofar gida suka, barshi domin yasamu isashshen barci.
“Bayan sumfito daga cikin soron gidanne, malam Sada yakalli malam Tsalha yace shin meka fahimta daga ciwonnan na malam Ummaru?Aini tumba yauba na fahimci cewa baya acikin hayyacinshi ma'ana akwai sihiri me k'arfi ajikinshi, domin kusan duk wanda yakwana yatashi acikin k'auyennan yasan malam Ummaru ya chanja sosai, abun Yana damuna rashin samun wanda zamu tattauna matsalar dashine yasa kawai nayi shiru ina jiran dawowarka daga tafiyar nan da kayi.
Huuuuuuuuuhuuuuum wata doguwar ajiyar zuciya malam Sada yaja yace bakomi za'asan abunda za'ayi akai, amma nayi matuk'ar mamaki akan yadda sammu Yakama malam Ummaru, mutum meyawan ambaton Allah, aiba abun mamaki bane wannan shine jarrabawarshi saide muyi mishi fatan cinyeta.
Allah yarufa asiri aini tunda nadawo muka had'u naganshi ahargitse, jikina yabani ba lafiya ba amma dana tambayeshi sai yace min bakomi, aihaka yakecea koni nasha yimishi irin wannan tambayar ammade amsar d'ayace lafiya lau, amma yanzu meyakawo wannan matsalar ne? Kawaifa muna gaisawa shine na tambayeshi wajensu yaya Garba da Indo shinefa kawai ya shid'e min, Allah yarufa asiri "ameen de kashiga gida ka huta nima zanshiga ciki tunda lokacin sallama ya kusa, amma insha Allahu ayau zamfara aikinnan koda irin aikinan yanada matuk'ar wuya inji malam sada,". Bakomi Allah yasa afara asa'a ya amsada ameeeeeeen.
*KATSINA*
Wasa-wasa saiga Abuwa itama tafara zama star domin da k'arfinta tashiga barikin, batare da shakkar komi ba tunda dama tuni tagama da mijinnata domin yanzu duk wanda yaga Haruna sai ya tausaya mishi yayi bak'i yayi Rama sosai domin akwai ciwon dake cinshi arai wanda koshi besan wanne irin ciwo bane.
Ahakade yanajinshi kamar bashi bane ahakade adaddafe yasamu ya diploma d'inshi a 'yar'aduwa university dake katsina yau kimanin shekararsu hud'u kenan agarin katsina Allah yasani yanason zuwa gida amma yana tsoron tambayar Abuwa domin, akwai lokacin da megari ya aiko akan duk abinda yakeyi agarinnan to yabarshi yadawo gida, dayazo yafad'a mata fad'a tadinga yimishi harda cemishi duk ranar da yak'ara yimata maganar zuwa wannan shegen k'auyen saita cimashi mutunci.
Haka rayuwa keja Abuwa idan tabar gida bazata dawoba sai sha biyu nadare ko d'aya sannan azo ajiyeta a k'ofar gida kafin, kace me saiga Abuwar tak'ara chanjawa tazama farar k'arfi da yaji domin inkakalleta har wani kashe maka ido zakaga tanayi,
"Kud'ifa sunfara zama ajikinta ga hutu domin tuni tasa wani saurayinta ya chanja mata komi na d'akinta akasa mata placema tv k'atuwa bango guda da ac rayuwafa sabuwa, tuni tamance da wata Gwagwgo dake chan k'auye cikin begenta.Domin yanzu Gwagwgo hankalinta nakan Abuwa domin har boka tasa yaduba mata halin da 'yartata take ciki, abunku da matsafi tuni yabinciko ta yakuma nunawa Gwagwgo ita da irin daular datake aciki akan madubin tsafinshi, hankalin ta yayi mummunan tashi dataji cewa ai Abuwa ma tuni tamanta da ita ranar tayi kuka sosai kamar ranta zaifita. Dama ita rayuwa ai haka take Allah kasamuyi kuakykyawan k'arshe.....................
*Pls kuyi hak'uri da wannan babu yawa comments d'inkune ma yabani k'arfin gwiwar yimuku shi kucigaba da subur-bud'omin comments nikuma nadinga yimuku ruwan post*l ngd love you all my fans😍💋💋💋💋💋💋*
*Follow me*
*Wattpad Ummuhfadima*
*Instagram Ummuhfadima*
*Thanks*Ummuhfadima@gmail.com
YOU ARE READING
INDO AISHA
RandomLabarin wata yarinya da ta taso cikin wahala da azabtar wa akwai abin tausayi sosai da soyya me ratsa zuciya%