Page 01

1.9K 64 6
                                    

Doctor Laylah.

By: Safiyya (Mrs j moon.)

_Allahumma salli ala muhammad wa'ala alihi wa as'habihi wasalliman taslimin kasirah S.A.W._

Littafan marubuciyar:
Ruwan dare
A tunanina
Rayuwar Bahijja
Banyi zato Ba
Rabi'atul Addawiyya
Ra'ayi
Mabruka
Rashin jituwa
Bak'on lamari
Mutunci madara ne
Rumasa'u and now tafe da
Dr. Laylah.

(Labarin kagagge ne ba'ayi dan wani ko wata ba. Mallakan marubuciyar ne dan haka aguji juya mata labarin ta wani siga ko dorawa a wani wurin batare da izininta ba. Labarin Ba kyauta baya ne amma a kwai pages masu zuwa domin jin dadin ku masoya.)

01.

Tafi awa biyu tsaye a bakin windon d'akin ta, sam bata gaji ba hasalima hankalinta ya yi nisa da son samun cikar burin ta dalilin kenan da ya hana mata gajiya da tsayuwar. Tana nan tsaye aka soma kiran sallar subahi, ajiyar zuciya ta sauke tare da shafo fuskanta ta ja hancinta cikin lumshe ido ta furta "Lokacina ya yi da yardan Allah."

Bajimawa damar da ta ke muradi ya samu saka makon ganin fitar su Dady zuwa masallaci, cikin gaggawa ta fice d'akin ta sauka downstairs dik a hanzarce domin bibiyu ta rik'a had'a stairs. Ta bud'e k'ofar falon a hankali ta fice zuwa parking lot, batare da bata lokaci ba ta kunna motarta ta barshi a slow ta isa wurin gate ta bude ta dawo ta ja motar ta fitar waje sannan ta maida gate yarda ya ke ta bi ta k'aramin gate ta fice zuwa waje ta shige motar tare da harbata saman kwalta wanda ya fito tundaga babban titi ya shigo layin su.

Gudu ta keyi bana wasa ba sabida tasan dole ne abiyo bayarta da zarar suka dawo masjid suka sami labarin bata nan, bata fatar a sameta a hanya domin faruwar hakan nak'asu ne ga cikar burin ta. K'arfe tara da mintoci ta iso cikin k'auyen SHAGOJI. Koda ta iso k'ofar gidan su Mama Zainabu, parking ta gyara a k'asar bishiyar durimi mai yalwar ganye, ta kife kanta a saman steering wani zafi takeji na ratsa ruhinta, lamari ne da bata tab'a hasashen zai faru gareta ba amma sai gashi ya faru tamkar a mafarki.

'Ba zan raga masa ba, ba zan tab'a duba waye shi ba, wulak'ancin da ya yi min insha Allah sai na rama da abinda ke k'yan-k'yami domin shi ne babban makami na, zan shayar da shi dafin so wanda ke rintse ido akansa.

Momyna ban da burin komi a gareki face faranta miki to amma ta yaya zan soma?.

Dady affuwan dan Allah ka yacemin banyi dan ba...

"Laylatu! Ina ki ke ne? Laylatu fito inganki Hasken alkhairi."

Muryan Mama Zainabu ya karade kunnuwarta wanda ya katse mata zantukan zuccin da ta ke yi. Siririn tsaki ta ja tare da dagowa ta zuba mata ido batare da ta bude motar ba kamar yarda ta ke da buk'ata.

"Ikon Allah sai ji da gani, a she kuwa da gaske ita d'in ce, to maza fito mu shiga ciki inji abinda ya kawoki fatana dai lafiya kika dako wannan uwar sammako."

Bata fito ba haka batayi magana ba, sai kallon Maman ta ke yi da manyan idanunta wanda damuwa suka bayya cikin su, lamarin da ta ke bakin ciki da shi kenan domin inda abinda ta tsana to bayyanar karatun zuciyarta a saman fuskan ta.

Kama hab'a Mama Zainabu ta yi cike da k'osawa ta kuma cewa "Matsalata da ke kenan Laylatu wata rana kin fiye nuna shegen mulkin tsiya, to bari inyi miki kirari tunda shi ki ke so jikar saraki." Ta gyara tsayuwa kafin ta soma kirarin Laylah ta bude motar ta ziro k'afarta waje tare da lumshe ido jin iskan bishiyar ya kad'a tare da buso da k'amshin fureninsa.

Murmushi ta sa ki kad'an sannan ta fito ta yi arba da mata da maza manya da kananu sun ke waye motar ta, sai da ta d'aga glasses ta kulle motar sannan ta iso gaban Mama Zainabu ta rungume ta tare da sauke mata kiss a gefen kumatu. Taping bayarta Maman ta yi cike da jin dad'in ganinta.

Doctor Laylah.Where stories live. Discover now