Dr. Laylah.
14.
Laylah ce zaune tana shafawa hannunta tender care, kallo d'aya zakayi mata ka hango rashin walwala a tare da ita. Daga kai sama ta yi taja siririn tsakia karo na ba adadi.
"Laylatu kinga hannu ya warke tamkar ba shi ne ya kunbura ba."
Ta tsikayi maganar Mama Zainabu daf da ita, waigowa ta yi ta sa ki murmushi wanda baida maraba da ya k'e ta cigaba da shafa hannun batare da ta ce kanzil ba.
"Kai wannan mai na da abin mamaki ya ke, ga shi dan mitsitsi amma sai aiki, lalli nima inason in ajiyeshi ko idan an sami masu targade in taimaka da magani"
Murmushi mai sauti Laylah ta yi tare da mik'owa Mama robar tender care din ta ce "Gashi sai ki a jiye idan na sami mai zuwa zan karo miki wasu dan har da basir na warkarwa kya bawa Maman Maryama dan naji tana maganar basir na damunta."
"Ikon Allah ki ce wannan abu sunarsa komi da ruwanka."
Murmusawa ta kuma yi ta ce "Mama kenan kema ki rik'a shabawa lebenki da ke yawan bushewa."
"Angama Laylatu Hasken alkhairi."
Numfashi ta sauke ta ce "Jiya na yi magana da Musa idan na koma Kawu Alkasim zai kawoshi dan soma aiki da su Rahma, dazun na gama duba takardunsa baida matsala."
"Masha Allah dama ya kammala karatusa ba aikin yi, kinsan dik garin nan shi ne wanda ya tsallake makarantar gaba da secondary."
"Kema ida ace Kawu Alkasim ya kai irin matakin da tuni yana Kano rik'e da matsayi babba."
"Kayya Laylatu sam bazaku fahimta ba, bana son ya yi nesa da ni ne shi yasa."
"To ai gashin nan kiyi ta kallo kuma tafawa da shewa abinku."
"Gidanku na ce."
Ja baya Laylah ta yi tana dariya ganin Mama Zainabu ta kawo mata duka.
"Mama gobe zan tafi gida."
"Gobe fa?"
"Eh."
"Wani abu akayi miki?"
"A'a na daiga ya dace in koma ne."
"To tare zamu tafi dan in jiyo dalilin zuwarki a can tunda kinki sanar min."
"Da Maryama zan tafi in yaso ke sai kuzo da Musa."
"Na ce miki Maryama aure zamuyi mata."
"Da Musa ba."
"A'a yaron ciroma akayiwa kamenta tun tana tsumman goyo."
"Shi yaron yana son ta ne?"
"Ko bai sonta idan akayi auren zai so ta."
"Bada Maryama d'ina za'ayi wannan auren ba, tunda Musa ya nuna na ciki to shi zata aura dan yafi wancan komi."
"Laylatu dan Allah ka da ki sani jin kunyar mahaifiyan yaron nan."
"Mama yanzu fa ba irin zamanin ku ba ne da ake yin aure ko da ba'a san juna ba kuma a zauna lafiya dan haka Maryama Musa ta ke so, ta tabbatar min da haka shima na tambayeshi ya amsamin ita ce burinsa."
"Laylatu ka da ki had'a rigima tsakanin iyayen yara kinga tsatso daya suka fito Ciroma shi ya saki nono kakan Musa ya kama, kinga kenan Ayuba k'anin Uban Musa ne."
"Mama ni me ye nawa ciki? Kawai wanda yarinya ta ke so shi zata aura ba wani zancen had'a rigima ko b'ata zumunci, Allah na tuba ko Ciroman ke son ta idan ta ce ga wanda ta ke so ai dole ya janye balle d'ansa."
Zare ido Mama Zainabu ta yi baki bud'e.
"Kin san Allah Mama Maryama Musa zata aura, hankalin kowa yafi kwanciya da shi hatta da Malam ya tabbatar min Musa zai bawa Maryama domin ubansa ya taho da kansa ya nemi izini kuma ya amince masa."