Dr. Laylah.
13.
Har wayan ya yanke ba'a d'aga ba komawa ya yi ya kwanta kansa na kallon ceiling. 'Me Fatima ke nufi?' Ya ambata cikin ransa. Ya ja tsaki ya k'ara tsare gira "Doctor Noor da alama kaima matsala ce tarayyanmu. Ga shegen surutu kamar rub'abben mota." Ya watsawa k'ofar da likitan ya bi harara yana mai jin wani makakin daci a harshensa.
'Wai me ke damun ka ne Mahi?' Wani part na heart nasa ya jefo masa tambayar.
"Laylah." Ya ambata tare da da kaiwa k'irjinsa duka, ya rintse ido cikin hanzari ya dafe wurin da ya duka yana ambaton sunar Allah sabida jin da ya yi tamkar zai fasa heart nasa sabida yarda dukan ya shige sa.
"Zan nemoki bada jimawa ba kona huta da wannan shiriritan wofin da zuciyata keyi." Ya sa ke ambata cikin kaushin murya, sai kuma ya sakko daga gadon ya shiga bayi ya jima ciki sannan ya fito kansa na digan ruwa alamun wanka ya yi, goge sumarsa ya yi da sabon towel da ya gani a rataye a karfen gado, wata leda ya bud'e kaftan ne a ciki sabuwa dal ruwan madara sai kamshi ke fitarwa na turaren signature ya cillar da ledar kayan ya zube k'asa yabi ya taka ya fice daga d'akin yana cewa "Bana son shishshigi ko ce masa na yi ina buk'atar suturar sanjawa dan iskanci har da sanya daya daga cikin turarenta, anya kuwa bazan tuhumi mutumin nan inda Laylah ta ke ba? Du ba da yarda ya ambaci sunana kai tsaye tare da yi min hidima tamkar yaga d'an uwansa na jini." Shiru ya yi cikin nazari sai kuma ya zunkud'a shoulder gami da tab'e baki ya bud'e k'ofar. Yana fitowa nurses uku suka tare sa cikin jera masa tambayar abinda ya ke buk'ata. Kallonsu ya yi tamkar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce "Nagode amma ina son d'aya ta biyoni zan fidda kudi in bata ta bawa doctor Noor idan kuma cikinku da mai details na account nasa ya bani ina buk'atar wucewa."
"Amma yallab'ai ya ce ka da mu bari ka tafi sabida baka gama warwarewa ba." Cikin nurse d'aya ta furta bakinta na rawa sabida kwarjinin da ya yi mata, wanda wannan a jininsa ya ke cikawa mutane ido.
"Wanne zan samu ciki abinda na lissafa yanzu?" Ya share zancen tamkar bai fahimta ba.
"Bari mu kirasa muji daga garesa ko zai had'aka da Doctor Lukman."
"No banson yasan zan wuce, na roki wannan alfarman ku bar zance kiransa"
"Yallab'ai zaka sanyamu cikin matsala" Wata cikinsu ta ambata a hankali tana k'are masa kallo cike da k'auna.
"Zanyi masa bayani kafin ya iso gareku, kada ku damu kawai idan da account number din a bani."
Sanar masa sukayi a ta ke ya yi masa transfer na kudi mai yawa wanda ya ninka abinda zai iya nema dan hakkinsa dik kuwa son kud'insa.
Yana fitowa gate motar Baba k'arami na sanyo kai da sauri ya lab'e a bayan wata Jeep da ke ajiye daf da gate, suna shigewa ya fito cikin sa'a sai ga mai taxi bakowa ciki, ya tsayar ya shiga suka bar wurin a hanzarce.
'Bazan koma gida ba sai da farin cikin Magajin Gari's family insha Allah.' Ya ambata cikin jan dogon hancinsa cike da tunanin garin da zai sauka a karo na biyu.
"Yallab'ai ina muka nufa?"
"Zaka iya kaini garin Kaduna yanzu?"
"Eh yallab'ai amma zamu shiga da dare ne."
"Kada ka damu Allah dai ya kaimu lafiya."
"Amin."
*A asibiti.*
Saifullah sarai ya ga fitowar Mahi amma ganin ya b'oye bai son su gansa sai bai tona nasa ba amma ya cika da mamakin dalilin da ya sa ya gudu alhalin yana cikin rashin lafiya yana da buk'atar ganin wani a kusa da shi mussanman jininsa.
'Mahi halinsa sai shi, shi yasa Allah ya had'ashi da mai halinsa ya ke k'orafin banza.'
"Saifullah kiramana likitan dan ban son ya san munzo tafiya da shi ne, na fison ya ganmu kwatsam." Maganar Baba k'arami ya katse masa zancen zucci.