Dr. Laylah
05.
"Laylah na rantse haduwarmu ba zaiyi miki kyau ba, saina hukuntaki ta hanya mafi ciwo." Ya furta cikin furzar da ruwan bakinsa cike da huci.
Fidda kayan jikinsa ya yi ya zuba a washing machine ya gabatar da wanka cikin ruwan sanyin bayan ya kammala ya dauro alwallah ya fito yana rawar sanyi ya zube saman Italian bed, dik yarda yaso ya gabatar da sallalolin da ake binsa kasawa ya yi bashi da zab'i illa samawa kansa mafita dan samin saukin sanyin da ke nukurkusan gabbansa. Da kyar ya iya janyo duvet ya rufa ruf har saman kansa tare da cure jikinsa wuri d'aya, bargon sai motsawa ya ke yi da k'arfi sautin haduwar hakorar kuwa na fita kas!-kas!!-kas!!!. Tun yana tuna me ya ke ciki har ya fice hayyacinsa zuwa wani lokacin bargon ya daina motsawa tare da tsayuwar sautin fitar numfashi sa, d'akin ya yi tsit tamkar babu mai rai a cikinsa.
****
Cikin amo mai nuni da b'acin rai tsan-tsa Alhaji Abdul Waheed ya ce "Hafsat yau naga danki na bi bayarsa amma ya b'acemin to zanyi miki magana na k'arshe akan lamarin nan, wallahi kinji na rantse idan Muhammad bai nemomin inda d'iyarta ta ke ba ranki sai yafi nawa b'aci, dafatan kin fahimta?"Tajima tana kallonsa kafin ta bude baki cikin kwantar da murya ta ce "Dadyn Moh'd shin inyi maka wata tambaya mana?"
"Ina jinki." Ya amsa a fad'a ce
"Shin waye ta haifi Laylah a cikinta?"
Wani kallo ya watso mata ta gyad'a masa kai cikin danne b'acin ranta ta cigaba da cewa "Idan har ka amince ni ne mahaifiyarta ya kama ta ka dakata da yimin irin wad'an nan bayanan masu kama da rikonta ka ba ni, ba ni ce nasan zafin nak'udarta ba."
"Dakata Hafsat! dama tuni na gama fahimtarki sabida kina takamar ke kika haifeta yasa kike wulakantamin ita yarda kikaga dama to ki karkade kunnuwarki da kyau ki saurareni, dan kin haifata ba halittarta kikayi ba dan haka idan kina da hannu a cikin b'atan dabon da ta yi wallahi ki gaggauta nemomin d'iyata amma idan kika bari na gano ta da kai ta sanarmin da hannunki ciki wallahi zan dau mataki a kanki domin bazan duba matsayinki gareni ba balle ya zamo fakarki."
Itama cikin zafi ta amsa "Allah ya baka sa'a, kayi dik abinda kaga dama amma ina son ka sani idan ka wulakantawa Laylah mahaifiya tabbas bazata yafe maka ba wannan a rubuce ya ke, wallahi nafika son Laylah haka nafika sanin wacece ita. Dadyn Moh'd ka yarda Laylah ta bar gida ne bisa ra'ayin kanta babu hannun kowa cikin lamarin. Dan Allah ka fahimci zancen nan, yarona bazai taba zamowa silar barin farin cikin kowa gida nan ba kuma inaji a jikina tana wuri na gari bada jimawa ba zata dawo garemu, dan Allah mijina ka sassauta zuciyarka ka mik'awa Allah lamarin sai kaga nasara ya samu amma ba yawan tasar da hankalin muta ne ba." Ta k'arasa cikin kwantar da harshe.
Dafe kansa ya yi yana sauraren dikkan bayanenta na san yasu a mizanin hankali.
"Kai yanzu ko ganin yarda Yaya Alhaji da Hajiya suka daga hankalinsu bai isa yasa kayi kawaici ba? Dan Allah Dadyn Moh'd ka sakko mu koma zaman lafiya mai cike da nishad'i, katuna fa moh'd din ka ne mai son ka sama da kowa mai gudun b'acin ranka, dan girman Allah ka kauda komi walwalarka ya dawo hakan zai taimaka hankula su kwanta mu duk'a ga addu'ar bayyanarta."
"Hafsat ba zan iya walwala ba idan har banga haskenmu ba, kiyi hak'uri kawai."
"Laylah zata dawo insha Allah mijina domin tasan inda kanta keyi mata ciwo, ina da tabbacin wata k'ila baud'add'en halinta ne ya motsa ta gujemu amma ba da jimawa ba zata dawo."
"Nima ina tunamin hakan amma ita kawai na ke son gani a idanuna Momyn Sawwama ki fahimceni mana."
"Na fahimce ka mijina amma nima ina son ka fahimceni."
"Ba mai yiwuwa ba ne fahimtarki idan har banga Laylah a gabana ba. Baki d'aya na rasa gane amfanin masu bincikenan kullum babu cigaba Moh'd kadai suka gano maboyarsa amma labarin d'iyata shiru, tun ranar ba wanda ya ga koda mai maka da motar ta balle ita, ya rabbi ka kawomin mafita."