Dr. Laylah
03
"Affuwan yallab'ai bayarda zanyi ne domin ban iya k'arya ba."
Ma'aikacin ya furta bakinsa na rawa.
"Tafi amma ka shirya amsar hukunci dan alamu ya nuna za'a iya hada baki da kai ayi kisan kai."
"A'a yallab'ai wallahi nasan shi dan uwanka ne kuma kun saba zuwa tare wannan dalili yasa na sanar masa da gaskiyan inda kake amma wannan shi ne na farko kuma na k'arshe sabida kiyayewar tsaro."
Harara ya watsa masa ya koma ciki Saifullah ya d'oki kafadar ma'aikacin tare da furta masa wata kalma cikin rad'a, ya gyad'a kai tare da barin wurin da sauri, murmushi Saifullah ya sa ki ya shige ciki tare da kullo k'ofar.
"Brother me ka ke shirin yi? Shin wai ko kana da sa hannu a barinta gida ne?"
"Saifullah bansan komi a kai ba, ka yarda da ni."
"Idan ka tabbatar da hakan gaskiya ne yanzu ka taho muje ka kare kanka domin kowa na family ya dora zargin alhakin tafiyarta akan ka."
"Ya salam ni Mahi na ga ta kaina kam."
"Brother wannan zancen ba ita ce mafita ba domin ka gama b'atawa kowa rai, Umma ta yi fushi da kai ainun haka Baba Alhaji ya fusata da lamarin kai hatta momy da ta ke bayanka na hango b'acin rai a idanun ta ga Hajiya ta hana kowa sukuni da rigiman sai an nemo mata jikanta, Ammi da Ummi tare da su Abba dik suna cikin damuwa, kai kowa hankalinsa a tashe ya ke barinma da ake ta kiran layinta bai tafiya, wannan dalilin ya sa na zare jiki na fice a wurin taron batare da sanin kowa ba nazo tafiya da kai."
"Waya sanar maka da ina nan?" Ya cillo masa tambayar idanunsa jajur.
"Kunna wayarka ya bani damar gano mafakarka."
"Saifullah ba zan bika ba domin na yiwa kaina alk'awarin nemo musu diyarsu ko aina ta ke dan na tabbata bata bar Nigeria ba."
"Kana da tabbacin tana k'asar nan?"
" Eh."
" Ok sai ince Allah ya baka nasarar gano inda ta ke, ni zan koma amma ka tabbatar da ka rage damuwa kuma ka kunna wayoyinka ka kira su Baba Alhaji domin wanke kanka."
"Insha Allah zan kira."
"Ok."
"Nagode da kulawa brother."
"Ka da ka damu hakkin na ne kula da zumunci."
Murmushi suka sakarwa juna sannan suka rungume juna cikin tarin k'auna mara misaltuwa.
Bayan fitar Saifullah, Mahi ya zauna shiru zuwa can ya tashi ya fice ya yi sallama da hotel din ya shiga motarsa ya dauki hanayar Zaria sai da ya fice garin Kano sannan ya sa ki ajiyar zuciya ya doki steering cikin furta "Saifullah kenan sarkin wayau to na hasko dibarar ka, kafin su Baba Alhaji su ritsani na san inda dare ya yi min."
Ya shafi beard nasa ya kuma kaiwa steering duka tare da jan tsaki mai k'arfi. "Damuwa dai damuwa dik akan wacce bata isa ba." Ya furta hakan cike da takaici wasu kwalla suka taro cikin kwqrmin idanunsa, ya shafosu zuciyarsa na kuma d'aukan zafi, cikin cije lips ya girgiza kai tare da k'ara speed.
***
Saifullah ban sanka da karya ba amma sai gashi yau ka aika tamin, me ya sa?""Baba Alhaji wallahi yanzu muka rabu da shi a d'akin nan kuma bai nunamin zai tafi ko ina ba, shi yasa na zare key din d'akin batare da ya sani ba, wallahi Baba kayarda da ni ba zan yi ma karya ba."
" Shi kenan na ji amma na dora maka alhakin kawomin d'an uwanka gabana daga yau zuwa gobe domin rigimar Abdul waheed ya soma isa ta wallahi daren jiya ban iya barci ba musanman ganin yarda Hajiya ke kuka da hawaye dik sabida abinda yaron nan ya aikata."