Dr. Laylah.
10.
Sunyi tafi kad'an ta ce su zauna inda zasu rik'a hango jama'ar gari ba musu suka zauna a k'asar wata bishiyar mangoro. Gefe daya ta koma ta yi shiru ya yin da su kuwa yaran suka soma sabgarsu na wasanni yarda dai mafi akasarin yaran karkara keyi dik in sun had'u.
Photonsa ta tsirawa ido zuwa can ta ja tsaki ta ajiye wayar tana mai korar tunninsa wanda a tsakanin ya zame mata shan maganani domin dik yarda taso kaucewa tunaninsa hakan bai samuwa shi yasa yanzu ta maida hankali ga yawan karatun Qur'ani domin samun natsuwa wanda a kullum ta zauna yi sai Mama Zainabu ta sanyata a gaba ta yi ta kallo lamarin da ke bawa Laylah dariya sosai sabida a fili ta ke hango mamaki tare da tulin tambayoyi a fuskan Maman amma ta kasa furta su. Motsa zara-zaran yatsunta ta yi suka bada sauti, cikin son kauda tunanin da k'arfi da yaji ta kuma jan tsaki mai sauti wanda saida yaran suka kalleta ta d'auke kai gefe gudun ka da Maryama ta isheta da tambayar abinda ke damunta.
"Yaya Deen." Ta ambata fuska d'aure sai kuma ta mik'e da hanzari ta dubi yaran ta ce "Ku zo muje kogin Balanmado yau dai in ganta ido da ido."
"Yaya Laylatu Mama ta gargademu cewa ka da mu kaiki sabida wurin na da hatsari mu kammu yan gari ba'a bari muna zuwa sai a b'oye."
Gaba ta yi tana cewa "Ni ma a b'oye zaku kaini sannan ba jimawa zamuyi ba ina dai son ganinta ne ko dan tarihi."
Ba da son ran Maryama ba suka biyo bayanta. Tafiyar mintoci ya kawo su bakin kogin mai abin al'ajabi domin gata dai bata kai Mashaya (kogin da sukaje kwanaki) tsawo ba amma tafita fad'i haka ruwan kogin mashaya yafi nata kyau domin ita wannan yana da duhu sabanin na wancan mai haske dan ana hango yashin k'asar kogin wanda ke dauke da kananun tsirrai wannan kam ba'a hango abinda ke k'asanta.
Tsoro kogi ta bawa Laylah wanda faruwar hakan bak'on lamari ne a gareta domin sam bata san tsoron ba balle nuna gazawa cikin dik kan lamuran ta.
"Kai ku taho mu bar wurin nan gaskiya ne bai da kyau jiri na ke gani." Ta ambata cikin fitowar tsoro a idanunta.
Dariya suka kyalkyale mata da shi jin abinda ta ce.
"A she Yaya laylatu matsoraciya ce." Maryama ta ambata cikin dariya.
Kallonta kawai ta yi ta juya dan komawa gida suka biyota.
"Yaya laylatu bakiga wancan gadar ba da kuma bishiyoyin da suka rufe da ita masu ban sha'awa ga wurin na d'auke da sanyi tamkar ansanya masa abin sanyaya d'aki irin na gidajen birni." Cikin yaran mai suna Salimatu ke furtawa tare da nuna wurin da yatsa.
Tsigar jikin Laylah ne ya tashi wani sabon tsoro ya kuma shiganta amma sai ta samu kanta da son ganin gadar idan ma ta samu dama ta hau samanta ta d'auki photo.
"Ku muje in gani dan nima na bada labarin na tab'a hawa saman Gadar Balanmado." Ta furta cikin murmushi.
Suka tafi da sauri wurin Gadar, ta biyo bayansu cikin tafiyarta na ko da yaushe, like a Queen.
Abinda ya kuma bata mamaki ganin yarda itaciya ce babba shimfide wanda ta ratsa ruwan biyu ta tsaye, ta mik'e har zuwa bakin hanyar fita a matsayin gadar, gata silili tamkar an shafa mata mai. Ji ta yi tana son hawa gadar dik da ruwan da ta hango na bin kasarta a guje cikin mudewar igiya tare da fitar kumfa, lumshe ido ta yi sadda ta isa wurin itacen sakamakon jin iska mai dadi na busawa, ta waiyaya gefen Gadar tana k'arewa wurin kallo wanda manyan bishiyoyi suka cewayeta masu yalwan ganye sannan ta gefen hagu lungune ya nausa ciki ta inda fili ne babba tare da bishiyoyi masu yawa sun kewaye wurin, ga ruwa nan ta tsakiyar filin na fitowa,ya yin da gefen dama kuwa ya ke da karancin bishiyoyi domin ta nan ruwan ke bi a guje zuwa babban kogin da masinta ke yin su. Ajiyar zuciya Laylah ta sauke cike da jin wurin ya burgeta dik da har zuwa lokacin tsoro bai bar ruhinta ba. Bisa mamaki sai ta ji ta sami kanta da soma karanta Ayatulkursiyyu a zucci, tana isa baki gadar ta soma hawa Gadar jikinta na rawa yaran na ihu tare da yi mata tafi, ta kai tsakiyar Gadar wani iska ya busa jiri ya kwashe ta tamkar wacce aka tunkud'a haka lamarin ya faru ta tafi cikin ruwar direct amma kafin ta fad'a Allah ya bata iko ta rik'e Gadar da ta ratsa ruwan wayarta da ke hannunta ya yi tsalle ya fad'a cikin ruwa ya yin da kafafunta su ke tab'o ruwan sanyin ruwan na ratsata har cikin kashinta, jin tana zamewa da alamu ruwan zaka k'arasa fad'awa sai ta kuma rik'e Gadar da hannu biyu tana jin kashin hannunta ya yi k'ara ta runtse ido tare da furta "Help!."