page 11

204 13 0
                                    

Dr. Laylah.

11.

Murmushi ne ya kubce mata saka makon ganin hannun kunbura ya yi shima ba sosai ba. 'Amma dan iya tada hankali mama na kiran zan koma mai hannu d'aya.' Ta ambata cikin ranta tana saukewa Maman hararan gefen ido.

"Laylah mun gode Allah da had'arin ya tsaya a hannun hagu kai amma abu baiyi dad'i ba, ko da ya ke maganin marajin magana kenan idan ba neman magana ta ya za'ayi ke da baki tab'a zuwa wuri ba kice za ki hau saman itaciya mai d'auke da kwankwamai, ni dai Allah ya sa basu shafeki ba dama ance junnu sunfi lak'ewa kyawawa kuma fararen mata."

Idanu waje Laylah ke kallon Mama cike da tsoron kalamanta sannan rawar sanyin da ta keyi ta nemesa ta rasa.

'Na shiga uku! dama aljannu na zo daukowa kaina a garin nan?'

Dafa kafadarta da Mama ta yi ya katse mata zancen zucci da ta ke yi, ta zuba mata ido cikin bayyanar rauni domin kalman aljannu ya daki ruhinta.

"Kogin Balanmado ba wurin zuwar mata ba ne ko maza sai jarumai sabida wuri ne mai dauke da rundunar almatsutsai kala-kala,wasu masu kyan gani wasu kuwa kallo d'aya mutum bai iya bari ya yi musu sabida tsabar muninsu da ban tsoro."

Dariya Maryama ta kyalkyale da shi tana nuno Mama da yatsa cikin cewa "Ke Mama wa ya kaiki wurin da har kika gano rundunarsu masu kyau da munana?"

Shiru Mama ta yi tana mazurai ganin Maryama ta bata mata plan na son tsorata Laylah dan ka da ta sa ke marmarin zuwa wurin ko a mafarki.

Murmushi Laylah ta yi tare da komawa ta kwanta ta lumshe ido, jama'ar da ke waje suka sanya dariya ganin yarda Mama Zainabu ta yi jagwale tana bin Laylah da ido.

D'aya bayan d'aya mutanen suka rik'a shigo suna yiwa Laylah sannu tana amsawa idanunta kulle, domin sun san halin sababin Mama suna shigo dik kansu yanzu zata korasu.

Habu ya dawo Mama ta hanata shan maganin sai da ta had'a mata tea tasha rabin kofi ta mik'awa Maryama ragowar. Tana gama shan maganin ta kwanta cikin cije lips, dik yarda Mama ta so hanata kwanciya a lokacin sabida ana daf da kiran sallar magrib amma ta k'i ji saka makon wani barci mai dad'i da ke kawo mata ziyara, ba jimawa kuwa ya d'auke ta, ruwan wanka dai anmanta da shafinsa.

Sai k'arfe goma na dare ta farka ta yi arba da Mama zaune nayi mata fifita, Maryama kwance a gefenta.

"Nagode Mama Allah ya biyaki da alkhairi, a kullum idan tunanin gida ya bijiromin dana tuna ina tare da ke sai naji tamkar ina gaban Hajiya ce.."

"Laylatu ba za ki gane k'aunar da na ke yiwa mahaifiyarki ba wanda shi ne ya shafeki dan a kullum na bude ido na ganki zaune d'akina garin da ba wutan nepa ba ruwan famfo balle na'urar sanyaya d'aki amma ki ka iya jure zama a haka alhalin kin baro muhallinki mai d'auke da komi na jin dadin rayuwa wallahi sai naji hawaye na zubomin na jin dadin wannan karamci da ku ke yimin dik sanadin tarbiyyan Yaya Abba dattijon kirki."

Hannunta mai ciwon ta motsa cikin murmushi ta ce "Wannan bakomi ba ne Mama domin nima zuwana gareki yanzu ina kan yin wani karatu wanda bantab'a tunanin da irin rayuwar a duniya ba."

"Wani karatu kuma ki ke yi a garinmu Laylatu?

Sa ke lafewa ta yi jikin Mama sannan ta amsa "Karatun sanin mabam-banta rayuwa na al'umma da yarda suke tsara cigabansu mai ban mamaki."

"Kamar su me fa?"

"Kinga Mama ban tab'a sanin mata na zuwa gona taya mazajensu noma ba sai zuwa na garin nan naga yarda mata ke tafiya gona haka ban yi tunanin a kwai masu imani da taimako tsakanin da Allah ba tare da sun nemi abiyasu ba sai anan garin dan abinda Musa ya yimin ya tsayamin arai, ban tab'a ganin yaran mata na gudanar da rayuwarsu cike da ilimi na bin dokar Allah ba kamar yarda naga su Maryama na gudanarwa. A kullum hangena 'yan karkara basu san komi na cigaban rayuwa da shari'a ba amma zamana na kwanaki a garinku na k'aryata wad'an da ke yawan aibata karkara domin naga zahirin inda ake aiki da umurnin Allah sannan da wayewa daidai misali ba wancan ta zamani ba wanda k'arara halaka ce."

Doctor Laylah.Unde poveștirile trăiesc. Descoperă acum