Dr. Laylah.
08.
K'arfe takwas da minti biyu Ishaq ya kira sallar isha'i ba jimawa mutane suka cika masallacin Baba Alhaji ya ja su limanci. Bayan idarwa sukayi ta bawa juna hannu ta hanyar yada sallama tsakanin su dan koyi da ma'aiki S.A.W, Mahi ya sunkuya gaban Baba Alhaji ya gaisheshi ya amsa tamkar babu komi, jiki a sanyaye ya somabin iyayen nasa yana gaisarwa tamkar yarda sauran yan uwansa keyi. Zuwa dan lokaci kowa ya fice masallacin ya rage saura shi da amininsa.
Saifullah ya dubi Mahi kafin ya yi magana muryan Deen ya ratsa kunnuwansu "Malamai ku sami fitowa daga waje damin masjid ba wurin tattauna bayanen juna bane dan anyisa ne sabida bautar Allah da neman gafarsa tare neman biyan buk'ata na gari ba wai shiri...
"Twins wai me ye damuwarka da lamarinmu?" Saifullah ya katse shi a fusa ce.
"Babu amma dai ina son ganinku a waje sabida zan kammala aikina na kulle masjid."
Tsaki Mahi ya ja ya fice Saifullah ya dubi Deen ya ce "Please brother kabaryin haka dan abinda ya faru ya riga da ya faru dan haka ka kama kanka tun fushin Mahi bai sauka akan ka ba."
"Kai ne fushinsa ke tsorata ka amma ni daukansa na ke holok'o hadarin kaka wanda dik had'uwar sa bai tab'a zubda ruwa."
"Allah ya yaye muku wannan mugun halin."
"Amin, dan koran wanda bai kai ba kawai."
Kamar Saifullah zai sa ke magana sai kuma ya wuce yana gyad'a kai, Deen ya rakashi da mugun kallo.
"Brother idan kana son ganin Deen da lafiyar hakora to ka sanar masa ya daina shiga sabgata."
"Kai ni ba ruwana da shirmenku abinda zan iya ce muku shi ne ku nutsu ku san inda kanku keyi muku ciwo wannan fad'ar sama da shekaru ashirin kuna yinsa amma har yanzu bata sanja zani ba saima kara girmama ta keyi dik akan abu d'aya, anya ba zan kai kararku gaban Baba Alhaji ba? Domin nagaji da ganin wannan munafuncin naku a gaban kowa ku nuna bakomi amma da zarar manya sun kauce ku koma tamkar mayak'a. Haba dan Allah wallahi ku gyara halinku domin wannan lamarin na kusantaku da zuwa gidan wuta ne."
Shiru Mahi ya yi yana saurarensa ya yin da Deena ya iso wurin ya doki kafadar Saifullah cikin cewa "Ya magajin yallab'ai magajin gari takawarka lafiya, gaba salamun baya salamun amma a kula domin damisa k'i sabo yana ankare da kai kuma cike ya ke da burin yi maka kaca-caka idan aka kuma nuna masa fin k'arfi akan abinda ya ke mallakinsa ne tun a can baya."
Cikim mugun fushi Mahi ya kawo wa bakin Deen naushi, Saifullah ya tare da tafin hannunsa yana girgiza masa kai.
"Barshi twins ya gwada dukana wallahi ya daukowa kansa abinda zai addabi rayuwarsa."
"Deen ina ga kana maraba da zama mai wawulo dan wallahi kaji na rantse yau shi ne rana na k'arshe da zaka tsaya a gabana kana fad'amin zancen banza batare dana zubda maka da hakora ba."
"Wow a she ka warke haka ban sani ba, to sarkin dambe kaga tafiyata amma ka sani ba wai tsoronka na ji ba ina dai son na gama da mahaifana lafiya ne musanman Ammi wacce addu'ar ta ke tare da ni domin nayi hannun riga da bin hanyar sanyata fushi."
Kallonsa Mahi ya yi cikin jan ido numfashinsa yana fita da sauri da sauri, dafa chest nasa Saifullah ya yi yana ambatar kalman innalillahi wa inna ilaihin raji'un, a ta ke Mahi yasoma maimaitawa ya yin da Deen ya kyalkyale da dariya ya wuce zuwa wurin motar sa.
"Ya tabbata Umma na fushi da ni Saifullah."
"Zata huce idan mun isa gareta dan haka ka kwantar da hankalinka kasan kana da gazawar lafiyar zuciya sannan ina rokonka da ka koma ainihin Mahin nan na shekarun baya wanda kalaman Deen baita ba fusata shi ko da ya fusata shi bai tab'a bari ya baiyana saman fuskansa balle ya fito cikin furucinsa."