Dr. Laylah.
BY SAFIYYA (Mrs J Moon).
02.
"Yi barcinki Hasken alkhairi, ke kuma fice kibata wuri ta huta, kina ta dariya kamar sauniya."
Da sauri maryama ta fice tana cigaba da dariyar, ta samu kawayenta sun cika k'ofar Mama Zainabu, suna ganinta suka tareta, ta dubesu kamar zatayi magana sai kuma ta yi gaba suka rufa mata baya.
Lumshe ido Laylah ta yi tana sauke numfashi amma sam barcin ya ki zuwa. Hannu ta dora saman forehead nata ta yi rigingine tana kallon rufin d'akin, mama da ke kallonta ta tab'e baki ta mike ta dauko wankakken bargo ta rufa mata tana cewa "Daure ki sami barci ko kya daina karanta wasikar jaki da ba zai kareki da komi ba sai janyo ciwon kai."
Gyad'a kai ta yi batare da ta bude idanunta da suke lumshe ba.
"Na tafi in tama uwar Maryama sussukan gyeron yin fura da tuwon gobe." Mama ta furta batare da ta jira amswar Laylah ba ta fice. Ta shi zaune ta yi jin ficewarta, ta sakko ta bude hand bag d'inta ta b'alli tablet ta sha sannan ta koma ta kwanta ba jimawa kuwa barci ya d'auke ta.
*** *** ***
Birnin Kano.Zaune ya ke cikin mota a bakin gate din wani babban estate ya kasa shiga ciki domin yasan b'acin rai zaici karo da shi wanda zai kuma dagula masa lissafi. Tun misalin k'arfe bakwai na safe ya ke gararin nemanta amma har zuwa yanzu da duhun magriba ya kawo jiki bai yi nasarar gano inda ta ke ba, ya gama zagaye clubs da hotels dik da ya san tana zuwa kai harma da karin wasu amma baiyi nasarar ganin ko mai kama da ita ba, kawayenta da ya sani ya gama zagaye gidajensu zancen kenan d'aya shi ne tun bayan bikinta rabonsu da ita lamarin da ya kuma rikita shi kenan, ya fada cikin tunani mai zurfi tare da jin fargaba mara misali, ya dafe goshinsa ya yi shiru tare da tsirawa teddy mai siffarn shanuwa da ke ajiye a gaban motan ido tamkar mai son yin drowning nasa amma sam Na teddyndin yake kallo ba, tuni ruhinsa ya nutsuna cikin tunani inda zai ganota.
Tun isowarsa akan idonunsa, ganin baida niyyar fitowa ta ke farin ciki ya mamaye ruhinsa, dan idan da abinda Deen ya tsana shi ne ganinsa cikin rashin wal-wala. 'Uhm labarin gizo dai bai wuce na k'oki.' Ya ambata cikin ransa tare da tunkaror motar cike da neman magana.
Saifullah da ke hango inda ya nufa ya girgiza kai domin yasan yanzu za'ajiyosu. "Lamari tun yarinta har zuwa girma sam bai sanja zani ba, kai Allah ya kyauta dai." Ya ambaci hakan yana mai latsa wayarsa.
Kwankwasa motar Deen ya yi cikin dai-daita fuskansa wanda hakan ya yi nasarar dawo da Mahi duniyar tunanin da ya fad'a, ya ja ajiyar zuciya ya mik'e hannu ya sauke glass yana mai kallonsa tamkar zai fashe da kuka.
Dariyar da ya kyalkyale da shi ya tona masa wanda ke gabansa Saifuddeen ne ba mutuminsa Saifullah ba.
A fusace ya fito ya yi banging murfin motar ya nufi gate tamkar zai tashi sama.
Dariya Saifuddeen ya kuma kwashewa da shi har da buga kafa a k'asa yana kaiwa motar duka tare da rik'e ciki dik a lokaci d'aya.
A mugun fusace Mahi ya dawo ya cukumeshi ya hada da jikin mota ya jijjiga amma still bai daina dariyar ba.
"Zan zubarma da hakora Deen! Wallahi zan sanja maka halitta yanzu dan kafi kowa sanin ban daukan rainin hankali."
"Am sorry yallab'ai, sa ke ni in tafi samawa matana abinda babynmu ke muradi." Ya furta cikin d'auke dariyar.
Hanka dashi gefe ya yi ya koma cikin motar ya fizga a guje ya bar wurin. Sosa neck nasa Saifuddeen ya keyi cikin hade rai tamkar ba shi ne yanzu ya gama kwasan dariya ba.
"Tafiyarta shi ne kwanciyar hankali, Allah ya sa ta shiga duniya kenan kowa ya huta domin faruwar hakan shi ne raba gardama, dan ina nan akan bakana, banga kuma wanda ya isa ya dakatar dani ba." Ya furta cikin voice mai kaushi, fuskan nan kamar hadari sabida bayyanar b'acin rai a kansa.