Dr. Laylah.
07
'Kina da babban aiki Ramla.' Wani shashi na zuciyarta ya bata amsa.
Tashi ta yi cikin diraba ta matsa ta jingina da jikin gadon yarda zataji dadin zama.
"Bayan dik abin da ya faru sai da Yaya Mahi ya kuma dagula komi, shin wai dama yasan yana... Bata k'arasa ba ta yi shiru cikin tunani tare da tsirawa agogo da mab'allen idanu.
" Shakka babu cikin Yaya Mahi da Yaya Deen wani yasan dalilin tafiyar 'yar uwata Laylah. To amma me sukayi mata? Kar dai a ce dik sun kasan ce da... Nan ma bata k'arasa ba ta girgiza kai " No! hakan bazai faru ba." Ta furta cikin furzar da iska tare da share gumin da ke tsats-tsafo mata a goshinta tamkar wacce ta hadiyi kunama.
'A da ina ganin tafiyata shi ne alkhairi amma yanzu na karyata. Zanyi ne ba dan wani manufa na daban ba.' Kalaman Deen na dazun suka dawo mata a brain ta kuma furzar da iska tare da shafo saitin zuciyarta dake harbawa da sauri da sauri.
Motsin tab'a k'ofa taji ta yi hanzarin zuba tarkacen a pose d'inta tare da daidaita fuskanta. Momy ce ta shigo ta zauna gefenta tana mai nazarin yanayinta.
" Me ke damunki Ramlah?"
" Baya da marata Momy suna matsamin da ciwo."
"Innalillahi! Tun tsawon wani lokaci suka soma?"
"Cikin kwanakin nan ne."
"Dole ki sami hutu dan haka maganar zuwa aiki babu sai kin haihu."
"Momy jama'a suna buk'ata na domin kula da lafiyarsu."
"Mu kuma muna buk'atar lafiyarki dana Baby dan haka bansan gardama dole ki sami hutu kuma zai fara daga yau anjima zansa Mamie ta dauko miki abinda kike buk'ata."
"Momy Allah zan iya aiki rashina a wurin zai iya kawo nakasu tunda kinga Yaya Deen a sati sau biyu ke shigowa ga shi Laylah ta dakatar da Dr. Bilkisu da Dr. Lere, ni ce kad'ai akan komi yanzu."
" Yau she hakan ya faru ban da labari?"
"Anjima da dakatar da Dr. Lere, Dr. Bilkisu ce bai wuce wata biyu ba."
"To akan me hakan ya faru?"
"Dr. Bilkisu dai sabida kanwarta Fatima, ta yi k'ok'arin yi mata rashin kunya a cikin jama'a shi ne ta hukunta kuma hukuncin ya shafi yayarta shi kuwa Dr. Lere ba zance ga abinda ya hadasu ba." Ta kai k'arshen maganar cikin nuna alamun b'oye dalilin.
"Ok in haka ne yazama dole Dr. Bilkisu da dawo bakin aikinta, anjima zanje gidan nasu na sameta shi kuma Dr. Lere idan na samu natsuwa zan bibiye abida ya hadasu sannan dole Saifuddeen ya koma aiki regular, Ishaq ma zai dawo aiki da ku dan ba ruwana da shiriritarsu shi da Saifuddeen abinda na sani ne dole su had'u dan kawowa asibitin ci gaba."
"Hakan ya yi Momy, ba dan ita ma Rahma taki karatun medicine ba da yanzu da ita ake taimakon al'umma."
"Ai ko yanzu tana bakin k'ok'arin ta ki duba irin cigaban da ta ke kawowa a L.L Company, ai ko namiji ke wurin iyakarsa kenan."
"Gaskiya tana k'ok'ari amma bisa jajircewar Yaya Mahi ne har ta zamo hakan." Ta ambata cikin murmushi.
"Da wannan kam kuma hakan ne ma na ke zaton ya burge Laylah har take son samun ilimi akan kasuwanci itama a dama da ita."
"Uhm Momy har yanzu baki gama sanin Laylah ba, tana son samun ilimin kasuwanci ne dan amsar ragamar companin a hannun Yaya Mahi wannan dalilin yasa kikaga Dady ya soma gina new company dan raba gardama dan ya san in har burinta ya cika da rigima."
"Ya Salam amma Laylah anji ja'irar yarinya."
Dariya Ramlah ta sanya ganin yarda momy ta furta maganar cikin zare idanu.