Page 06.

255 16 2
                                    

*Dr. Laylah.*

06.

Cike da kulawa ta sunkuya gabansa ya kalleta kad'an ya maida kansa yarda ya ke wato kallon saman ceiling.

"Yaya Deen kaima Sister ko?" Ta ambata cikin amo mai sanyi wanda ya nuna tamkar ba ita ta furta maganar ba.

'Sosai komi nata ke yanayi da Laylah.' Ya ambata cikin ransa tare da sauke mata kallon gefen ido cikin murmushi ya furta "No." A takaice.

Kamo hannunsa ta yi cikin cewa "Uhm Yaya kenan wallahi ba zanyi kaffara ba na tabbata kaima ita ce a ranka tamkar yarda ta ke ran kowa, shin wai ba wanda zai samo mafita a cikinku ne?"

"Mafita naga mai son zuciyar nan yayanki."

"Yaya Mahi bai san inda ta ke ba, idan ko da ya sani shakka babu da ba'akawo yanzu ba batare da ya bayyata ba."

"Ki tafi majinyata na bukatarki tunda ta bar miki aikinta sai ki maida hankali kuma ki kula da kanki dan kinsan bake kadai ba ce." Ya sauya zancen.

Tsira masa ido ta yi cikin nazari kamar zatayi magana sai kuma ta mik'e ta nufi hanyar barin parlorn. Bayanta yabi da kallo abin mamaki lafiyar Laylah sak mai cike da takama, lumshe ido ya yi cikin korar tunanin dan ya san gizo yanayin nata ke yi masa kawai sannan hakan bai kamace shi ba.

"Ramla." Ya kira sunarta a hankali, ta juyo batare da ta amsa ba.

"Ki cire damuwa, ba da jimawa ba zan nemota dik ada ina ganin tafiyarta alkhairi ne amma yanzu na karyata hakan musanman yau da na shiga wurin Hajiya naga yarda ta koma abin ya tab'amin zuciya, banyi zaton haka ta ke son jikarta ba, kukan da ta ke min akan in nemo inda Laylah ta shiga ya bani kwarin guiwan inshiga lamarin amma ki sani ba zanyi dan wata alak'a na da ban ba, trust me please."

"Alhamdulillah, ka da kasami damuwa Ramlah ta yarda da kai, Allah yasa kayi nasarar gano mana inda farin cikin Magajin gari's family ta b'oye."

"Amin." Ya amsa cikin sauke mata murmushi wanda a kwanaki biyu nan bata sami ganinsa saman fuskansa ba.

"Idan na tashi aiki zan shiga wurin Momy tana nema na."

" Ok sai kin dawo nima yau zan tafi Zaria dan ina zargin tana can, wata kila ita tanemi da ka da su sanar tana tare da su."

"Anya, gaskiya inda tana can kome ta ce sai Goggo ta kira ta sanar, kasan bata daukan shiririta."

"Haka ne amma zan dai je ingani."

" Allah ya tsare hanya ya dawo da kai lafiya."

" Amin."

Har ta shiga mota ta dawo daidai lokacin Deen zai fito ya dubeta kafin ya furta kalma ta yi hanzarin cewa "Yawwa dama zan tambayeka yarda ka baro yaya Mahi ne jiya dafatan ka bashi abinci?"

" Kafin in iso ya bar asibitin so ban san yarda ya kwana ba." Ya amsa cikin halin ko in kula.

Gyad'a kai ta yi tare da juyawa ta koma inda motarta ta ke ta fice daga gidan, Deen ya rakata da ido ransa a dagule.

" Ina ki ke Laylah!?" Ya furta da k'arfi cikin kaiwa iska naushi. Ya koma cikin falon ya zauna dafe da kansa.

"Amma Laylah kin san kan tsiya, a lokaci daya ran kowa ya b'aci sabida rashin ki, hak'ik'a kinci sunarki haske mai cike da alkhairi." Ya kuma furtawa tare da jan hancinsa, sai kuma ya mike da sauri ya fice zuwa parking lot yana kallon agogon da ke daure a tsintsiyar hannunsa na hagu.

*** ***
Hasken da ya shigo windo shi ne ya dameshi ya nemi tashi zaune yaji ya kasa, a hankali ya soma bude idanunsa ya sauke kan agogo ya mike a hanzarce ya sauko daga gadon, jin iska na shigarsa yasa ya shafo waist masa sai ya koma da sauri ya shige bargo yana jan salati dalilin jinsa tsirara. Abinda ya faru da shi yammacin jiya yasoma dawo masa salati ya rafka tare da fallawa fuskansa mari, ya sa ki kara sabida zafi da ya ratsashi. Taba k'ofar da akayi ya ja hankalinsa ya zubawa k'ofar ido tare da gyara rufar da yayiwa jikinsa.

Doctor Laylah.Donde viven las historias. Descúbrelo ahora