🎈🎀 *ZAMAN KISHI*🎈🎀
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ/HYDAR**BISMILLAH RAHMANIR RAHIM*
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN KAI*
*DUKKAN YABO DA GODIYA SU TABBATA GA ALLAH SUBHANAHU WATA ALA, MAI KOWA ME KOMAI*
'''TSIRA DA AMINCI SU TABBATA GA SHUGABAN MU ANNABI MUHAMMADU (SAW).'''*GARGAD'I!!!!!!*
*BAN YARDA WATA KO WANI YA JUYAMUN LITTAFI TA KO WANNE FANNI BA! DAN KUWA YIN HAKAN BABBAN KUSKURE NE SANNAN BAN YAFE BA MUDDEN AKAYI AMFANI DASHI BADA SANI NA BA!!! SABODA HAKA A KIYAYE.*
_WANNAN LITTAFINA NE NA ZAMA DA KISHIYA NA MAIDA SHI ZAMAN KISHI SABODA INASON KARASA MUKU LABARIN DA FATAN ZAKU AMSHESHI HANNU BIBBIYU_
*PAGE 1~5*
Zaune muke a babban parlourn sabon gidan mu da jiya jiya muka dawo ciki da zama.
Gida ne ma dai-dai ci dan ba wani babba bane can sai dai ba laifi an tsara mana shi yayi kyau.
Ciki da parlour ne nawa da kitchen sai na yara na shima d'aki d'aya a gefe, idan ka fito a nawa babban parlourn Waleed ne a tsakiya sai d'akin sa a ciki, a gefe guda kuma shima d'aki ne ciki da parlour da kitchen kamar dai nawa sai dai babu d'akin yara a nan.
Kuna ganin yanda ya tsara gidan kad'ai zai tabbatar muku gidan Mata biyu ne.
Kallon sa nayi d'auke da murmushi a fuska na nace
"Abban Sadiq wllh har yanzu ji nake kamar a mafarki wai yau mune a cikin irin wannan gidan kuma namu na kanmu."na k'arasa maganar cike a jin dad'i.Murmushi shima yayi yace mun
"Haka Allah yake ikon sa Kubrah duk wani wahalar da mukasha yanzu ya zama tarihi kamar bani bane Walid me sai da ruwa ba, gashi Allah cikin ikon sa ya sakamun albarka a sana'ata da ban raina ba, lokaci d'aya Allah ya azurta ni cikin ni'imomin sa ta arziki."Murmushi na sake masa hawayen farin ciki na sake zubowa a idanu na nace
"Haka ne Abban Sadiq Amman dan Allah akwai abinda nakeson na fad'a maka idan ba matsala."Kallon ta yayi a nutse yace
"Inajin ki Kubrah.""Nidai a gani na tunda dai yanzu alhamdullah kasuwa tana tafiya gashi har Allah ya hure maka da muhalli, dan Allah karka manta da mabuk'ata da almajirai da miskinai, tunda kaima yanzu kana samu alhamdullah sai kana taimakawa kaga Allah zaici gaba da bud'a maka."na k'arasa maganar murmushi dauke a fuskana.
Murmushi jin dad'i yayi dan a kullum sai yayi godiya ga Allah da ya bashi mata kamar Kubrah dan tanada hankali sosai gata da sanin ya kamata.
Hannun na ya ruk'o yace
"Nagode sosai matata da kika bani wannan shawara Kuma insha Allah zanyi amfani dashi kamar yanda kika fad'a mun ngd kwarai 'yar aljannah."Murmushin jin dad'i nayi nace
"Yauwa mijina Nima nagode bari na tashi na shiga kitchen dan had'a maka abincin da kafi so."Shima mik'ewa yayi yace
"Muje na tayaki ko matata."
A tare muka sakarwa juna murmushi sannan muka wuce kitchen.********
"Kasan Allah baka Isa kace zaka mun kishiya ba, ai kafin auren mu sai da kamun alk'awarin bazaka kara aure ba sai yanzu da ka gama lalata ni ka b'ata mun jiki dubi ko Ina jikina sai da ya lalace sannan kace zaka kawo mun wata budurwa gidan Nan wllh baka Isa ba!" Wata Mata me kimanin shekara 25 a duniya take wannan maganar.
Kallon ta Kabir mijin ta yayi yace
"Wai ke Jiddah wannan masifar takice zaisa na fasa abinda nayi niya?
To wllh ki sani babu abinda zai hanani kara aure Kuma Nan da wata d'aya za'ayi biki saboda haka ki fara shirye-shirye, sannan batun jikin ki ya lalace ni na b'ata Miki? Da ni kaina inada hanyar gyara shi ba tare da kin sani ba zan gyara miki shi Jiddah domin kinsan inason ki, wllh kazantar kice ta b'ata miki kije ki gyara abinki idan zaki iya."
YOU ARE READING
ZAMAN KISHI
General Fictionlabarine akan gidaje uku wanda ko wanne cikin su nashi salon kishin, labarine me dauke darusa da dama ki nutsu ki karanta domin limintuwa da wannan k'ayatattacen labarin.