PAGE 71~75

8 2 0
                                    

🎈🎀 *ZAMAN KISHI*🎈🎀

*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ/HYDAR*✍🏻

*PAGE 71~75*

Sake kallon sa Hafsat tayi tace
"Kana nufin mahaifiyar ka Wai."
"Eh itace mana wai me kike nufi ne Hafsat baki gane ta bane?"
Kallon Waleed Mama tayi tace
"Waleed daman wannan ce yarinyar da ka auro? Wannan fitsarriyar ce matar ka! Tab wllh zaman ta bazaiyu a gidan Nan ba kayi maza ka saketa a gabana yanzun nan."ta k'arasa maganar tana nuna Hafsat da dan yatsa.

Bud'e idanu😳 Waleed yayi yace
"Mama me Hafsat tayi Miki da zakice na saketa daga zuwan ki!
Yanzu mama karyan da Kubrah ta had'a kema kin yarda kenan,?
Kubrah fa karya take na tabbata Hafsat bazata tab'a aikata abu makamancin wannan ba Kuma......"katseshi mama tayi da cewa
"Kai Waleed ba Wasa nake maka ba umarni ne nake baka yanzu ka saki yariyar Nan tabar gidan Nan idan Kuma ba haka ba wllh sai nayi fishi da kai!"

Kallon Hafsat Waleed yayi sannan ya juya ya kalli mahaifiyar sa yace
"Kiyi hakuri Mama bazan iya sakin Hafsat ba."

  Ran mama yayi matuk'ar b'aci duk da tasan Waleed ba a cikin hayyacin sa yake ba,Amman ai sakacin sane hakan yasa tace
"To Waleed tunda har ka zabi matar ka akai na mahaifiyar ka! bani ba Kai karka kuskura ka taka kaje inda nake sannan karkaje wajen Kubrah da yaran ta, idan kuwa ka kurkusa ka taka inda muke Allah ya Isa!"tana gama fad'an haka ta juya tayi ficewar ta tana me Jan hannun Sadiq.

  Tab'e baki Waleed yayi ya juya ya kalli su Hafsat wacce sai faman murmushin murna take tace
"Gaskiya sweetheart naji dad'in abinda kayi yau sai yanzu na tabbatar da kana matuk'ar Sona."

  Murmushi yayi mata yace
"Ohh da kin d'auka bana sonki kenan."
Dariya tayi tace
"Ba haka nake nufi ba, yanzu de muje Ka Kai mun kawaye na gidajen su."

  "Ok kizo muje tare daga Nan akwia wani waje da zan kaiki ma."

  Cike da jin dad'i Hafsat ta fita suka tafi sai da suka sauke ko wacce a gida sannan suka wace wani babban shago dan mata siyayya.

 
Sosai ran mahaifiyar Waleed ya b'ace dan har wani rufewa idanun ta suke a haka ta hau Napep ya kaisu gida.

   Tana sauke suka shige gida tare da Sadiq ba tare da tayiwa Malam da yake zaune a k'ofar gida magana ba ta wuce.

  Da kallo ya bita ganin Rai a matuk'ar b'ace ne ya tabbatar mishi da akwai matsala.

  Mik'ewa yayi ya bi bayan ta,
Zaune ya sameta a parlourn ta ta rafka uban tagumi tana hawaye.

  Da sauri Malam ya k'araso wajen ta yana cewa
"Subhallahi Zainabu lafiya kike hawaye ko Humaira ce Allah ya amshi abinsa?"

  Dago idanu tayi tace
"A'a Malam Humaira tana Nan a raye, Waleed ne....."sai Kuma tayi shiru taci gaba da hawayen ta.

  K'arasowa yayi kusa da ita ya kama hannayen ta yace
"Tabbas al'amarin Waleed yana buk'atar bincike Zainabu domin Nima abinda yayi mun a asibiti ya matuk'ar bata mun rai, Amman dan Allah ki daina zubar mishi da hawaye addu'a ya kamata kiyi masa."

  Kallon sa tayi tace
"Malam kasan kuwa me Waleed yayi mun!
A gaban fitsarriyar matar sa da kawayen ta ya tsaya yana fad'a mun magana sannan Ina bashi umarni yana cemun bazaiyi ba............."Nan ta kwashe komai ta fad'a mishi abinda ya faru.

  Numfasawa Malam yayi yace
"Tabbas kamar yanda ta fad'a Miki akwai wani abu da sukayiwa Waleed da har ya koma haka!
Amman ba komai muci gaba da addu'a insha Allah komai zai dai-dai ta."

  Kallon Malam tayi tace
"Malam wllh Waleed ya matuk'ar bata mun rai saboda haka yaje yaci gaba da zama da matar sa Ni........."katseta Malam yayi da cewa
"Haba Zainabu me bakin ki yake shirin fad'a ne akan danki guda d'aya da Allah ya baki?"
"Yaje Malam yaje idan duniyacr ta ishesa riga da wando, tunda har ya nuna matar sa tafi uwar sa yaje ya zauna da ita Amman ba ni Zainabun ba!"

ZAMAN KISHIWhere stories live. Discover now