🎈🎀 *ZAMAN KISHI*🎈🎀
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ/HYDAR*✍🏻*PAGE 76~80*
Sai azahar waleed ya farfad'o daga suman da yayi, dakyar ya bud'e idanun sa ya sauke su akan Hafsat da har yanzu tana sume.
Hawaye ne suka zubo a idanun sa yana sake kallon ta.
K'ok'arin mik'ewa yayi yana tashi yaji kafar sa tayi wani kara karr da wani mugun ciwo, K'ara ya saka ya sake kwanciya a wajen yana sauke numfashi.Wayar sa da yagani a wajen a gefe ne yasashi sauke ajiyar zuci ko ba komai zai samu me taimaka musu.
Dakyar yaja jikin sa ya k'arasa inda wayar take ya dauko.
Tsayawa yayi ya fara tunanin Wanda zai Kira a waya, Baba shine abinda ya fad'o mishi.
Da sauri ya samo number ya kira shi.Malam Abdullah da yake zaune a masallaci yana addu'a kiran Waleed ya shigo mishi.
Bai d'auka ba sai da ya kammala abinda yake sannan ya dauka.Cikin da shasshiyar murya Waleed yace
"Baba kazo ka taimaka mun karna mutu."
"Subhallahi Waleed me yake faruw?a me ya sameka Ina ne?" Duk a tare Malam ya mishi tambayar.Ba tare da Waleed ya amsa mishi ba yace
"Muna gida Baba."daga haka Malam ya kashe wayar sa ya mik'e jikin sa na rawa ya shiga cikin gida ya fad'awa Zainabu.
Itama ta shiga tashin hankali sosai duk da batasan me ya faru da su ba Amman tasan tabbas ba abu bane me kyau.D'aki Malam Abdullah ya shiga ya dauko wani kullin magani ya fita sannan yace da Zainabu tazu su tafi.
Cikin kankanin lokaci suka k'arasa gidan waleed, yanda suka gansu abjn ya matuk'ar tayar musu da hankali musamman hafsayda har yanzu bata motsi sai jini da take ta faman zubarwa ta gaban ta.
Da gudu Malam ya fita ya Kira me Napep shi ya taimaka mishi suka fito da Waleed sannan Malam da Zainabu suka fito da Hafsat wacce idan ka ganta sai da rantse da Allah ta mutu.
Asibitin da muke aka Kai su Nan kuwa aka karbesu aka shiga dasu emergency.
Daure karar kafar Waleed sukayi sannan aka mishi dressing ciwukan da suka jimishi a jiki.
Hafsat kuwa alluran tsayar da jini aka mata sannan aka mata dinkuna dan wajen yafi karfin dinki d'aya ko biyu sai da aka dinke ta ko wanne gefe,sannan Kuma aka bukaci jini da za'a sa mata.
A wajen Malam suka bukaci jini amsa musu yayi da to sannan suka shiga dashi ciki, gwada jinin akayi da na Hafsat Amman na banbanta bazaiyu a saka mata ba hakan yasa Malam yace zaije gidan su Hafsat yayi magana ko za'a dace.
Gidan su Hafsat yaje bayan sun gaisa da mahaifin ta Nan yake fad'a mishi halin da su Hafsat suke ciki.
Wani irin razana mahaifin Hafsat yyai sannan yace a kaishi asibitin yaje yaga Yar tashi.
Tare da mahaifiyar Hafsat da kannen ta suka nufi asibitin baki d'aya.
Doctor suka samu sukace ya musu bayanin halin da yarsa take ciki
Nan doctor ya fad'a musu cewa anyi amfani da itane ta hanyar karfi, sannan mazanda sukayi Mata fyaden sunada yawa hanadiyar hakan ne yasata zuban jini da dogon suma sannan sunyi mata dinki yanzu jini kawai suke buk'ata bayan wannan insha Allah ba wani matsala.
Sosai mahaifiyar Hafsat take kuka tana tsinewa Waleed da ya kasa ceton yarta har ya Bari aka illata mata da 'ya.
Duk wannan abinda suke a gaban mahaifin Waleed da yayi shiru yana jinsu baice komai ba.
Jinin maihaifin ta aka diba aka saka mata sannan aka kaita wani d'aki na daban da za'a dinga kula da ita na musamman.
Mahaifin Hafsat ya biya duk wani kud'i na asibitin.
YOU ARE READING
ZAMAN KISHI
General Fictionlabarine akan gidaje uku wanda ko wanne cikin su nashi salon kishin, labarine me dauke darusa da dama ki nutsu ki karanta domin limintuwa da wannan k'ayatattacen labarin.