🎈🎀 *ZAMAN KISHI*🎈🎀
*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ/HYDAR*✍🏻*PAGE 31~35*
Koda na shiga d'akin da aka kwantar da ita zaune na samu Hassana Usaina tana gefen ta da plate a hannun ta da alama yanzu suka gama breakfast.
Suna ganin na suka saki murmushi ni Kuma nayi saurin k'arasawa wajen Hassana ina cewa
"K'anwata ya jikin naki da sauki ko?
Babu inda yake miki ciwo?
Kanki baya miki ciwo Hassana?" A lokaci d'aya na dinga mata tambayoyi ganin kamar a rikice nake yasa Hassana tace mun
"Lahh Aunty Kubrah naji sauki sosai fa ni da yanzu likita ma yazo yace zai sallameni su Baba kawai ake jira su dawo dan sun koma gida kafin likitan ya shigo."Ajiyar zuci na sauki sannan na kalli Usaina nace
"Yadai Usy kin wani kafeni da idanu."na gama maganar ina daga mata gira d'aya."Hmmm ba dole ba kin shigo Hassana kawai kika sani baki san Dani ba."
Dariya nayi na rungumo ta jikina Ina cewa
"Ina na Isa na manta da 'yar uwa rabin jiki na."
Dariya gaba d'aya mukayi, dariyar kuma yayi dai-dai da shigowar su Waleed cikin d'akin tare da yaran shi.Da gudu Humaira ta k'araso wajen Usaina Sadiq kuma yazo wajen Hassana.
Murmushi dauke a fuskan su suka gaidasu sai a sannan su Hassana suka Ankara da basu gaida Waleed ba,a kunya ce suka gaida shi.
Kallon su yayi yace
"Hmmm sai yanzu kuka tuna dani kenan."Murmushi Hassana tayi tace
"Kayi hakuri ya Waleed wllh bamu manta da kai ba."Har Waleed ya bud'e baki zai magana su Baba suka shigo haka muka durkusa muka gaidasu da tambayar ya me jiki.
Bayan sun amsa Mana Waleed ya mik'e yace zai kai yara makaranta karsu makara.
Kamar su Sadiq zasuyi kuka haka suka fita sunata faman turo baki.Fitan Waleed baifi da minti goma ba sai ga Dr ya shigo ya sake duba jikin Hassana ganin Bata da wani matsala hakan yasa ya sallame mu muka koma gida.
Koda muka koma gida mun gama aikin gida misalin k'arfe sha d'aya muna zaune a parlour Ni da mama tace mun
"Kubrah banason abinda ya faru jiya yasa ki chanzawa mijinki ko wani dangin shi ko b'angaren ita amaryar!
Babu bawan da ya isa ya tsallake kaddarar sa saboda haka Hassana wannan abu da ya faru da ita yana cikin k'addarorin ta ne!
Ban yarda naji tashin hankali ko makamancin haka a tattare da ke ba Kubrah! Ki kula ki hankalta kisan abinda yake gabanki da bayan ki, zaman ki dana da da na yanzu dole zai banbanta domin wata zatazo ta shiga cikin rayuwar auren ku, banason tashin hankali duk da bansan ki da wannan ba!
Idan wani abu ya sameki ko ya shige Miki duhu ki raba dare ki kaiwa Allah kukan ki ban yarda da kina sanar da kawaye duk wani halin da kike ciki ba, ke ko ni kaina mahaifiyar ki ban yarda da ki fad'a mun wani sirri na cikin gidan ki ba, saboda haka Kubrah dan Allah ki zama me hakuri da juriya,ki daure ki zauna a gidan mijin ki duk wuya duk rintsi wata rana zakici ribar hakuri."Shiru tayi ta sauke numfashi sannan ta kara da cewa
"Karkiyi tunanin dan banida shiyasa nake fad'a Miki haka Kubrah,a'a banida kishiya Amman nasan sirrikan zama da ita sannan nasan ciwon ta Wanda duk a gaba zaki sansu. *ZAMA DA KISHIYA* yana da wuya kuma yanada dad'i a duk yanda kika d'auki abin ta haka zaizo miki, saboda haka kisan yanda zaki zauna da ita yanda zaizo miki cikin salama, kishi dole ne 'ya ta amman kiyi shi na hankali ba na hauka ba,kiyi koyi da kishin Matan Annabawa ba irin namu na matan zamanin yanzu da suka haukace akan kishi,Dan Allah'yata karki bamu kunya kiyi Koda bakyajin dad'in sa tabbas wata ran sai kinji dad'in sa, Allah ya Miki albarka ya baku zaman lfy ya albarkaci rayuwar ku baki d'aya."Tunda Mama ta fara magana na fara hawaye har ta gama, goge fuska na nayi nace
"Insha Allah Mama zan zame muku 'ya ta gari zan zauna da amaryar Waleed duk dad'i ko duk wuya bazaku tab'a jina da wani mummanar abu ba, nidai addu'a kawai nake buk'ata a wajen ku Mama."
YOU ARE READING
ZAMAN KISHI
General Fictionlabarine akan gidaje uku wanda ko wanne cikin su nashi salon kishin, labarine me dauke darusa da dama ki nutsu ki karanta domin limintuwa da wannan k'ayatattacen labarin.