PAGE 61~65

8 1 0
                                    

🎈🎀 *ZAMAN KISHI*🎈🎀

*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ/HYDAR*✍🏻

*PAGE 61~65*

Durkushewa Ummu tayi a wajen ta fashe da kuka dan tunda take a rayuwar ta bata tab'a d'aukan abin wani ba,sannan ba'a tab'a cewa ta d'auka ba sai gashi yau a gaban mijin ta ana mata sharrin ta d'auki kud'i.

  K'arasowa gaban ta Kabir yayi yace
"Kiyi hakuri Ummu ki daina kuka ki kwantar da hankalin ki nasan bazaki d'auki kud'in ta ba."ya k'arasa maganar yana daga ta tsaye.

  Kallon sa tayi tace
"Wllh wllh kaji nayi maka rantsuwar dan musulmai ban tab'a d'aukan abin wani ba."
"Na sani Ummu nasan halin ki saboda haka karki damu tashi muje mu kwanta dare yayi."

Haka ya kashe komai na parlour yaja hannun ta suka wuce d'aki.

  Haka Ummu ta kwana da wannan abinda Jiddah tayi mata a rai.

______________

  Ko yau ma da na tashi a asuba ban koma ba aiki na nayi na shiga kitchen na daura breakfast.

  Sai da na gama komai sannan ya koma d'aki nayi wanka na chanza Kaya, Mai kawai na shafa na fito.

A parlour na samu su Humaira har sun fito, komawa mukayi tare nayi musu wanka na shirya su sannan muka fito da su tare na zuba musu abinci ni Kuma na koma d'aki.

  Gaba d'aya abin duniya ya isheni abinda bai tab'a faruwa tsakani na da Waleed ba sai gashi yanzu Waleed baya mun magana baya son ko kallona idan ya ganni gani yake kamar yaga mutuwar sa, a fili nace
"Allah kaga halin da nake ciki Allah ka fiddani Allah ka sanyaya ran Waleed idan wali laifi namishi idan kuma ban mishi komai ba Allah ka sasanta tsakanin mu."na k'arasa maganar cikin kuka.

  Sosai nayi kuka domin tun jiya da abin Nan ya faru na nemi kuka na rasa sai yanzu.

  Sosai nayi kuka Wanda ya haddasa mun ciwon Kai hakan yasa na k'asa tashi a wajen barci me nauyi ya dauke ni.

  Waleed da Hafsat kuwa sosai suke more amarcin su gashi yanzu Waleed har yakai da bayason yaji an ambaci sunan Kubra sai yaji kamar zai mutu tsabar ya tsani me irin sunan.

  Yau tun 8 Waleed ya fita kasuwa saboda ankira shi a waya ance yazo yau kasuwa babu lfy.

  A rikice ya fita saboda Wanda ya Kiran shi kansa a rikicen yake hakan yasa ya fita ko karyawa baiyi ba bare wanka.

  A parlourn Waleed Hafsat ta ajiye duk wani abinda ta dafa dan karyawa sannan ta shiga wanka.

  Humaira da Sadiq kuwa Wasa suke sosai a parlourn don su kwata-kwata Basu kula da abincin da Hafsat ta ajiye ba.
Da gudu Humaira tazo tayi wurgi da plate din da aka rufe ta wuce.
  Doyar ciki kuwa gaba d'aya ya zube kan carpet.
Faruwan hakan yayi dai-dai da shigowar Hafsat parlour.

  Wani uban ashar ta dura sannan tace
"Uban waye ya zubar mun abinci."
A tsorace Sadiq yace
"Ba ni bane Humaira ce."
Tuni Humaira ta fara kuka tana cewa
"Kiyi hakuri Anty bangani ba."
Sam Hafsat idanun ta sun rufe tsabar b'acin rai haka ta kama Humaira tahau dukan ta.
Sai da ta mata duka Sosai sannan tayi wurgi da ita tana cewa
"Shegiyar yarinya wllh watan sai na kasheki."

  Ai kuwa Hafsat tana wurga Humaira ta bigi gini hannun ta yayi wani Kara kashh wani razannen ihu Humaira ta saka sannan numfashin ta ya d'auke.

  Ihun da Humaira ta sakane ya tasheni a barci a firgice.
Da addu'a na mik'e na fito Ina kwallawa Sadiq da Humaira kira.

  Sadiq ya k'araso wajena a guje yana kuka yace
"Momy Anty ta kashe Humaira."

  Wani irin jiri naji Yana shirin d'auka na idanuna suka fara ganin dishi-dishi duk da zancen yaro ne amman dakyar na samu nace
"Tana Ina ita Humaira?"
"Tana kwance a parlourn Dady kuma kanta yana jini."

ZAMAN KISHIWhere stories live. Discover now