PAGE 26~30

15 1 0
                                    

🎈🎀 *ZAMAN KISHI*🎈🎀

*WRITTEN BY*
*MOMYN MUSADDIQ/HYDAR*✍🏻

*PAGE 26~30*

Mik'ewa tsaye tayi ta wanke Hassana da mari tace
"Ni sa'arki ce da zaki...."
Bata kai ga k'arasa maganar da take ba itama Hassana ta wanke ta da mari tace
"Baki isa ki mareni na barki ba wllh."

  Ai kuwa Nan danb'e ya barke a tsakanin su.

  Su kusan biyar suka taru akan Hassana yayin da Usaina ke k'ok'arin taimakawa 'yar uwar ta ganin abin yafi karfin ta ne yasa ta fito da gudu ta nufi wajen Kubrah tace
"Aunty Kubrah kizo sun tararwa Hassana suna mata duka."

  Mik'ewa Kubrah tayi tace
"Duka kamar ya?
Me ta musu?"
"Aunty Kubrah pls muje yanzu ba lokacin tambaya bane."
Da sauri muka shiga cikin parlour dan raba wannan fad'an.

  Muna shiga d'aya daga cikin su ta dauko wani kwalba ta rad'awa Hassana a kai.

  Wani irin razanannen kara ta saka ta fad'i a wajen sumammeya.

  Da gudu na k'arasa wajen Ina ambatan innalillahi dan abun ya matuk'ar bani tsoro ganin Hassana tana zubar da jini gashi bata motsi.

  Daga rinannun idanuna nayi na kallesu ganin babu wacce ta damu a cikin su yasa na kalli Usaina wacce tayi suman tsaye a wajen tunda muka shigo.

  Hawaye na zuba a idanuna na tausayin kai na da kannena na tab'a Usaina nace
"Taimaka mun mu fita da ita."

  Kallona kawai take dan har yanzu a tsaye take bata motsa ba.

  Da karfi na bigi kafar ta nace
"Ki taimaka mun mu fita da ita nace."

  Sai a sannan tayi wani razanannen kara ta fara wani irin numfashi.

  Sai a lokacin na tuna da Usaina tana da aljanu Wanda idan har aka tab'a d'aya daga cikin su to tabbas sai sun tashi.

  Sauke kan Hassana nayi akan cinyana na komawa Usaina da gudu na ruk'o hannun ta.

  Wani mugun bugu tayi mun ta turani gefe Allah yasa akwai kujera a wajen shine ya taimaka mun na fad'a saman sa.

  Matar da ta ratsawa Hassana kwalb'a Usaina taje ta shak'e,sosai matar take ihu tana neman taimako.

  Yan uwanta da suke wajen ne suka k'araso da gudu dan kwaceta a hannun Usaina.

  Gaba d'ayan su zubar dasu tayi a wajen ta komawa matar.

  Da gudu na koma parlourn na na wuce kitchen na d'auko ruwa a cup na tofa addu'o'i sannan na koma wajen ta.

  Har sannan bata saki matar ba ta galabayyata sosai sai faman zare idanu kawai take tana sake numfashi.

  Zuwa nayi gaban ta na watsa mata ruwan addu'a a fuskan ta sau uku,a take ta saketa ta sulale a wajen ta kwanta.

  Ajiyar zuci na sauke na koma parlour na da gudu na d'auko wayana na kira Baba na sanar dashi duk abinda yake faruwa.

  Cemun yayi gashi nan zuwa kar nakira Waleed.
Amsa mishi nayi da to sannan ya katse wayar.

  Wad'an da sukazo gere kuwa gaba d'aya sun gudu sunbar gidan dan tsoron Usaina sukaji yanzu.

Hassana kuwa har yanzu tana sume bata farfad'o ba,ga kuma kanta da har yanzu jini ke zuba.

  Haka na sasu a tsakiya na zauna Ina hawaye Ina tunanin wanne irin rayuwa zamuyi da wannan amaryar da tun batazo ba mun fara ganin tashin hankali.

  Ba'afi minti goma ba sai ga su Baba da Mama sai wasu a cikin almajiran sa samari Wanda suke zaune a gidan mu kamar yaran Baba.

  Addu'a yayiwa Usaina a take kuwa ta Mik'e sai dai har yanzu idanun ta bai gama budewa duka ba, nida Mama ne muka kama Hassana muka fita da ita.

ZAMAN KISHIWhere stories live. Discover now